PAGE 1

6 1 0
                                    

💥💥💥 *ANEESAH*💥💥💥

*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻

_Bismillahir rahmanir rahim_
_Da sunan Allah me rahma maijin kai_
_Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanahu wata'ala Mai kowa me komai_
*_Tsira da aminci su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammadu (s,a,w)_*

*_INA ME GABATAR MUKU SABON LITTAFINA ME SUNA ANEESAH! LITTAFI NE DA YA KUNSHI ABUBUWA DA DAMA, KISHI, TSANTSAN SOYAYYA, CIN AMANA,TSANTSAN MUGUNTA DA ZALUNCI, TAUSAYI,BAN DARIYA, KAI ABIN DAI SAI WANDA YA KARANTA, ZAKI/KA SAMU SAMAN KARANTAWA NE AKAN 200 KACAL GA ME BUK'ATA SAI YA TUNTUNI TA NUMBER NA NAGODE MASOYA SAI NAJIKU_* 🥰❤️

_Wannan littafin na kud'i ne zaku samu karanta shi akan 200 kacal ga me buk'ata tamun magana ta number nan 08146196391_

_Free page_

   🅿️1️⃣

Alhaji Muhammad bafulatani ne usul, haifaffen Adamawa, a nan garin Adamawa aka haifeshi ana Kuma yayi auren fari  amman neman kud'i ya fito dashi ya dawo dashi cikin garin Kano.

  Alh Muhammad yanada mata uku wad'an da Allah ya azurta ko wannen su da haihuwa.
Gwaggo itace uwar gidan sa da ta haifa mishi yara uku biyu maza d'ayar su mace,
Ibrahim da Idris sai kuma Halima k'aramar su kenan .

  Sai Innah matar sa ta biyu wacce ita kuma yara hudu Allah ya bata gaba d'ayan su mata ne, _AISHA, HAJARA, ZAINAB, ZUBAIDA,_ Wanda yanzu gaba d'ayan su sun aurar da yaran su.

  Sai matar sa ta uku BaaBaa kenan wacce ita kuma yaran ta biyu me, _KARIMA, DA HAUWA,_ suma suna gidan mazajen su tare da yaran su baki d'aya.

   Ibrahim shine babban d'ansa Wanda yanzu shima yana da iyalinsa, matar sa d'aya Hajiya Maimuna da ta haifa masa yara biyar, Muhammad shine babba Wanda suke kira da _ARYAN_, sai   Sadiq sai yan biyu Abdul-Rahman da Abdul-Rahim, sai autar su Fateemah wacce ake kira da Ameerah kasancewar sunan Gwaggo ne da ita.

  Hajiya Maimuna macece me mutunci da sanin ya kamata, ga sanin darajan mutum Koda kuwa ta girmeshi ne, sam bata da damuwa ko kadan, shiyasa Alhaji Ibrahim yake matukar kaunar ta, sannan wannan halin nata ne duk yaran ta suka d'auka, Amman Banda ARYAN wanda sam shi ba haka yake ba, ya banbanta dasu Sadiq nesa ba kusa ba duk da daman shine babban su amman yanada matuk'ar zafi da saurin fushi idan aka tab'a sa.

  Alhaji Idris matan sa biyu Hajiya lailah da Hajiya Hadeeza gaba d'ayan su sun haihu, Hajiya lailah yaran ta biyar gaba d'aya 'yan mata sai autan ta namiji me sunan Alhaji Ibrahim da suke Kiran sa Khalil.

  Hajiya Hadeeza kuwa yaran ta uku 'yar ta babba itace _ANISAH_ me sunan Gwaggo sai k'annen ta biyu Hassan da Usaini, bayan su kuma haihuwa ya tsaya mata.

  Hajiya lailah sam bata da hali ko kad'an, don irin matan nan ne masifaffu ga masifar kishi sam bata san mutumci ba, domin bata ragawa kowa a wannan family, sam bata bawa kowa girman sa, mutum d'aya ne take shakka Alhaji Ibrahim dan yanda take tsoron sa ko Baffa mahaifin su bata tsoro.

  Hajiya lailah tana matukar muzgunawa Hajiya Hadeeza da yaranta, ba abinda Hajiya lailah ta tsana kamar Hadeeza da yaran ta, sam bata sonsu ko kad'an burin ta kullum shine ta gansu cikin wani hali, gashi Hajiya lailah irin matan nan ne masu son abin duniya dan ita sam bata son talaka kai ko gidan ta batason talaka ya shigo bare har ya rab'eta ya shafa mata talauci.

  Kamar yanda Hajiya lailah batason Hajiya Hadeeza haka yaranta ma duk ta koya musu tsantsan kiyayyan yan uwan su, sam basa raga musu a cikin gidan Nan ko kad'an, haka kuma suka raini Hajiya Hadeeza sam basa shakkan yi mata rashin kunya a gaban kowa.

Hajiya Hadeeza Kam macece kamila me mutunci da sanyi hali da sanin darajar dan Adam, kamar yanda take haka yaranta ma suke, musamman _ANISAH_ wacce sam batada damuwa babu ruwanta da kowa harkan gaban ta kawai take, duk abinda za'ayi musu a cikin gidan nan bata saka baki haka Kuma bata barin k'annen ta suma su saka bakin har suyi su gama.

  ANEESAHWhere stories live. Discover now