CHAPTER 15

610 80 7
                                    

Marka zaune a kan kujera ana mara fifita sai shan kamshi take wata baiwa na bare Mata tanjirun. Sanarwa taji bafaden ta yayi yace ranki shi Dade waziri da bafadai biyu sunzo sarki yana neman ki. Murmushi tayi ta Mike tare da cewa ni nasan bazai iya hure rashina ba ace yayi kwana 3 bai zo ba? Durkusawa bafaden nan yayi yace ranki shi Dade ki yafe min amma bana tunanin kiran nan akwai arziki a cikin sa.

Wanka masa Mari tayi har saida ya furzar da jini tace yayi ta lasa har sai ta dawo. Fita tayi da bayin ta biye da ita zata nufi hanyan turakan sarki daya daga cikin bafadi biyun yace AI barin khadija zasu. Kirjin ta ne ya fadi tace khadija kuma?

Ba Wanda ya kulata rimi rimi har fadan khadija kamar da gaske harda sallama ta shigo tana fadin kanwata lafiya ake nema na ko dai nakuda ne? Sarki ne yace rufe mana baki mutuniyar banza. Da sauri ta rissina tace Allah ya huci ran sarki ko zan iya sanin abinda na aikata? Sarki yace me yasa ba'a bawa khadija hakkin ta? Da sauri marks ta dara zubda kwalla tace mai martaba na rantse maka da Allah ina bata komai yadda ka bada umarni. Munira tace karya ne ko wani lokaci idan naje da kwando ku bamu gawayi bakwa bamu.

Abinci ma sai kowa yaci ake bamu sauran sadiya ne ta rufe Mata baki saboda nuni da khadija tayi Mata da ido. Sarki yace ke marka kince kin bayar munira tace baki bada ba wanne zan dauka? Jakadiyar marka ne ta durkusa tace mai martaba nasan bani sa muhallin saka baki amma sadiya je sace duk abinda aka bayar tana siyar wa tana siyo kayan alatu tana tarawa nima tace min na dinga daukan na uwar daki na amma ban aminta ba shine tace idan na kuskura na fada zata sa a kashe ni.

Munira ne tace karya kike yi talatu karya kike yi yaya sadiya bazata taba cutan mu ba. Talatu tace wallahi gaskiya nake fada Kofi munira ta dauka ta jefi talatu da shi. Ruwan da ke ciki ya watso har jikin marka. Tsawa sarki ya daka Mata ya kalli wani bafade yace sabo, fita da ita. Rike hannun ta sabo zaiyi tace duk Wanda ya taba ni sai na kashe shi.

Cikin daga murya Sarki yace ku fita da ita ko kuna tsoron yarinya ne? Cacumar ta sukayi tana kokuwa tana fadin ku sake ni ku sake ni nace ku sake ni bazan yadda naga anyi zalinci ba. Bayan an fita da ita tana kuka tana kiran maman ta sarki ya kalli sadiya da ba alamun tsoro ko mamaki a tattare da ita yace bazaki kare kanki ba?

Tace mai martaba na yarda da kaina kuma Allah yasa nice da gaskiya bana bukatan na kare kaina. Talatu race toh a bincika kayan ta. Sadiya tace bari in dauko muku da sauri talatu tace saboda ki samu daman boyewa ko? Mai Marta ni zan dauko. Da hannu yayi umarnin ta dauko. Dauko kayan sadiya talatu tayi AI kuwa ana juyewa ga himilin sarkoki ne da wasu gwala gwalai da murjani.

Sarki yace a kama sadiya a kashe ta. Saboda ta saci kayan uwar gijiyar ta, ta wahalar da ita sannan ta wahalar da sarki kuma an kusa tukunya wani bisa laifin ta. Murmushi tayi tace baza'a bani dama na kare kaina ba kamar dazu? Talatu tace daman me za'a baki bakida karyan da zai cece ki. Dauko abubuwan sadiya tayi tace tabbas wannan kayan alatu ne. Amma abin tambayan anan shine ni da na tara dukiya me tarin yawan nan mai yasa har yanzu ban gudu ba?

Talatu tace saboda basu isheki ba, sadiya tace ko kuma kazafi aka min ba. Cikin bacin rai batasan sanda tace sarki ka duba jakar da aka samu kayan nan a ciki wannan sakar ba irin na bangaren mu bane na sashin su ne. Talatu tace AI zaki iya koya Dan kiyi mana sharri. Sadiya tace cikin kayan nan wannan abin hannun Wanda mai martaba ya bawa kuyanga marka ne ranan sallah kuma kaf cikin kayan ta tafi son sa. Ta yaya akayi na samu na siya a kasuwa?

Talatu cikin rawan baki tace sata kikayi.  Sadiya tace me zaisa na saci abinda nasan shi uwar dakin ki tafi so Dan haka zata yi saurin gane ya bata? Kuma wannan yasin kowa yasan bamai irinsa a masarautar nan daga masarautar kushma inda kuyanga marka tazo ta taho dashi matsayin kayan aurensa yanzu an daina samun irinsa a ko ina shi ta ya akayi na samu. Shiru talatu tayi. Sarki yace ba tambayan ki akayi ba?

Da sauri ta durkusa tace mai martaba kayi min afuwa ka yafe min wal..... marka ne ta dauke ta da Mari ganin asirin ta zai tonu tace amma talatu kin bani kunya yanzu duk yadda nake kula da ke ki rasa yadda zaki saka min sai ta haka? Ki saci kaya na kuma kiyi kokarin sawa a kashe sadiya ? Nasan kinason musa shi kuma musa bafade sadiya yake so amma shin har abin yakai kiyi kokarin kashe ta da hannun sarki?

Matsowa tayi tace mijina nasan kashe talatu ya dace ayi amma duba da dadewan da muka yi mai zai hana a Koreta daga masarautar nan kawai? Shafa gemu yayi ya kalli talatu yace kinci darajar  ina son marka Dan ahaka a Mata bulala 20 sannan a raka ta wajen gari na. Godiya talatu tayi suka hada ido da marka tayi Mata alamun in kika sake kika ce wani Abu sai na kashe ki.
Sarki yace wannan kuma yana nufin sadiya, a kaita gidan aiki tayi wanki da guga ba mako biyu sai ta dawo saboda daga murya da tayi a gaban sarki. Sadiya tace godiya nake. Kallon marka yayi yace ke kuma zaki bada Rabin albashin ki har na wata 3 ma khadija saboda rashin kula da kika yi wajen tabbatar wa an bata hakkin ta. Marka tace amma..... yace da kayan ki kala 5 da sauri tace tuba nake.

Fita marka tayi ranta na 'kuna ta koma barin ta sai huci take tace shegiya daya daga cikin bayin ta ta kalla tace ke asabe daga yau kin maye gurbin talatu. Je ki Nemo min mai magani ya duba ni kaina ciwo yake. Asabe tace an gama shugaba ta. Fita tayi ta Nemo auwalu mai magani bayan ya duba marka yace bacin raine yada kike jin ciwon kai in kika huta zaki ji daidai.

Tace kaje yar uwa ta sadiya ba lafiya ka duba ta. Yace an gama  bayan kamar dakika 15 sai gashi ya dawo yace na duba kuyanga sadiya Dan da ke cikin ta ne masha Allah tabarakallah akwai girma ita kuma tana da karancin jini a dinga bata abinci masu kara jini bawai Gina jiki ba. Marka tace mun gode auwalu mai magani yace Allah ya kara lafiya shugaba ta sannan ya fice.

Murmushin mugunta tayi ta kalli asabe tace kin San mai zakiyi. Murmushi asabe tayi sannan tace an gama.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now