Chapter one

77 9 6
                                    

♥️SO HANA GANIN LAIFI♥️

✍🏻 Rashida Bature


I think you'd like this story: "SO HANA GANIN LAIFI" by RASHOWS on Wattpad https://my.w.tt/E1eYyWzedcb



PAGE1️⃣
tafiya nakeyi a hankali kamar wacce banason yin tafiyar,yayinda gefe guda kuma wasu yara ne guda biyu kowacce tana kan lilon wasa,Wanda hukumar makarantar ta tanada domin yin wasan yara.

"gurinsu na nufa duk da na girme ma shekarunsu amma hakan bai hanani zuwa gunsu ba don ganin nasamu abokan yin wasa, duk da inada tabbaccin ba lallai bane su amince da ni muyi wansan .

da isata gurin yaran dukansu suka sauk'o daga kan lilon ,babbar ta kama hannun k'aramar sukabar gurin bawai don sun gama lilonba,sedan bazasuyi wasa da ni ba ne kamar yandà kowa yakemin haka a cikin school din, don kamar masu kyama na ko masu tsorona.

"jiki a sanyaye na tsaya a gurin batareda na K'ara ko 1 step ba, nabi bayan yaran da kallo har suka b'ace ma gani na.

"in zakima yara magana kiringa musu murmushi tun kafin ki k'araso gurinsu,domin yin hakan zai basu tabbaccin cewan ba cutar dasu zakiyiba.

"Juyowa nayi ina duban me maganar wani yaro nagani yana maganar yana tafiya.

Cigaba nayi da tafiya don rashin taka man-man gurin zuwa.
ahaka nagama zaga gurin ban samu wanda ya yarda yayi mu'amula dani ba , har aka kad'a bell d'in komawa class.

bayan an tashine daga school d'in kowa yanata kiciniyar ganin yanufi gida ,wasu kuma anzo d'aukar su don yawanci ma Wanda ake zuwa d'aukar sun sunfi yawa masu tafiyar k'afar k'alilan ne.

tsayuwa nayi daga gefe ina kallon masu futa suna nufan gidajensu ,wasu kuma suna nufar motocin su abun gwanin ban sha'awa,kallo d'aya zakamin kagane Ina cikin gajiya domin fuskar nan tawa tayi zuru zuru , inama ace nice nake wannan d'okin komawa gida bayan an tashi daga school kamar wad'an nan yaran da naga suna murna in anzo d'aukarsu,nayi maganar zuci.

"ahaka har aka watse a makarantan ina tsaye ,ganin tsayuwar bazai fushsheni bane na fara tafiya duk da ban san Ina na nufaba,haka na ringa zaga anguwa anguwa .

"horn naji anayi daga gefena ,"juyowa nayi don ni a iya sanina ba'a kan hanya nake tsaye ba, bare ace za'a min horn don na kwauce."

"d'aga min hannu me  motar tayi alamar Kira .

"jimmm nayi kamar bazani ba,
"sedai na daure na k'araso kusa da motar, amma ban karasa jikin motar sosai ba.

"meya hanaki zuwa gida haryanzu kike yawo da uniform ajikinki? tambayar da mai motar tamin ne yasani d'ago kainà Ina duban matar, senaga ashe matar d'azu ne wacce tazo d'aukar yaron dayamin magana a school."

"kwarjini matar tamin ,haka kurin kuma  naji na aminta da ita duk da ba lallai bane Wanda zuciyar ka ta aminta dashi yakasance hakan yake azahiri.

"mama na bata nanne ."na bata amsa cikin galabaita, don Ina matukar jin yunwa alokacin,ga gajiyar yawon danasha."

"Ina mahaifinki to?

" yarasu tun Ina karama."

nabata amsan tambayar ta,shiru tayi tareda tsuramin ido na wasu lokaci.

"shigo cikin motana muje gidana kafun mahaifiyar taki ta dawo ,don ba abu me kyau bane kina d'iya mace amma kina ta zaga gari .

"Jim nayi! sannan na bude gidan gaba wajen me zaman banza na zauna, don inaga binta gidan tan shine min mafuta agareni ,don banida yanda zanje na rab'e ayanzu, sedai na K'are a yawona abin an guwannin al'umma.

"ido kawai na baza Ina kallon manyan gidajen damuke wucewa masu matukar kyau da girma . "agaban wani tan gamemen gida naga tayi parking,tareda danna horn.

"wangale kofar akayi ,Wanda ya bud'e k'ofar da alama shine get man din don ganin danayi ya rusuna yana cewa
"hajiya barka da dawowa .
kai ta d'aga masa" yauwa sallau sannu da aiki ,sannan ta ja motar muka karasa shiga cikin haraban gidan da aka bud'e mana.

K'atone gidan ga fili sosai a haraban gidan,ga wasu fulawoyi Wanda ya dad'a k'awata gidan seya bada wani ni'imtaccen kamshi, parking tayi agurin da aka tanada domin a jiye motoci ,ta bud'e k'ofar gefenta ta futa ,sannan ta duben tace" bisimillah muje ko!futowa nayi Ina me rik'e jikina tareda sunkuyar da kaina ,gaba tayi Ina biye da ita abaya har mukazo bakin wani k'ofa ,ta danna wani abu me kaman glass sedai an kewayeshi da wani adon fulawa yana manne a gefen k'ofar shiga gurin ,take k'ofar ta bud'e, lumshe ido nayi Wanda bansan lokacin danayi hakanba don jin wani sanyi me d'auke da k'amshi ya doki fuskata ,ciki tashiga nikuma na samu gefen k'ofar na mak'ure agurin ,juyowa tayi taga a yanda na tsaya sannan na wani mak'ure jikina,batamin ganaba sema dawowa datayi ta kama hannuna tanufi cikin falon dani,ido na bud'e don ganin irin had'uwar da falon yayi ,wasu kujeru ne na alfarma a falon ,ga wata gin-gimemen tv a manne a falon ,gefe guda kuma gurin dinning table ne ,ban gama kallon falon ba najiyo muryan wata mace.
"Kai mom meya had'aki da pretty kuma ? harkika jajib'o mana ita gida salon ta goga ma mutum datti?
"b'ata fuska wacce aka kirata da mom d'in tayi ba tareda tace komaiba.
hakan yasa wannan yarinyar taja bakinta tayi shiru .
a raina nace "indai nan ne gidanku lallai kunyi gaskiya nak'in kulani da bakuyi a school daman ina ku Ina kula talaka irina.

kujera wacce aka kira da mom ta nunamin tace "zauna barinzo,ciki ta nufa ta haye sama yanda naga k'ofofi a jere,nikuma na nemi guri a k'asa na takure agurin .

"hello pretty"

d'ago kaina nayi don jin muryan yaron dayamin magana d'azu a school, murmushi yamin yace "segaki a gidan mu ?

nidai kallo da Ido nabishi.
"tabbas nayi murnan ganinki anan mom ta kyauta data zo mana dake.

nidai ido kawai na tsura masa don daman haka nake bamai yawan magana bane ni,sekuma ya had'u mun da rashin gata se abun ya had'u yamun yawa.

mom kamar yanda naji yaranta suna cewa bata jima da shiga ciki ba segata ita da mijinta sun fito daga wata k'ofa,suka zauna akan kujerun falon ta duben ,"meyasa baki zauna asamaba kika zauna a k'asa?

kaina na K'ara sunkuyar wa , ahankali nace "Ina wuni inagaida mijinta ,amsawa yayi tareda cewa "maza tashi ki hau kan kujera  mom d'inku batason jayayya ,intace ayi abu tafison ayishi a lokacin,maza tashi kihau sama ".

a d'ofane nazauna akan   kujeran ,
"zanso ki gaya mana sunanki duk da nasan yarana may be sunsan sunanki tunda makarantar ku d'aya. amma zanfison sani daga bakinki,duk ido suka zubamin yarinyar datayi magana d'azu kuma se aikamin da harara takeyi.

"Cikin sanyin murya kamar wacce akamin dole na bud'e baki da kyar .

"sunana maryam muktar,anacemin pretty.

"ok "nasan tun d'azu bakiyi sallah ba don haka yanzu kije kifara yin salla gacan d'aki zamuje na nuna miki ,idan kin idar sekizo ga abinci can akan dining table sekici inyaso semu karasa maganar.

"kaina gyad'a mata ,tashi tayi tana gaba Ina bin bayanta .wani d'aki takaini Wanda bawani girma yake dashiba, d'an ma dai-dai cine ,se dai kam yaji kayan alatu ,ga ac dawani kamshi me dad'i yana tashi a cikin d'akin , direct bathroom d'in cikin d'akin tanufa,kamar tasan ban San kan kayan bayan gidan ba,ta tsaya tana nunnu namin ,sannan tace"seki kunna komai nagani ko kin gane . fuskata kamar koda yaushe tana a had'e na nuna mata sannan tafuta taban guri nayi uzuri na had'e da d'auro alwala.

kamar yanda tace idan na idar na sameta a falon hakan nayi ,Ina tafiya Ina rarrakub'ewa, hannuna ta kama,muka nufi yanda aka jera abincin ,akan kujeran dinning na zauna, ta zuzzuba min abincin "inkinci be ishekiba  gashinan seki K'ara kici iya yanda kikeso .

"nagode abunda kawai na iya furta mata kenan..

*To masoya gani dasabon buk senaji daga gareku ,ammafa kusani yawan comments dinku shizai bani kwarin gwaiwar cigaba da rubutashi ,banison comment da sticker😊*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 14, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SO HANA GANIN LAIFIWhere stories live. Discover now