humood✨3.

230 16 0
                                    

#Wattpad
20/4/2021
#fatimalawlbmg

Lovesaga ❤️

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨❤️

Humood

3️⃣

Da asissiba ta tashi bayan ta idar da fajr,Bata koma ba kitchen tawuce tare da kunna Dan madaidai cin gas dinsu ta daura ruwan wanka.
Daki takoma ganin har yanzu Hanan Bata tashi ba,wani dukan tasake kaimata,ke kan ko shedan ne yamiki fitsari aka yaci ace kin tashi,wani juyin Hanan take tare da gyara kwanciyarta.

Yatsa taciza tsabar haushi,sunkuyawa Tai tare da leka kasan gadonsu ta janyo tsintsiyar su ta dakin ta zari guda biyu, murmushin mugun ta tayi tare da kwaye cinyar Hanan ta tsula Mata biyu.
Arazane Hanan tamike tana Sosa cinya,tare da fadin Allah ya,isa shikenan ke baki da aiki se na cin zali,

Hanan tin yau she nake tashinki kinki kina so kicemin bakiji bane koko.a hakanne kikeso kije Oxford din kina Latin lecture.

Ina ruwanki koke zakimin karatun ha,a haka kurin da asubaen fari mutun ya dameka!nazo hutun ma baza abanni in huta ba. Tashi tayi tana kunkuni tashige toilet.

Karkada kai tayi tana mamakin halin Hanan.
6:00 daidai tagama shirinta tsaff Daman class din safe ne dasu fito wa Tai tayi dakin Abba.
Sallama Tai seda ya ansamata tare dacewa shigo sanan tashiga.

Ina kwana Abba katashi lafiya.
Lfy Lau mamana harkin shirya ne
Ah Abba Daman lecture din safe ne da mu,Nina wuce.
Harta Mike zata tafi yakira ta,hannu yasa aljihu yazaro 1k yamika Mata.
Laa Abba Aida kabarshi ma Ina da chanji,
A,ah nimrah banasan gardama kirike zemiki amfani nasan Yan chanjin wajanki baza su ishekiba kikara kiyi kudin mota.
Karba Tai tare da Masa godiya Allah yakara budi Abbana.
Allah yamiki Albarka inshallah muna gama kwangilar da aka bamu da kudi yazo hannuna hostel xankama Miki ki huta da neman mota.
Ameen Abba Allah yasa.
To maza Tashi kije karki makara Allah yabada sa,a

Tashi Tai tafita ranta fesss tare da jin Dadi addu,ar da iyayen ta suke Mata tasan duk inda take Albarka su nabinta shisa inta fita kodar Bata ji.
Alhamdulillah Allah nagode ma daka bani iyaye nagari.

Tana fita Tai kichibis da motarsu sumeey, murmushi tamata tindaga nesa,Dadi taji sosai Daman tana tinanin samun mota yau Friday babu cab.
Shiga Tai suka ja mota.

Wuyansa Ameer yataba yaji haryanzu da zafi,daukan tsuman da yadaura Masa agoshi yayi yasake tsomawa a ruwa sanan yasake manna masa.

Hamma yasaka sanan yayi a,uziya tinawa da tin jiya basuyi bacciba saboda abunda yasanu humood aduk sanda daddy yamasa irin wannan to akwance yake wuni se yayi kwana uku bashida lafiya!.

Kallan Ahlam dake gefen humood yayi ta kankame hannun Dan,uwan nata kamar za,a kwance Mata shi,itama Bata dade da samun bacci ba ta jin gina kanta a kafadar sa.

Mikewa Ameer yayi daga inda yake ya karasa inda take,kallan ta yayi na Dan lokaci,wani mugun tausayi take bashi karama da ita tana going true pain shafo kyakyawar fuskar ta yayi tare da gyaramata gashin da ya zubo fuskar ta yayi,sanan ya rufeta da blanket.

Jin kiraye kirayen sallahr asuba yasa yamike cikin azama yafita saboda Karya rasa sallah.

Yanafita ta bude idanunta tabi bayansa da kallo,Ashe ta tashi jin antaba fuskarta yasa Tai kamar bacci take, murmushi tayi thank you ya Ameer ko bakomai kana nunamin kulawa.

Mikewa Tai tadau wanan ruwan Dan chanjo wani ruwan.

Kichibis sukai da nanny tana kokarin shigowa dakin,Cikin nuna kulawa da damuwa tace Ahlam ya jikin Dan,uwan naki.
Murmushi Tai Wanda iya labbenta yatsaya tace da sauki.

Humood!!!✨Where stories live. Discover now