4

83 16 1
                                    

Shirye shiryen auren Husna da Aryan ne ya kan kama, yau ake ta shirin kai lefe gidansu Husnah, a gidan Mummy aka ha'du gaba 'daya,Ummi (siyamah) ita ce jagora tunda ita ce qanwar mummy, ita Mami bazata samu daman zuwa ba saboda ta tafi Kano wurin Mahaifiyar Farha, su Noorie, Anaan, Anty Fadeelah, Anty Ameerah, da dai sauran su ne zasu je kai lefen.

Tasneem Farha ce na ga ta shigo gidan tayi parking mota, fitowa tayi ta shiga cikin gidan da tafiyar ta cikin natsuwa da kamala, a parlor ta iske Noorie , tana shigowa Noorie tace

"Barka da isowa tauraruwa a cikin taurari, Me sunan uwa ta Tasneem Farha Ahmad, Babyn Mami, uwar gidan Ahmad Aryan, Maman Fatima Airah, surukar Hajia Fatima Zahrah Ahmad"

Dariya Farha tayi tace

"Ina gaisuwa Hafsat Noorie Adeel Noor, Amarya kuma Uwargida a gidan Mukhtar Saheeb, maman Fadeelah Amani, Yayar Adeel Noor, shalelen Baban ta Alhaji Maheer Yusuf, surukar Hajia Fadeelah Yusuf "

Dariya sukayi gaba 'daya,kullum suka ha'du irin kirarin da suke ma kansu kenan, sannan Farha ta samu wuri ta zauna, cewa tayi

"Haba no wonder ashe Mamma bata nan ne shiyasa kika wangale baki kina ta surutu"

Noorie tace

"Ke suna 'dakin mummy suna tattaunawa fa ni ka'dai ce anan"

"Ayyoo, qarfe nawa zamu tafi kai kayan?"

Noorie ta watso mata harara tace

"Ban gane ba, wai dake za'a je?"

"Ha'a ji wannan, dani za'a je mana, to me nazo yi nan in ba zuwa nayi mu tafi tare ba"

"Wasa kike yi, da ke za'a je kai lefen kishiyar ki?"

"Sosai ma kuwa to meye a ciki?"

"Tabbb bazan iya ba ooo, a gaishe ki"

"Hahaha to Noorie kishin me zanyi, ai bata isa inyi kishi da ita ba kema kinsani, qanwa ta ce wannan"

"Gaskia ne wannan, kishi ai ya zama old fashion"

"Ashe brain 'din ki na ja"

"Taso muje ki gaida su mummy se muji yadda za'a tsara tafiyan"

Nan suka nufi wurin su Mummy, suna shiga 'dakin Mummy tace ma Farha

"Se da dai kika zo ko? kin dai san ba cikakken lafia gare ki ba, ga zirga zirgan da kika yi na siyo kaya, Allah ya shirya ki Babyn Ukhtieey "

Mamma ce tace

"Oh bata da lafia, Farha me ke damun ki?"

Farha tace

"Mamma gajiya ne kawai wallahi, amma naji sauki "

Nan dai akayi ta mata sannu sannan aka firfito dan tafiya, Ummi ce tace

"To wai wa ya san gidan ne? Farha ko zaki kira muna Aryan ya yi muna kwatance?"

Fitowa da ga mota Farha tayi tace

"Nasan gidan ai Ummi"

"Yauwa to madalla muje"

A cikin motar Farha aka sa wasu akwatunan, wasu kuma a cikin motar Noorie, mota uku akayi, wasu suka shiga na Noorie, wasu na Farha wasu kuma na Anaan sannan aka wuce, Farha tayi masu jagora motar ta na gaba, cikin mintuna ka'dan se gasu a qofar gidansu Husnah, basu fito daga motocin su ba suna jira suji abunda Farha zata ce, Farha rage glass 'din motar ta tayi sannan ta 'daga ma Noorie da ke bayan ta hannu alamun sun iso, fitowa suka fara yi daga motar, ita ma Farha ta fito, akwatunan suka 'dauka a ka fara shiga dasu, sallama sukayi tayi amma shiru babu wanda ya ansa su kuma gidan babu mutane, can se ga Aunty ta fito idon ta a kumbure alamun ta sha kuka, washe baki tayi cikin fara'a ta fara gaisawa da su, tabarma ta 'dauko ta shimfi'da masu sannan ta ce su zazzauna, tana ta cewa

"Maraba da ku sannun ku da zuwa"

Gaisawa sukayi sannan Ummi ta fara magana

"Mu dangin Aryan ne, munzo kawo kayan lefe, nan ne gidan ai ko?"

Aunty ta ce

"Eh nan ne gidan amma ba anan za'a ansa lefen ba, a can gidan Mahaifiyar ta ne"

Mamma ce tace

"Tohh ikon Allah yanzu can 'din zamu je?"

Kafin Aunty ta bada amsa se Ummi ta sake cewa

"Gashi ba mu san gidan ba ko za'a kwatanta muna?"

Cewa Aunty tayi

"To bari inyi ma Khadeeja magana se ta raka ku"

Tashi tayi ta shiga cikin 'daki, can se gasu sun fito tare da Khadijan, ita ma idon nata yayi ja, gaida su tayi sannan Aunty tace tayi musu jagora, maida kayan akayi mota sannan suka shiga motocin, motar Noorie Khadija ta shiga sannan suka kama hanya, gidan babu nisa da gidan nasu shiyasa sukayi saurin isowa, tun daga bakin gate ake jin hayaniyar mutane a cikin gidan, Khadija na nuna musu gidan tace ita zata koma, Ummi tace mata

"Ba zaki shiga ba ke?"

Cewa tayi

"Aa sauri nake yi zan tafi, na bar Mama ita ka'dai a gida"

Dubu biyu Ummi ta zaro ta miqa mata, qin amsa tayi se da Ummi ta takura mata sannan ta amsa tayi godia, Ummi ta sake cewa

"Ya sunan ki? "

Cewa tayi

"Sunana Khadija"

Jinjina kai tayi sannan tace

"sannu Khadija, ke ma a gidan su amaryar kike?

Cewa tayi

"Eh ni qanwar ta ce uwar mu 'daya uban mu 'daya "

"Ahh MashaAllah sannu kinji Allah yayi albarka mungode"

"Ameen" kowa ya amsa da shi sannan Khadija ta sake musu godia ta wuce, Noorie tace

"Ummi na ga alamar Khadija tayi miki ko?"

Nan dai sukayi raha sannan suka shiga gidan.

Taku a Kullum

Aisha Ameerah ❤️

TASNEEM 2 in Tasneem series✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora