31

1.2K 27 0
                                    

💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫


💫💫 *_DUNIYA BIYU MABANBANTA*_💫 💫
      

            ✍️ M SHAKUR



                        3️⃣1️⃣


FREE PAGE
Shirya yaron akayi aka fito da fitoda shi aka kawoma Mummy shi, ahankali Mummy ta karbe shi tana murmushi tace "miji nasamu ko kishiya"? Dariya nurse din tayi tace "miji ne Hajiya" karbanshi Mummy tayi tana kallonshi yaron kato dashi Masha Allah.

Daidai mijinta yakaraso tace "Alhaji kaga mijina masha Allah dawa yay kama"? Dan dariya Alhaji yayi yace "ai kamanshi daban da uwar da baban, hala sai nan gaba zai dauki kamanni, sake gwada namban mijinta dana mahaifiyar shi kiji ko zasu samu yakamata" number Waleed tafara dialing amman bai shiga har lokacin hakan yasa tai dialing number Ammi, lucky wayar ta shiga, wayar na gab da katsewa Ammi ta dauka, kafin ma Ammi tai magana Mummy tace "kawata lpy kuwa? Tun jiya da daddare muke kiranki dagake har Waleed baya shiga wlh hankalina yatashi" dan murmushi Ammi tayi tace "Waleed ne yadan sami hatsari wlh yana asibiti agidan marayun shi har karyewa yayi akafada, ban fadima Ilham bane kinsan mai ciki ba'a daga musu hankali haka, nikuma ina dawowa gida magani nasha na kwanta sabida hawan jinina yatashi, Mom ce awurin shi amman yanzu nai wanka shiryawa ma nike nakaimusu breakfast" da sauri Mummy tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, ashe abinda yafaru kenan Ilham takira takira mijinta bayi shiga daga karshe saidai takira mu mukazo gamunan a asibiti wlh tasami karuwa yanzun nan amman tun cikin dare mukazo, anmiki miji fa, baki ganshi ba dan lukuti dashi" Mummy tafada cikeda farin ciki sabida tasan yanda Aminiyarta keson jika, Ammi mutuwan zaune tayi tama kasa magana, hakan yasa Mummy ta kyalkyace da dariya ta kalli mijinta tace "Alhaji tayi mutuwar zaune fa" sukahau dariya sanan tace "ki shirya saiki biyo kiga jikanki kafin ki kaima su Waleed abinci, Allah yabashi lpy, anjima dazaran an sallameta zamuje mu gaidashi"

Ammi kasa yarda da abinda aka gayamata tayi hannunta har wani irin rawa yake tai dialing number Mom dake zaune dakin tana kallon Waleed da tun jiya daya lumshe ido yaki budesu bacci mai nauyi ya kwasheshi yanzu muka yatashi dan tasan yana jinta sarai wlh, kaman bazata dauki wayan Ammi ba saikuma ta dauka takai wayar kunnenta, wani irin zabura tayi tace "Ilham ta haihu?" rass Waleed yabude idanunshi jin ance Ilham ta haihu, katse wayan Mom tayi tana murmushi sanan ta kalli Waleed dake kallonta ta tabe baki tace "mara kunya aika bude ido dakaji matarka ta haihu, suna asibiti ta haihu ansami namiji" ahankali yadan saki wata yar kyakkyawan murmushi sanan ya yunkura zai tashi, kafadarshi kawai da akai dauri kehanashi motsi yanda yakeso, da taimakon Mom ya iya tashi, Mom tace "me kakeso?" ahankali yace "office dina zani, I want to shower na chanza kaya naje nagansu" taimaka mai Mom tayi yamike tsaye ahankali suka fito waje, nurses sai gaidashi suke gyadamusu kai kawai yake, haryakai kofa yatuna alkawarin dayama Widad, Mom ya kalla yace "am coming Mom" sanan yay hanyar dakin datake, hannunshi yasa yabude kofar ahankali yashiga yana kallonta ganin tana bacci, ahankali yakarasa gaban gadon ya tsaya akanta yana kallon fuskarta kaman yatasheta dan taganshi saikuma yafasa yajuya kawai yafito tareda kullo mata dakin sanan yafito yay office dinshi shida Mom suka shiga ciki, dakin shi ya shiga yay bayi, brush yayi sanan yay wanka da ruwan zafi, jikinshi ciwo yakemai bana wasaba bai taba fada a rayuwanshi ba ko saisa Arham yay galaba akanshi oho, fitowa yayi yadauko wani jean yasaka da kyar sanan yadauko wata riga sai saka yakasa sawa, kwalama Mom kira yayi hakan yasa ta shigo, wani scissors yanuna mata, saida suka yanke hannun rigan daman sabida hannunshi yay balance sanan tasamai rigan ta shinfidamai dadduma yay sallolin da ake binshi sanan suka fito, Mom kejan motar suka dauki hanyar asibitin da Ilham take, parking sukayi suka fito sanan suka fara tafiya har zuwa dakin datake akwance.

Bude kofan Mom tayi ta shiga, Ilham na kwance kan gado, fuskarta ya kumbura suntum tsabagen kuka, sai Mummy dake zaune kan kujera rikeda jaririn da aka shirya yay kyau, Mummy na ganinshi tace "subhallahi, innalillahi wa innailaihi raji'un, Waleed wanan wani irin hatsari ne kaga yanda jini yataru a idanunka kuwa, jibi wuyanka da fuskarka sannu Waleed" kanshi akasa duk take maganganun nan ahankali yace "ina kwana Mummy" "ina kwana Waleed, ya karfin jiki? Allah yabaka lpy kaji, Allah yasa kaffara ne sannu" gyada matakai yayi suka shiga gaisawa da Mom sunama juna barka, karasawa gaban gadon yayi yana kallon Ilham data tsareshi da ido itama tana kallonshi tana mamakin abinda yasame shi haka, dan murmushi yamata ya shafa goshinta da hannunshi saida ta lumshe ido tabude su ahankali ta kalleshi, murya chan kasa yace "thanks for giving me a baby khadija, Allah yamiki albarka" gyadamai kai tayi tareda mika hannunta takama lafiyayyen hannunshi tarike gam, cikin muryanta da baya fita sosai tace "what happen to you Babyna"? Baki yabude zaiyi magana Mom ta taho rikeda jaririn tace "wato agaban mu ake nuna mana sonkai ko kana nuna kafi damuwa da matarka kan yaronka dayazo duniya yauko" murmushi Mummy tayi ranta fess ganin Waleed naji da yarta. Mom tamikamai yaron tace "ga danka nan dauki abinka kaga yanda yay kama da abokin ka kuwa kaman yay kaki ya tofar" wani irin mummunan faduwa gaban Ilham yayi saikuma ta daure ta lumshe idanunta da sauri kaman wacce bacci ya sace, ahankali Waleed yasa hannunshi ya karbi yaron yana kallon fuskarshi sanan yazauna abakin gadon yana rikeda shi yana kallon fuskar jaririn dake bacci yana murmushi, ko Allah yasan cewan yanason Arham, so na domin Allah, Allah ya azurtashi da d'a amman sai yaron bai biyoshi ba bai biyo mahaifiyar shi ba saiya dauko kamannin amininshi hakan yasa yaji bazaima iya sakama yaron sunan mahaifinshi ba, dan da yace in namiji yahaifa zai sakamai sunan mahaifinshi but wanan da yaron ke kama da Arham dole Arham zai bama yaron kodan Arham yagane shibai rikeshi da komiba sanan har gobe har jibi shi dan uwanshi ne no matter what.

DUNIYA BIYU MABANBANTA (TWO DIFFERENT WORLD) Where stories live. Discover now