page 4

12 2 0
                                    

💅🏻💅🏻SLAIM💅🏻💅🏻

FREE BOOK

BY
AMNAH A MUHAMMAD

(MIEMIE MUHAMMAD)

PAGE 16-20

Kamar yanda sukayi magana da Kakale haka washe gari da safe ta tashi tayi wanka ta shirya cikin shigan t-shirt da wando wanda koda yaushe kalan shigar ta kenan saidai t-shirt din tana da tsayi da fadi haka ma wandon yanada fadi sannan tasa hula ta yafa gyale Kakale data kalle ta taga takammala shiri ta dauki kudi da bazai wuce 2k bah ta bata tareda faɗa mata address din makarantan da zata sannan
tace "ki tambayi kudin admission da registration in kinje, kinga at least kin San wani abu akan makarantan ma koh?" Ta qare maganan tana kallon silaim. Ita kuwa Slaim din dariya tayi mata sannan tace "OK Ma, bakida matsala" fita tayi agidan Kakale na bin bayanta da kallo murmushi kwance a fuskarta.

Ita kuwa Slaim tunda ta fita tayi cikin kasuwa abinta inda take yawace yawacen ta tareda siye siye har dan kudaden ta suka qare ta shiga kudin da kakale ta bata, can taga wani shagon sayar da DVD da CD plate ta fada inda taga wani album da ta dade tana nema na misselia ikyawan duba kudin hannun tayi taga cewa inta biya kudin plate din toh lallai zata koma gida aqasa kuma tanada tabbacin bazata iya bah gashi ta gama kashe kudin da Kakale ta bata a kasuwan kuma album din shi daya ya rage awurin tana tunanin inta tafi bai zama lallai ta qara ganin plate din bah.
Shiru tayi n a wasu lokuta kafin wani tunani yazo mata daga ido tayi kawai hada ido da wani matashi murmushi ya mata inda itama tayi mai atake koh wanne su ya kau da kai gefe minti kadan tayi hanyan fita daga shagon cikin yaran shagon wani yayi saurin shan ganban ta inda ta fara ce mai "malam lafiya?" Tayi maganan agajarce, cewa yayi "ban plate din daki dauka" dan ja da baya kadan tayi kafin tace "plate?" Yace "eh plate din daki dauka awancan roll din ai naganki" zaro ido tayi sannan tace "malam toh na aje tunda nagan banda ishenshe kudi ajakata" nan fah wuri ya kaure da hayaniya inda gaba daya yan shagon ke bin bayan dan uwan su kan cewa tabbas ta dauki plate din matashin da suka hada ido dashi dazun yace "haba malam wannan qaramar yarinyan taya zaka tozarta ta tahanyan yi mata qazafin sata cikin tarin jama'a haka?" Wani ne a shagon yace "hmm malam kenan, Ku bakusan yanda barayin nan ke batda kama bane su shigo kasuwa suyita yima mutane barna bah kuma wasu sai ka gansu basu kai wannan yarinyan bah" shiru matashin yayi nadan wasu mintuna kafin yace "haka ne amman ni malamin secondary school next so, nasan halaiyan yara irin wadannan nasan wannan yarinyan bah barauniya bace kuma batai kama da barayi bah" nan dai sukaita cecekuce inda daga qarshe asalin mai yace "ton shikenan malam tunda ka matsa zamu barta da Allah kuma indai dagaske ta dauki plate din kaima kanada laifi anan" wani cikin yaran shagon yace "waya sani ma koh tare suke dan dazun kafin ta dauki plate din nagan sun Kali juna suna murmushi" main shagon yace koma dai meye suda Allah.

SLAIMWhere stories live. Discover now