page 3

15 2 0
                                    

💅🏻💅🏻💅🏻SLAIM💅🏻💅🏻💅🏻

FREE BOOK

BY
AMNAH A MUHAMMAD

(MIEMIE MUHAMMAD)

PAGE 10-15

Idon ta ɗaya ta buɗe tana kallon Inna, mirmushi ta hau yi kafin tace da inna "haba kakale ta ke da wane kiketa hayaniya da farar safiyan haka?" "Da kaniyan ki nakeyi ja'irar yarinya kawai" ta karashe maganan da jan wani dan guntun tsaki kafin taci gaba da cewa "ki tashi ki wanke baki ki karya inason yin mgn dake" inna na kaiwa nan azancen ta tayi gaba ba tareda ta jiraye amsan slaim bah.

Yanda kakale ta umurce ta kuwa tayi saidai abin karyawan nata da tasan Yana kicin ta fita daukowa nan ta samu inna tsakar gida tana yankan ganye na sana'an ta wuce ta tayi batareda tace mata wani abu bah ta nufi kicin din ta dauko abincin ta ta samu wuri kusa da ita ta zauna.

Saidai ta gama karyawan ta tsaf sannan ta kalli Kakale dake gefen ta da tun fara karyawanta magana bai shiga tsakaninsu bah sanna tace "Kakale kince idan na karya zamuyi magana"
Murmushi Inna tayi dan ita manyancen Slaim yakan bata dariya wasu lokutan musammman ma idan ta tuna dududu shekarun ta nawa suke amma Allah ya yitada tsaurin ido ga iya zaro zance kaman wata uwar mata.

Barin abinda take yi Kakale tayi ta juyo ta fukanci Slaim da kyau sannan ta ambaci sunanta cikin sanyin mirya Wanda hakan yasa Slaim dagowa ta kalleta itama kafin Kakale ta cigaba da cewa "nasan kinada qananan shekaru anman abubuwa da yawa sun faru arayuwan ki kin fisakanci qalubale kala,kala"
Shiru Kakale tayi na wasu Yan sakwanni kafi ta cigaba da fadin "Ina so ki manta komai arayuwan ki na baya ki fuskanci gaba Kuma gyara rayuwanki na gaba ki inganta shi ta hanyar sammar ma kanki ilimi mai ingabci ki koma makaranta saboda hakan ne kawai zai gyara miki rayuwanki"
Kakale ta kai qarshin maganan ta ba tareda ta dauke idonta daga kan Slaim bah wanda tunda Kakale ta fara magana kanta ke qasa.

Inna tasan halin Slaim da kafiya idan bataso yin abu bah shiyasa ta zaunar da ita ta mata magana ta hanyar da zata ga kaman shawara take bata bawai umarni bah.

Shiru wajen ya dauka na wasu Yan mintuna Slaim kaman bazata yi magana bah sannan tace "Kakale inaso ki fahimci cewa rayuwa bah dole sai naje makaranta zan samu rayuwa mai kyau da inganci bah kawai ki barni haka rayuwata bazata tartse bah anman ni duk wata karatun bokon nan ki barshi kawai ni baya gaba na fah"

"Haba Slaim wannan bah hanya mai billewa bane koh kadan baki dauki hanyar gyara rayuwanki bah"

Shuru ne ya biyo bayan maganan Kakale na kusan minti biyar zuwa shida kafin Slaim ta dauke wani nannauyan ajiyan zuciya sannan tace "toh shikenan Kakale zan koma makaranta insha Allahu" Slaim ta fada hade da miqeawa ta shige daki.

Tabbas Kakale ta ji dadin hakan Wanda ya sanya ta furta "Alhamdulillah" tareda lumshe ido

SLAIMWhere stories live. Discover now