KUSKUREN BAYA EPISODE 5

892 42 12
                                    

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️05

Cikin  natsuwa  yake murza kan     
Stearing   motarsa  zuciyarsa  cike fal  da  matsanancin  farinciki  baro mahaifiyarsa  da  kannensa  cikin farinciki  mai  tsanani  da  yayi, a nan duniya  bashi  da  burin daya wuce sanya  ahlinsa  cikin  farinciki , numfashi  ya  janyo  ya fesar  yana ɗan  dukan  kan stearing "zan dangwama  ina  baki  farincikin da kika rasa ammina  har sai kin gaji , inshallahu   zan  ɗauke  miki kewar komai ,zan mallaka miki duk wani dadi   dake  cikin duniyar nan   ke da yan'uwana  lafiyarku   farincikinku  jin  dadin rayuwa  zan yi kokari  ......
   Kiran  Anas  da ya shigo wayarsa ne ya  katse masa zancen zuci da yake ,  ya  sauke naunauyen  ajiyar zuciya sannan   ya  kai idanunshi  kan wayar a natse  ya kai hannunsa ɗaya ya  ɗauki  bluetooth  dinsa ya manna a kunnen ya dannan wayar  take muryar Anas ta doki dodon kunnenshi   "kana  Ina  munzo gida mai  gadi  yace baka nan ? Iskar ya furzar sannan yace  "naje ganin ammina  ne   gani   akan hanyar dawowa   ku  bani  minti  goma zan karaso  "okay  sai  ka karaso muna jiranka ..
Ya cire bluetooth din ya ajiye a mazauninsa  ya cigaba  da tuki yana sake lulawa  zance  zuci har zuciyarsa ta  shiga  hasko  masa yarinyar daya baro a gidansa  dogon tsaki yaja saboda  tuno kalmar ta gareshi kalmar da yaki jininta kuma take bashi haushi ....

Jaguwa  zaune  cikin d'akin daya tanada  domin  tautauna bayanai masu  mahimmanci  akan aikinsa  ,gabansa laptop dinshi ne ,yana faman operating  yana sauraron  bayanan  jubi  inda yake bayani akan alhaji tanko gote wanda ya kasance shararraren dan kasuwa wanda   duniya tasan da zamansa sannan ya tara tarin  dukiya bilaadadin  anan  gida nigeria da kasashen  ketari  ,ya mallaki qadarori da dama  da companies a kowace jaha dake ƙasar nigeria " bincikenmu  ya nuna mana mutumin  baya zaman gidansa  da daddare sai da rana  bayan  haka  akwai  tsaro mai tsanani tun  daga bakin get  doping  estate  har  zuwa cikin gidansa ta kowani bangare  dakarunsa  zagaye suke  da gidan  bayan boyayyun  camerori dake lugu  da sako na gidansa, me zai hana  mu hakura da wannan taget din  muyi  facing din wani  yayi shiru hade da numfasawa  sannan ya cigaba da magana "jaguwa a ganina mu hakura da wannan aiki  kawai ko me kuka ce yan'uwa ?  ya  fadi haka yana kallon  sauran yan'uwansa dake zaune suna sauraronsa , duk suka gyara  "gaskiya mu hakura tun da tsaro yayi yawa  inji cewar kamil  ,Anas ya numfasa yace  " kuna nufin bazamu yi nasara ba akan aikin da muka ɗauki tsawon lokaci muna jiran aiwatar dashi ? a qalla wannan shine karo na hudu da muke rusa budget din aiki akan Alhaji tanko gote  gaskiya a ganina bai kamata muyi wasa da damarmu ba kawai mu fara shirin aiwatar dashi kuma a cikin satin nan "dan Allah malam ka natsu kayi nazari akan operation din nan    jabir ya katse masa hanzari  ta hanyar fadar haka"the best solution mu hakura tunda jubi da kamil suka nuna abar shi , kai koni nayi supporting dinsu mu hakura kawai muyi facing din wani aiki ......

    Sai lokacin Jaguwa ya d'ago kyawawan idanunshi masu matukar kyau jere da gashin ido  ya tsura musu yana  kallonsu daya bayan daya sai daya ɗauki tsawon minti biyar yana kallonsu  sannan ya mike  tsaye yana rufe  laptop d'insa  ya soma magana a tsanake kamar ba wannan shararraren tantirin daya addabi manya kusoshin gwanati  da manya attajirai ba  "duk naji bayaninku daya bayan daya amman kusani wannan aikina ne jiya ba yau ba , da  muna saka tsoro a zukatanmu da bamu kawo wannan matsayin ba  , matsayin ƙasar nan take bulayin neman Jaguwa ido rufe, burin duk wani dan sanda mai matsayi ya samu nasarar gano inda muke ,ko'ina acikin kasar nan magana ɗaya ne ana son ganin wanene wannan mutumin daya addabi kasa da kasa  gidajen radio dana  tv , news paper ko'ina magana ɗaya ne   amman har yau basu yi nasarar gano mu ba abinda zai faru yanzu shine ni da kaina zan tunkari tanko gote ya karasa maganar a fusace yana dukan table din dake tsakiyar su jabir  sannan ya juya musu baya rugume da hannunwansa duka  .....

KUSKUREN BAYADove le storie prendono vita. Scoprilo ora