page 5

9 1 0
                                    


           💅🏻💅🏻SILAIM💅🏻💅🏻

           
                 FREE BOOK

                     BY

     AMNAH A MUHAMMAD

  (MIEMIE MUHAMMAD)

         PAGE 21-25

Tafiya Slaim take tana saqe saqe cikin ranta bayan ta bullo ta wani siririn hanya da mutane basu fiya bi bah, kaman daga sama taji ana sallama cikin ranta tace "wannan kaman muryan namiji, kuma kaman mace, um toh meya dame ni. Amman muryan nada dadi" murmushi ne ya subuce mata inda ta qara jin muryan "Assalamu alaikum yan mata" gaban ta ne ya fadi inda wani 6ari na zuciyan ke raya mata da ita akeyi. Azahiri kuma tace "kaddai masu shagon nanne su biyo ni" numfashi ta sauke ahankali sannan ta girgiza kai kafin tace "inaaaaaaaa bama su bane"dake maganan ahankali takeyi hakan yasa wanda ke mata maganan  bai jita bah duk da yanzun ya qaraso inda take.
"Nayi sallama kintsaya kuma baki amsa min bah sai wani motsi da baki kike yi kaman mai cin goro" yayi magana fuskanshi cike da fara'a. Maganan shi ya dawo da ita cikin hayyacin ta "umm wa'alaikumus salaam" ta amsa tareda kallon shi sama da qasa. Tabbas ta gane shi wanda ya mata murmushi ne dazun cikin wannan shagon. Cikin sanyin murya dana jiki yace mata "yan mata, nasan baki manta fuskana bah saboda mintuna qal" ta yanke shi da fadi "toh bawan Allah lafiya?" Murmushi kawai yayi tareda girgiza kai kafin yace "magana nakeson nadan miki" "OK go ahead" ya fadi ataqaice. "Daman inason inmiki magana ne kan plate din daki dauka a wancan shagon ki bani in mayar musu dan naga sa'in dakika dauka kawai na rufa miki asiri ne saboda tozarci ne ace yarinya qarama ankamata tayi sata, wacce bata wuce matakin secondary school bah" "Bawan Allah dakata, ka daina dangantani da wani makaranta don ni bah daliba bace kuma bazan zama bah in sha Allah, maganan plate kuma kayi duk abinda kaga dama dan ni nasan ban dauki wani abu bah ashagon su mtsww" qarasa magananta da jan tsaki sannan ta bishi harara ta juya da niyan tafiya ta bar wurin yayi saurin daura hannunshi akafadanta da niyan juyo da ita, da sauri ta juyo tareda daga hannun ta da niyan  buge hannun shi daya daura akafadan ta saikuwa ga jakan ta ya fadi inda ya bude kayan ciki suka wargaje akan hanya dukan su kallon jakan sukayi tareda kayan ciki dake baje aqasa kallon kallo suka fara tsakanin su na wasu yan daqiqu ganin plate din cikin abubuwan da ke baje wurin kafin. Lokaci daya tayi hanzarin tattara kayanta dake qasa ta hada harda plate din ta tura Cikin jakan nata inda ya tsaya yana kallon ikon Allah cikin ranshi yana fadin "lallai wannan yarinyan akwaita da qarfin hali" lokacin da ya dawo daga duniyan tunanin daya shiga kuwa bata bah alaman ta tuni ta gama tattara kayanta ta wuce. Nan ya gama mamakin abin ya wuce abinshi.
Tafiya tana tunanin ina zata samu ta danyi fitsari can ta hango irin bayin kasuwan man da ake biya ashiga, da hanzari ta qarasa wurin ta biya ta shige, inda ta hangi wasu yan mata guda biyu riqe da wata budurwa guda daya sunata faman kokuwa batayi ta kansu bah saida ta sauke damuwan ta kafin ta fito taji daya tana ta bada haquri "dan Allah ku barmin jakana kuyi haquri" harta fito daga bayin data shiga bata daina basu haquri bah kuma basu qyaleta bah, kallon su tayi tsaf dukkansu shekarun su bazai gaza nata bah kuma ta tabbata bazasu girme mata bah tsaki ta ja sannan ta,qarasa wurinsu ta tabi daya inda ta juyo tace mata "ke lafiya kuwa?" Tayi maganan cike da gatsali murmushi Slaim tayi tareda girgiza mata kai sannan ta dauketa da mari cikin hanzari ta daga zata rama tayi saurin riqe hannun ta murde shi ta saki qara ta qara daura mata wani marin tuni ta gigice tana saki mata hannun kuwa ta fice da gudu dayan ma ganin haka ta fice aguje kafin adawo kan ta

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 04, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SLAIMWhere stories live. Discover now