TSAIKO (The Wait) CHAPTER SIX

13 1 0
                                    

#igbo

BOSS POV

aikin da take kamar ni nake duk a dame na ke saboda ina lura da ita yau ma luluna da yunwa ta zauna.
She didnt eat food na fada ina kallon kemal da ya zuba min ido an fada maka itama acici ce irinka wanda baya dagawa abinci kafa mutum ko rashin lapiya yake baya kincin abinci  daga kafada nayi hade da tabe baki nace ba gani nan ba very healthy

ya ce haka fa wannan matarka ta shiga uku da yin girki, sau biyar fa kake cin abinci a rana bayan kaci da Safe sau biyu zubin farko tea and bread na biyu kuma around 10am se ka ci kazo kaci lunch around 2 after 4 ka kara wani ga dinner sannan in zaka kwanta se ka sha fruits kuma kowanne abinci kala daban baka maimaici chaiii your wife will suffer oooo.
Murmushi nayi don kemal akwai surutu na ce i know my lulu will handle that, and if she cant We can hire a Cook you know?
hakane fa bari indan kwanta akan sofa in huta kafin lulu ta gama ya karasa hade da kwanciya ni kuma na koma na zauna akan kujera hade da lumshe idanuna na fada tunanin ta yadda zanyi confessing ina son lulu a gabanta am kinda nervous na rasa me yasa take min kwarjini bayan nasan am bold enough na tsaya a gaban kowacce ya mace duk kyawunta da  matsayinta amma With lulu is a different Case.
Knock naji hade da muryar ta tana excuse me sir bude idanuna nayi ina me zube su a kanta tare da tunanin da me tafi duk matan da su ke so na sunfi ta kyau da wayewa nesa ba kusa ba sannan ga su yayan masu kudi amma na kasa gani,
ni dai kawai nasan ina tsananin kaunar wannan halittar dake gabana, hada ido muka yi tayi maza ta dauke na ta idan hade da turo min file ta juya nayi yunkurin in ce mata ta tsaya in kaita gidah amma na kasa har ta tafi
Kemal ya ce me yasa baka ce ta tsaya mu bata lift ba kasan yamma tayi zata sha wahala kafin ta samu abin hawa this your Love i dont understand
na ce na kasa wallah i dont know how to say it se yace dont say it but rather show it let her know you Love her by Your actions bance wai kace kana sonta da baki ba.
Nace toh hade da janyo waya ta kirar samsung s10+ zan kira Love of my life naji ya jikin nata tace tana jin zazzabi duk da dai nasan kila yanzu suna shirin bacci ne duba da yanayin lokaci ba daya bane tsakanin nigeria da dubai daga wa akayi daga can bangaren hade da cewa OBIM nace NNE how are you tace fine and you? am fine what says the result tayi dan jim hade da cewa when are you coming nace not soon but if you misses me i can come tace no Stay but come see me when you are less busy nace okay NNE ta ce where is Kay give him the phone na mika wa kemal wayar ina murmushin saurin ganewar NNE ko da yake indai har tayimin magana da yaren igbo taji na bata amsa da English toh lallai kemal na nan domin na fahimci yana jin ba dadi sosai saboda be iya yaren ba.

Jinai yana ce mata NNE your son is in Love nayi hanzarin tahowa don in kwace waya ta amma na makaro naji tana tambayar shi who is the lucky girl ya ce she is his secretary cike da mamaki ta ce what! Ya ce yes and she is not a model as We thought she is very simple and matured and she is not too Pretty NNE tace thats totally our negative side of Views Kay, surely it is and he Love her more, whats her name? ta tambaya cike da doki yace Batulu but your OBIM here is calling her lulu tace oh is she a muslim? ya ce yes ma'am ta ce thank God i dont have to deal With his dad over this issue okay am sleepy gud night ta fada hade da kashe wayar.
Miko min wayar yayi yana murmushi na warce hade da cewa Fuck you, yace ba komi.

Waye BOSS ne?

KHALID MUHAMMAD DISO shine ainahin sunanshi Alhaji muhammad diso shine mahaifin shi haifaffen unguwar diso ne a nan cikin birnin jihar kano amma kakannin su wadanda suka yada zuriyar su yen asalin garin babura ne ta jihar jigawa, se dai daga kan kakansa har zuwa iyayen sa duk a diso a ka haifesu, gidan su katon gidah ne me cike da sassa daban2 malam ado shine mahaifin muhammad tare da mahifiyar shi sa'ade ana kiranta inna sa'ade a cikin gidan su malam ado yana da yen uwa da uba guda goma sha hudu bakwai maza bakwai mata amma duk cikin su shine babba mazan duk suna nan a cikin gidansu tare da matayensu su kuma matan kowaccensu tayi aure da yayaye wasu har ma da jikoki. A cikin gidan kuma kowanne sashi suna da yaya da yawa don daga me mata biyu se uku babu me mata daya yara ne a gidan rututu har ma baka iya banbancen yayen kowanne sashi malam adamu wanda ake kiransa da Kawu babba a cikin gidan matan da ya aura gudah shida ne in ka dauke matar sa ta fari sa'ade dukan su kuma babu wacce ta haihu se dai sa'ade ta taba bari sau daya tun farkon auren su daga nan kuma shiru har kusan shekara bakwai kannensa maza da mata duk sun yi aure kuma suna ta haihuwa bayan wadannan shekarun se ya karo aure da matarsa me suna hajara itama dai shiru babu haihuwar shekara uku da aurenta ya auro wata itama haka se kuma suka rabu don tace ita kam haihuwa take so a haka dai se da yayi mata biyar a bayan hajara amma basa zama saboda sun ce ai baya haihuwa sa'ade da hajara su ka ci gaba da zamansu tare cikin amana duk da dai wataran ana dan samun sabani amma ba me zafi ba.
A gaba daya gidan ma ba'a wani hayaniya ko gulma ko cecekuce irin na gidan gandu don kowa ta ciki na ciki amma ba'a nunawa, a takaice dai sunyi dacen mataye marasa kananun magana.

Bayan shekara 15 da auren malam adamu da sa'ade katsam se gata da ciki kowa ya taya su murna kawu babba ya dauki son duniya ya dora wa wannan cikin watan cikin biyar itama hajara Allah ya bata nata nan fa farin cikinsu ya ninku suka ci gaba da rainon cikin su a tare har cikin sa'ade ya isa haihuwa ta haihu danta namiji, ranar suna aka saka mashi muhammad (baban khalid/boss) bayan wata hudu hajara ma ta sauka lapiya yar ta mace aka saka mata khadijatu daga nan kuma basu kara haihuwa ba.
Muhammad ya taso yana me sha'awar ya ga yana aikin office sabanin duka yaran gidan daga sun gama Secondary suke fadawa kasuwa suna bin iyayen su ko kuma su samu ta su sana'ar daban amma basa cigaba da karatun boko to ana ta kai wa yake ta kaya!!
Shi kuwa muhammad bashi da burin kasuwa gashi Allah ya bashi basira yana sahun mutanennan da ake kira da gifted duk kuwa da cewa makarantar gwamnati ce se dai a lokacin su makarantun gwamnati ana basu kulawa sosai ba kamar yanzu ba.

Kokarinsa ya saka duk wani qiuz da za'a yi shine me jagorantar ta kuma ya ci.
ga makarantar allo ma ya kusa sauke alqur'ani me girma. Har ya shiga form 6 inda anan ne ze kare karatun Secondary se kuma jami'a amma a lokacin malam adamu bashi da kudin biya masa sakamakon auren khadijah da ya taso, mijin nata dan kanin baban su ne me suna hamza, kuma anan cikin gidan nasu zata zauna an ware musu sashin su.
Bayan gama jarabawar su ta fita ne kwatsam se ga bakin turawa sun zo makarantar, su na duba result din su domin tantance hazikan dalibai don daukar nauyin su zuwa america domin kammala karatunsu (a lokacin nan ba'a exam mal practice duk me ka gani a result din dalibi to kokarinshi ne) suna dubawa har suka ci karo da result din muhammad duk yafi kowanne dalibi kokari suka nemeshi don bashi scholarship tare da shirya shi domin tafiya.
Da kyar malam adamu ya yarda a lokacin kai be waye da turawa ba kowa kallon azzalumai ake musu cikin ikon Allah suka tafi ya fara karatunshi a america akan accounting har ya kammala degree dinshi ya dauki tsawon shekara uku ba tare da yaje gidah ba, wai! aiko hankula sun tashi a gidansu., da gamawarsa turawan nan suka bashi aikin yi hade da tayin kara karatunshi zuwa mataki na gaba ba tare da jinkiri ya amince ganin ze samu kudade., ya fara karatun masters dinshi da shekara daya ya shirya tafiya ganin gidah. ya taho cike da tarin nasara da kudade masu yawa.

A ranar da ya dawo ya sha fada gurin malam adamu  da yen uwansa ya basu hakuri tare da yi musu bayanin yadda tsarin yake da kuma yadda rayuwarsa ta kasance a can kowa ya taya shi murna, ciki kuwa harda kanwar shi khadija wacce take da yaranta mata guda biyu.
Bayan wata biyu yayi shirin sa na komawa, inda mahaifin shi yace be yarda ya tafi haka cikin nasara ba tare da yayi aure ba ya ce masa ya duba a sashin gidannan idan akwai wacce tayi masa cikin yen matan da suka rage ya zaba a daura masa aure da ita, shi dai be ga wacce tayi masa ba a kannen nasa domin dai danginsu duka bakake ne shi kuma yana son farar mace tar a rayuwar sa tun ma ada da beje ya ga fararen fata ba.
Shiru yayi na wani dan lokaci yana tunani a ransa ya kalli mahaifin nasa hade da cewa na baku zabi kai da inna ku zaba min me hankalin cikinsu. Ya tashi malam adamu na ta saka masa albarka.

Bayan kwana biyu mahaifinsa ya kira shi yace ya zaba masa Maryam nutsattsiyar yarinya me kunya kanwar hamza mijin khadijah se kaje ka ganta ku sasanta nan da sati biyu kafin ka tafi se a daura auren amma a ina zaka ajiye ta? Ya ce inshaa Allahu idan na koma zan yi kokari in turo da kudi a siya min dan fili haka a wajen gari se mu zauna in kuma da yiyuwar in dawo in dauke ta mu zauna a can to zan gani, malam adamu ya ce to madallah Allah taimaka ya tashi hade    da mikewa ya shige ciki.

Sati biyu tayi aka daura aure. Ya tafi ya barta anan yana mata aike duk bayan wata biyu a haka se da ya shafe wata shekara ukun sannan ya dawo da niyar ya dawo kenan domin ya nemi aiki anan BUK kuma sun bashi har ma sun masa tayin karbar gidaje na gwamnati da take ginawa na jan bulo anan wata unguwa kusa da buk din kuma ya karba saboda haka ya tattaro ya dawo gaba daya.

Bayan dawowarsa da sati biyu suka tare da amaryar shi a gidan sun fara rayuwa cikin aminci tun baya sonta har ya fara amma ba wai can ba saboda hakurin ta da kuma kawaici ga nutsuwa. Shekarar su ta farko da aure ta haifi yarta mace aka sa mata fatima, bayan ita ta kuma haifar mace aka saka mata sa'adatu, se kuma hajara a wannan Shekarar ne kuma ya biyawa mahaifin sa tare da mahaifiyarsa aikin hajji kowa ya taya su murna se dai inna sa'ade ce kawai ta dawo domin malam adamu ya rasu a can kuma an binne shi a can.

Sunyi kukan rashin sa sosai se dai ba kukan rashin madafa ba se dai na sabo domin kuwa muhammad shi yake dauke da nauyin Komai na su tun ma kafin malam adamu ya rasu. A cikin Shekarar sa ta biyar da aure ne a ka tura shi university of owerri seminar ta tsawon wata shida inda anan ne kuma ya hadu da elizabeth farar igbo tar dan kuwa farinta har daukar ido yake (maman khalid/boss)

TSAIKO (The Wait) Where stories live. Discover now