CHAPTER 26

469 71 12
                                    

Tunani nabila ta fara ya akayi har yanzu bata fadi tayi targade ba saide tunaninta ne ya tsaya lokacin da kasan takalmin kafanta da saman suka rabe. Ras kake ji a kasa ta gurje hannu da guiwa hakan yasa ta saki kara Dan haka hankalin kowa ya koma kanta. Murmushi munira bai gama daukewa ba Dan tasan za'ayi haka.

Lokacin da nana ra yi Mata nuni da kar ta karba yasa ta nazarta kila akwai yar kasa tsakanin laila da nabila amma da alamu a fili suna nuna kamar komai lafiya ne. Hakan yasa ta karba Dan kuwa kifi na ganin ki me jar koma. Ganin nabila ta fito da nata tana nuna Mata yasa ta kara murmusawa take ta jin dadi Dan faduwa tazo daidai da zama idan ma tana so ta cutar da muniran ne aide nata me kyau zata yi shi hakan yasa ta ajiye nata a gefen ta nabilan  da ta tashi dauka kuma ta dauki na nabilan lokacin da nabilan ke yaba kyan shinfidar gadon ta.

Shikenan idan cutar ta zata yi tasha idan kuma ba komai ma shikenan. Dukda kuwa ra lura kamar kasan takalmin da aka bata wato sol din bai zauna ba.  koda ta fita da gudun gwada nabilan take Dan taga yanayinta.

Kuka bibbiyu nabilan take yi kukan zahiri na ciwon da taji da kuma kuka na zuciya kuka na ruhi saboda taso ace munira ta fadi taji ciwo yanda za'a ki a kaita saboda kar a zabe ta don kamar de yadda yake a ka'ida baza'a kai me yunwa ko ciwo ba hakan ne yasa masu bayi suke kula da bayin su sosai musamman idan wannan lokacin ya matso.

Da salati Dan masani ya fito sanda ya samu labarin abin da ya samu nabila yana fadin shikenan da alamu dai ba dani za'a yi ba dama kece jarin nawa. Tsaki  maman laila taja tace ka bada ni wallahi baka dauki yaranka matsayin mutum ba sai abin samun kudi da suna?

Da badan ina yarinya aka yi min aure ba da ban auri mutum me son zuciya irinka ba. Tana kaiwa nan ta fisgi munira zuwa dakin ta. Nasiha tayi wa munira tace gashinan kwana uku ya rage ku tafi ki kula da kanki. Daga kai tayi maman laila tana sharan kwalla tace karki manta ki dinga kawo min ziyara kinji?

Rungume ta munira ma tayi tana shafa bayan ta alaman rarrashi. Abin kamar wasa har kwana uku ya kewayo. Fada kuwa sai rarraba ido ake yau za'a shigo da sabbin bayi Wanda aka siyo da Wanda aka bawa sarki kyauta.

Tsofin bayi na hassada kuyan hu ma na hadiyar karago Dan sunsan za'ayi musu karu wasu. Wata daga cikin kuyangun tace toh me anfanin in an kawo su ma? A kewayen da ya wuce aka kawo ni amma sarkin ko rike hannu na bai taba yi ba. Wata ce ta kalle ta tayi murmushi tace toh AI bakisan dawan garin ba sarki taimakon ki yayi domin yakan siya bayin ne idan ya yanta su haka kawai bazasu yi daraja ba amma idan yace kuyan gun sa ne daga baya sai ya yanta su idan aka siyo sabi sai kuma ya hada miki da kudi da nufin godiya bisa zaman amana da kika yi dashi Dan haka ba wai yana zaba Dan yanason yayi anfani dake bane.

Yana yin hakan ne Dan ya baki mukamin yanda Wanda zai aure ki a gaba bazai ce miki AI ke baiwa ce a da ba. Dan haka idan kika ga ya zabe ki bai nemeki ba alama ce ta zai yanta ki ne.  Kuyangan tace kina nufin zan fice gobe kenan? Dayar tace da alamun haka nide nasan zama ne. Dayar tace in kuwa haka ne Allah ya masa albarka Dan ni taki akaci garin mu dashi aka siyo mu aka kawo mu agadaz daga nan aka kawo ni nan a matsayin kyauta daga sarki agadaz.

Murmushi dayan tayi  domin kuwa ita tana daya daga cikin irin su munira da yan cinka ace kai bawa ne tana so ta taimaki Mata a daina zalinci anma bata da bakin magana. Toh ita a suwa? Kuyanga wacce batada ko mukami daya gashi tanantsoron sauran irin ta su tsorata su karyata ta idan an nemesu shaida.

Babban gate din masarautar unto aka bude bayi suka saki baki har ma da masu yancin domin ko su munira da taga gidan su na sarauta kuma taga gidan Dan masani Wanda yake da kudi gidan sarauta daban yake.

Shugaban bayi ne tace a nutsu kowa ya kalli kasa ban sauke kai kuma ban durkusawa. Bangaren bayi aka nufa dasu inda anan ne akwai Mata guda 2 Wanda zasu duba su baza ido su zabi Wanda suka ga ya dace a aikawa sarki daganan sai shima ya rege wani zubin kuma ya dauki duka ma amma dai acikin su bai wuce daya zuwa biyu yake kwanciya da su ba sannan baya musu dole ko ya zabe ki kika ce bakyason sa da aure zai mayar dake gidan bayi ba tare da musguna ko ya kuntata miki ba.

Su kusan Hamsin aka jera inda aka zabi munira da nana bude baki munira ke son yi tace batason a zabe ta amma ba bakin magana sai kuma ta tuna da maganar maman laila cewa kar ta dinga magana har a gane bata magana idan ba haka ba za'a iya Koran ta tun kamin taje gaban sarki ko a cutar da ita.

Makwanci aka basu bayan an duba lafiyan su kowa na zumudi da kuma tsoran aje ba'a zabe su ba. Zamu iya cewa banda munira a cikin masu zumudi Dan kuwa ita gobe ajiyar da ta daura shine ta tafi neman yarima yaya zatayi hakan ? Allah shine masani. Da wannan tunani bacci ya daukesu.

ALLAH YA NUNA MANA GOBEN....NASAN NA YAU KADAN NE AYI HAKURI GOBE DOGO NA MASIFA ZAN MUKU DA IZININ ALLAH KAR KU MANTA KUYI VOTING, COMMENTING SANNAN KUYI FOLLOWING DINA A WATTPAD @miss_untichlobanty

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now