KUSKUREN BAYA EPISODE 2

1.2K 47 7
                                    

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️02

A firgice ta juyo  Ibrahim ta  gani tsaye a bayanta yana sakar  mata  murmushi, ta yatsina  face d'inta  tana kauda  kanta gefe ,tsaye yayi yana kallonta gabansa na wani irin  fad'uwa, musamman daya tuna shine  dalilin accident din da tayi.
     Cike da sanyin jiki ya k'ara matsowa daf da ita ya rage tsawonsa har tana iya jin karar bugun zuciyarsa da hucin numfashinsa  a gefenta, runtse idannunta tayi ta juyo zata mishi magana karaf idanunsu  ya tsarke cikin juna  har saida hancinsu ya  da'n gogi  juna.

Tsura ma juna idanu sukai kafin daga baya  tayi ko'karin da'uke kanta shima yaso yin hakan sai dai ya kasa aiwatarwa,  sake juyo daita yayi akayi rashin saa hancinsu ya goge juna kanta ya bugi goshinsa  . "Ouch!". Ta furta a hankali cikin Jin zafi ta kai hannunta kan bandage din dake zagaye a kanta.

"So...sor...sorry!". Ya fada a rikice , ta  tsura masa Ido  tare da lumshe masa Ido tana radadi  , idannunsa ya runtse Shima  kamar ciwon a kanshi yake , ware idannunta tayi a hankali tana kallon yadda duk yabi ya rud'e yake bata hakuri a natse ta samu guri ta zauna  tuni  Shima gwiwowinsa suka   mazauni a gabanta  Yana kallonta kmr ranar ya fara ganinta .

          "I.B!". Ta Kira sunansa cikin sassanyar  muryarta  kamar yadda ta saba kiransa, lokaci guda ya d'ago rinannun idannunsa ya zuba mata Yana  kallonta itama shi take kallo cike da tsananin tausayawa."Tan I am really really sorry for causing you so much troubles on your special  day". Ya fada yana kallonta cike da kulawa da nuna lallai yana nufin abunda yake furta mata har cikin  ransa.

Lumshe idannunta tayi ta bud'e a hankali  " Hey is not your fault kawai haka Allah ya tsara karka yi blaming d'in kanka akan accident din Dana samu ". Ta fad'a tare da kauda kanta gefe  dan ko kada'n batason ganin irin wannan yanayin nasa , dan yana karya mata zuciya .

        "ni ne naja komai Kinga dole nayi  blamed kains akan   abinda ya faru idan  ban kira ba a wannan lokacin ba  this wouldn't have happened to you , nayi diverting attention di'nki I am very so......"."Oh my god  I.B!"ta sake  fada cike da bacin rai idannunta a rufe.

"I am s...".
        "I know you are Kuma nayi accepting kaima kayi hakuri". Ta faɗa lokacin data tashi tsaye tana binsa da kallo shima tashi yayi suka kalla juna murmushi ya sakar mata. Da sauri ta da'uke kanta tare da shooking d'in kanta  da murmushi me sauti.
         Jin sautin murmushinta yasa shima ya fad'ad'a nasa murmushi.

Taku tayi zuwa bakin window d'in shima cikin sauri yabi sahunta, yasa hannunsa biyu ya zagayeta dasu ya mannata a  jikinsa, Runtse idannunsa  yayi yana jin wani irin feelings d'inta, sam baisan  ya rasa ta a rayuwarsa.

Bangaren Tanweer kuwa  ajiyar zuciya ta sauke tare da runtse idannunta, tana matuk'ar tausaya ma d'an uwan nata da  irin son da yake mata tun bata san soba yake nuna kulawarsa akanta , ta rasa mai yasa har yau bata jin sonshi cikin ranta baya ga na 'yan uwanta   duk da tasan yana masifar sonta da rawar jiki a Duk abunda ya shafi lamarinta tare da rumgumarta  amma ta kasa sakin jiki dashi gashi shi  kusan bai da aiki saina  nuna mata tsantsar so da kulawa a ko yaushe Amman  hakan baya sata taji irin abunda take jin  friends dinta na bata labari sai dai kawai ta biye masa, Sun jima a tsaye yana rungume da ita inda sabo ta saba da wannan hug din nasa wanda iya abunda yake iya samu  kenan agunta  bayan shi ba wani.

"Salamu Alai... !".
      Momy tafad'a lokacin data turo kofar dakin  yanayin data gansu yasa tayi saurin kokarin komawa tare da jan ko'far da sauri Tanweer ta zame  jikinta daga rik'on da Ibrahim ya mata wanda shima tuni kunya ta gama rufe shi."Please Momy wait!". Ta fada lokacin data dan taka da sauri zuwa bakin ko'far tana kallon Momynta wacce ke kallonta cike ta tambayoyi ,ganin yadda take kamar tana Jin tsoron yin magana,  sun dauki minis a tsaye a haka tana jujjuya ka'farta ta rasa meyasa take jin tsoron yin magana akansa  duk da she don't know him.

KUSKUREN BAYAWhere stories live. Discover now