2

165 21 6
                                    

Husnah tana shiga ta iske Mama kwance a jikin wani qaton Alhaji, tana ganin Husna ta zabura ta miqe, wani kallon banza Husnah tayi musu sannan ta shige 'daki, bayan kamar minti biyu se ga maman ta ta shigo, kafin tayi ma ta magana tayi saurin cewa

"Haba Mama, Haba mama, wai yaushe zaki daina irin wannan halin ne, ni gaskia wallahi ba kya kyauta mun kwatakwata, saboda fa irin wannan halin naki ne fa yasa Khadija bata zuwa gidan nan, ke kika haife ta amma kamar ba ke kika haife ta ba, ni wallahi har mantawa nike yi ke ce Mahaifiyar khadija, yanzu duk wanda ya ga waccan Anty Zuwairan da Khadija se ya 'dauka ita ta haife ta"

Se da ta kai aya sannan mamar ta tace

"Uwa ta kin gama magana? Ko da saura in barki ki qarasa"

Gyara zama Husnah tayi sannan tace

"Ni fa Mama ba fa'da nake miki ba kawai ina gaya miki gaskia ne"

"Ai Shiyasa  nace in barki ki qarasa?"

Samun wurin Maman ta tayi ta zauna sannan tace

"Da ga zuwan ki kin tasa ni a gaba se jawabai kike mun, me kika ga nayi, wannan da ki ka gani auren shi zanyi, kuma irin wa'dannan Alhazawan se da tarairaya, in ban mishi haka ba ai se ya tafi ya barni, da kuma kike maganar waccan banzar yarinyar ta zama kamar 'yar Zuwairah to ina ruwana, sanin kanki ne tuni na cire Khadija acikin lissafin yara na, har yau ina tunanin da naje haihuwa chanja mun ita akayi, abunda yasa kawai na yarda yarinya ta ce saboda tsananin kamar da mukeyi da ita, yarinyar da tayi sanadiyar uwar ta ta bar gidan ubanta, duk ita ta kawo mana tsiya"

Ta'be baki Husnah tayi sannan tace

"Ai kema mama duk laifin ki ne, ya zaayi ki dinga bin maza, ai ba abu bane me kyau"

Cikin tsawa Mama tace

"Ke zan ci ubanki fa, ya ishe ki haka, dan uwarki ni zaki zauna kina fa'da ma wa'dannan maganganun, wai ma uban me ya fito da ke a daren nan"

Fuskan tausayi Huseey tayi saboda tasan halin mamar ta, dan tasan ba qaramin aikin ta bane ta mare ta, hakan yasa tayi fuskan tausayi dan ta samu mamar ta ta biya mata buqatan ta ta tashi ta bar mata gidan, cikin salon lallashi ta rungume mamar ta tace

"Sorry mummy nah, kar ki yi fushi dani"

Hararan ta mama tayi sannan tace

"Ke 'din ce ai, bakin ki baya da linzami, se kace kema ba'a ta'ba zubar miki da ciki ba, ke ubanwa ya fa'di naki, ina ce har yau ni ka'dai nasan maganar"

Idon Huseey ne ya cika da qwalla, saurin gogewa tayi tace

"Kin mun alqawari ba wanda ze ji maganar nan, amma se kiyi ta suka na da maganar, wallahi ni Allah yasan nawa qaddara ne"

Tausayi Huseey ta ba mama se mamar ta sake rungume ta tare da fa'din

"Daina kukan to, yi haquri kinji "

A Haka mama tayi ta lallashin ta ita ma, duk wanda ya ga Huseey da mama ze 'dauka qawaye ne kasancewar mama irin wa'dannan matan ne wainda ba sa kwa'ba ma yaransu saboda su ma tarbiyar bata ishe su ba ya sa Huseey dik ta lalace, ita kuma Khadija se ta bi tarbiyar da baba yake musu da kuma yadda matar baban nasu ke qoqarin yi musu tarbiya ita ma.

Nan dai Huseey ta gaya ma mama ku'di tazo nema wurin ta, haka ta 'dauka ta bata sannan ta fito tayi wucewar ta, tana isa gida a bakin qofa ta tarar da baba, da alamu ita yake jira, cikin rashin gaskia tace

"Barka da dare Baban Khadija"

Baba ne ya galla mata harara yace

"Sannu da dawowa, kin dawo lafia?"

TASNEEM 2 in Tasneem series✅Where stories live. Discover now