chapter eight

406 43 2
                                    

🤍 INA ZAN GANTA..?🤍

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

08

Washegari misalin karfe uku na rana Mama ta shigo dakin Abba..yana zaune da waya a kunnenshi tun dazu..ta ajiye tray din data shigo dashi kan mirror snn ta isa kusa dashi ta zauna..a hankali tace"har yanxun number nashi bai shiga ba?.."Abba ya sauke numfashi kafin ya dago ya kalleta..cikeda damuwa yace"har yanzu wlh..I wonder what is wrong with him..gashi Kuma na riga nayima Hajjaju alqawari"..mama ta riko hannunshi kafin tace"dole haka zatayi hakuri har mu samu Alh Sanin a waya tunda shi kadai ne Wanda mukasan yasan address din"..Abba na girgiza kai yace"No bazan karya alqawarin da na daukan Mata ba"..tace"to yanxu ya kakeso ayi?.."tana rufe baki yace"zamuje Abuja gobe kmr yanda na fada mata..inyaso sai muje office din Alh Sanin mu nemeshi a can..nasan InshaAllah ko baya gari bazamu rasa samun contact dinshi ba"..mama tayi shiru kawai lokaci daya duk jikinta yayi sanyi..Abba ya janyota jikinshi yana patting bayanta yace"you don't have to worry InshaAllah zamuje mu dawo lafiya..Kuma InshaAllah bazasu ki yafe Mana ba..yanxu idan na fita zan fara zuwa in bincika idan zaa samu available flight to Abuja gobe..idan Kuma baa samuba sai muje a mota" ...itadai batace komai ba sai hawaye daya shiga zubowa kan fuskanta..batasan meyasa gaba daya taji batason tafiyar nan ba..haka nan takejin gabanta na faduwa tun jiya da yace zasuje..it's like tana jin tsoron faruwar wani abun ne..amma ba yanda ta iya dole haka zasuje..ko ba komai itama tanason reuniting da family dinta..ga Kuma Amal ko kadan bazata so tayi rayuwa irin wanda sukayi ba..rayuwa ba tareda family dinka ba..rayuwa ba tareda kowa naka ba..rayuwa ce mai matukar wahala duk da cewa kusan laifinsu ne...wnn tunanin ya Sanya kukan nata ya Kara karfi..har yanxu ta kasa mance incident din..ta kasa mance yanda komai ya faru..abun na nan cikin ranta tamkar baa kwashi tsawon shekara da Shekaru ba..

Karfe hudu Amal ta fito daga wanka daure da dan towel dinta..ta karasa ta dauki wayanta da takejin yanata ringing tun tana bayi..ta saki murmushi tana girgiza kai don dama tun da taji irin yanda aketa jera mata missed calls tasan shine..shi baisan wani abu hakuri ba kaf a rayuwarshi..ko zaiyi hour yana kiranta bata daukaba to haka zaiyita Kira har sai lokacin da ta dauka din..tayi picking tareda dan hade rai tace"you want to finish my battery"..tana rufe baki yace"am sorry..kin ganni fa tun dazu a kofar gidanku shine kika ki daukan wayana"..Saida ta dan buda ido snn tace"hearty har kazo wai..wane irin gudu kayi haka?.."ya murguda Mata baki kmr tana ganinshi yace"koma dai wane irin driving nayi babu ruwanki a ciki..nidai kawai ki fito idan kuma ba so kike na shigo cikin gidan ba"..taja stool dake gaban mirror dinta ta zauna snn tace"ka shigo din Mana in har zaka iya"..kmr zaisa kuka yace"hearty plss mana..don kinga na matsu in ganki kike jamin rai koh"..tana dariya tace"sorry hearty Kai din ne kayi saurin zuwa..ni yanxu na fito daga wanka ma ko shiryawa banyi ba"..da sauri yace"Ni ba sai kin wani tsaya shiryawa ba kawai ki fito a haka.. seriously ni ban damu da wani kwalliya ba I just want to see you"..tayi rolling idanuwanta kafin tace"at least dai ka bari nasa kaya koh"..ya saki wani makirin smile yana shafa kanshi snn yayi kasa da murya yace"No..just come out a yanda kike..I promise bazan ga komai ba and bazan aikata komai ba..idan ma na ga wani abu I'll pretend banga komai ba".. siririn tsaki ta saki before tace"am hanging off"..da sauri yace"plss don't..nida ki fito a haka dan Allah..kinji"..tace"naji"..snn ta katse Kiran..ta nufi closet dinta tana girgiza Kai tana fadin"hauka nakeyi in fita wurinka a haka..tabb in kaima kura ajiyar nama knn"..sai Kuma ta fashe da dariya..tun jiya data fada mashi yanda sukayi da Abba ya dage shi lallai sai yazo tace mishi yayi hakuri sai yau...ta fiddo kayan da zata sa da sauri ta fara sa inners dinta snn ta zura doguwan rigan..ta karasa gaban mirror ta fesa perfumes tareda dan shafa lotion jikinta snn ta yafa karamin mayafin rigan a Kai kafin ta dauki wayanta ta fice daga dakin...ta samu mama a kitchen ta fada Mata zataje wurinshi snn ta fita da saurinta...tana zuwa parlon da take saukeshi kawai sai ta ganshi a ciki..ta saki murmushi tareda karasawa ciki..tayi tunanin zaiyita zama a waje ne kmr yanda yakeyi sometimes..kujeran dake opposite to him ta zauna..shi kuma yayi kicin kicin ya wani hade giran sama dana qasa..Amal batasan lokacinda ta kwashe da dariya ba..yayi shiru kawai yana kallonta..ita kuwa Saida tayi me isarta snn ta bari..ya kalleta still fuska a tsuke yace"are you done?.."tana murmushi tace"yi hakuri"..yace"nayi..sai ki dawo nan ki zauna"..ya nuna kusa dashi..Amal ta makale kafada kafin tace"am comfortable here"..tana rufe baki yace"wane irin you are comfortable..I told you inaso inyita kallonki shine zaki wani je can ki zauna..it's not as if am going to touch you dan Allah ki dawo nan"..bata sake yin musu ba ta mike tareda komawa inda ya nuna matan ta zauna..shi kuma ya juyo da hankalinshi gabaki daya kanta..ya zuba Mata idanunshi kafin yace"so ya jikinki"..tace"Alhamdulillah na warke"..yace"good..yanxu gobe war haka kina Abuja kin barni"..tace"ai ba dadewa zamuyi a can ba"..ya karya wuya Yana cewa"dukda haka am going to miss you..sai naji dama hutuna ya qare nima in koma kinga saidai kawai ki turomin address inzo"..itama tayi kasa da murya tace"zamuna yin waya ai"..yace"yeah..do you know what makes me happy?.."ta girgiza mishi Kai..ya saki murmushi kafin yace"idan na tuna kuna dawowa zaayi fixing date din bikinmu sai inji sanyi a raina"..ta zaro idanu tana kallonshi tace"Really..wa ya fada maka?.."tana rufe baki yace"come on hearty har sai na jira wani ya fadamin ma..zuwa kawai zanyi in samu Daddy ince mashi nidai aure nakeso shi Kuma sai yazo suyi mgn da Abba"..Amal ta dafa goshi tana cewa"Allah ya shiryamin kai hearty"..shima yaja kumatunta before saying"Ameen Ameen my Heart"..daga haka ya zura hannu cikin aljihunshi sai gashi ya fito da wani box mai kyau..ya dunkule abun a hannunshi kafin yace"bring your hand"..batayi musu ba ta Mika mashi hannunta..ya ciro abun dake cikin box din ya nufi hannunta dashi..ya daura Mata abun daidai wrist dinta...lokaci daya ta wara idanu sosae tana kallon diamond bracelet din da sai shinning yake yana daukar ido...ta matsar da hannun nata saitin idonta yanda zataga rubutun dake jiki da kyau..AmBash...shine sunan data ga an rubutu jikin bracelet din..ta lumshe idanu tana tuno ranar daya fara hada musu wnn sunan..hatta password din wayanshi dana sauran abubuwanshi abinda yasa knn..ta bude hannayenta cikeda murna zatayi hugging dinshi sai kuma ta tsaya cak kmr wanda ta tuna da wani abun..lokaci daya ta koma baya da sauri tareda yin kasa da kanta..duk kunya ya isheta..shi Kuma Bahseer dake kallonta yace"hearty dan Allah hug me mana..me yasa kika fasa"..batace komai ba sai dagowa da tayi ta galla mishi harara..shi Kuma yasa dariya kafin ya sake dauko wani bracelet din a aljihunshi..ya mika mata shi snn yace"now it's your turn"..ta dago idanunta ta saukesu kan bracelet din..iri dayane exactly da nata..har sunan ma iri daya ne a jiki..ba tayi musu ba ta karba shima ta sa mishi a wrist dinshi..tana gamawa yakai hannun bakinshi yayi kissing tareda kashe mata ido..ita Kuma ta kauda kanta gefe tana murmushi..cikin ranta ko Fadi take"Ya Allah ka shirya wnn bawa naka"..kmr daga sama taji yace"do you like it?.."da sauri tace"sosae ma..yayi kyau sosae and I love it"..ya wani shagwabe fuska hadda turo baki yana kallonta...ita Kuma ta saki smile kafin tace"but I Love you more than anything..I love you so much"...kasa hakura yayi Saida yayi hugging dinta..murya can kasa ya rada Mata"and I love you more my heart..inasonki fiyeda yanda duk kike tsammani"...
A takaice dai Basheer na  gidan har akayi sallahn Isha..Abba kanshi Saida yayi mamaki da yaga har yanxu motanshi na compound din gidan..yayi murmushi kawai snn ya shiga ciki..don dawowarshi knn daga masallaci..jin motsi a kitchen yasan mama na ciki knn..don haka ya wuce kitchen din shima direct..tana kokarin fitowa da tray a hannunta suka ci karo..ya amsa tray din hannun nata suka fito daga kitchen din yana cewa"wai har yanxu yaron nan bai tafi ba?.."Mama ta dan tabe baki tana"Nima abinda nake ta fada knn tun dazu..sai in rasa me suke cewa ne haka kusan awa biyar ana abu daya"...Abba dake murmushi ya karasa dinning ya ajiye tray din hannunshi..snn ya juya yana facing dinta yace"duk abinda zasuyi nasan ko kafar mu basu kama ba..ko kin manta yanda mukayi namu lokacin ne"..Mama ta kauda Kai gefe tace"nidai a bar mgnr nan Yaya"..ya janyota jikinshi yace"no sai mun karasa ta..ki fada min idan kin manta yanxun nan in tuna maki"..a hankali tace"Dan Allah mubar mgnr nan..banason Ina tunawa da abubuwan da suka faru"..ganin kmr kuka zatayi Abba yace"na Dena..bazan karaba InshaAllah..yanxu bari in kira Basheer din dama Ina sonyin mgn dashi"..Mama ta daga mishi Kai..shi Kuma ya saketa tareda komawa parlor..bayan ya zauna sai ya dauki waya har zai Kira number Amal sai Kuma ya fasa ya Kira na Basheer din...suna zaune tana ta faman ce mishi yazo ya wuce don tasan Abba ya dawo shi Kuma yana cewa shi bai gaji da ganinta ba..Kiran na shigowa da yaga Abba sai ya dora hannu a Kai tareda zare duk idanuwanshi waje tamkar Wanda yaga abun tsoro..Amal na dubanshi da mamaki tace"meya faru Kuma?.."baice komai ba sai wayan daya nuna Mata..ta saki murmushi hadda su girgiza kai tana cewa"Very good..nasan cewa zaiyi kazo ka wuce gida haka nan dare yayi"..baice Mata komai ba har Saida yaga Kiran ya kusa katsewa snn yayi picking...Abba yace"Bash kana jina..ka shigo ciki ka sameni kafin ka wuce..akwai mgnr da nakeson yi da Kai".. Basheer ya hadiye wani yawu da kyar kafin yace"to Abba gani nan..dama yanzu nake Shirin tafiya"...Abba baice komai ba yayi hanging call din Yana murmushi...Basheer ya dubi Amal daketa faman dirka mishi dariya tun dazu..baice komai ba sai da ya mike snn yace Mata"idan kin gama dariyan sai ki tashi ki rakani wurinshi..he said he wants to talk to me"...ta tsaida dariyan nata snn ta mike itama..tana gaba Yana binta a baya har suka shiga main parlor dinsu..Abba ne zaune shi kadai..suka karasa cikin parlon..Basheer kai a kasa ya shiga kokarin zama nan kan carpet sai ji yayi Abba ya rikoshi ya zaunar dashi kusa dashi..ya sake yin kasa da kai yana jin kmr kasa ta tsage ya boye kanshi ciki don kunya..shi kanshi bai San yanada kunya har haka ba..bai sake tsinkewa da al'amarin ba sai da yaji Abba na cewa"Hajjaju je ki kawo mana abinci"..Amal ta mike da sauri ta tafi dinning..ta dauko musu tray din gaba daya don already mama ta gama shirya komai...ta dawo nan parlon ta ajiye kan center table snn ta fara serving dinsu..tanayi tana kallon Bahseer ta gefen idonta da yayi wani lakwas sai kace na Allah..tana gamawa tayi pouring musu drink a cups snn ta juya ta tafi tana dariya kasa kasa..ita dariya ma yake bata wlh..bata taba tunanin ya san da wani abu mai suna kunya ba...Abba yace"to Bash Bismillah ga abinci"...Basheer ya sake noke kai kasa..duk ya kirashi Bash din nan sai yaji wani iri wlh..dukda dama haka Daddy ke kiranshi.. Hardly ya kirashi da Basheer saidai Bash..da dai mommy ne Kam ita wnn tafi kowa iya Kiran Basheer din ma..har wani gunna takema sunan...Abba da har yakai spoon na biyu bakinshi ya juya yana kallon Basheer din yace"ya dai..ko bazaka iya cin abinci dani ba?.."da sauri ya dauki spoon din ya fara ci...Abba yace"ka saki jikinka dani..consider me as your Dad"..a hankali Basheer dake ta faman yake yace"InshaAllah Abba"..daga haka suka cigaba da cin abincin...Basheer tun Yanada jin kunya har ya dan ware yaci sosae...bayan sun kammala Abba yace"dama mgn ce nakeso muyi akan rashin lafiyan Hajjaju..kasan tanada Asthma koh"..a hankali Bash yace"na sani Abba"...Abba yace"Alhamdulillah..nasan ko babu aure kai mai kula Mana da ita ne tunda nida mahaifinki tamkar yan uwa muke..kaf girman kano banada Wanda ya fishi..he's like a brother to me..Dan Allah amanarta zan baka Basheer..nasan you are a very good boy shiyasa na amince zan baka aurenta..Kuma Ina sa rai InshaAllah ko babu raina zaka kula da ita yanda ya kamata..ka kula da ita sosae Basheer ka riketa tamkar 'kanwarka..kaga ita kenan Allah ya bamu..inaso kayi mata rikon da ko bayan ranmu bazata yi kukan rashin gata ba..inaso ka zame Mata uwa..uba..snn ka zama dan uwa a gareta..itama kuma InshaAllah zata zauna dakai lfy"..Basheer da duk jikinshi yayi sanyi da mgnr abban yace"InshaAllah zan riketa Amana Abba.. Bi'iznillah bazakayi dana sanin bani amanarta ba"..cikeda gamsuwa Abba yace"Alhamdulillah nagode..nogede sosae..Allah yayi Albarka Allah Kuma ya tabbatar da alkhairi"..a hankali Bash yace"Ameen Abba"..suka danyi shiru for sometimes kafin Abba yace"in Allah yakaimu gobe zamu tafi Abuja..inaso inyi introducing dinta wa family and InshaAllah Muna dawowa zaa tsaida lokacin bikinku kmr yanda mukayi mgn da mahaifinka"...Basheer ya wani lumshe ido yanajin wani irin farin ciki na mamaye zuciyarshi..wnn magana ba karamin faranta ranshi yayi ba..cikin zuciyarshi yace"you shall live long abbanmu"..a zahiri Kuma sai yace"Abba nagode Allah ya saka da alkhairi..Allah ya Kara girma"...Abba na murmushi yace"Ameen Ameen"...Shi Kuma Basheer ya mike tsaye kanshi a kasa ya sake cewa"ni zan wuce Abba..Allah ya kiyaye hanya"..Abba yace"Ameen ya Allah..bari a kirata sai kuyi sallama koh"..Saida ya kama hanyar fita snn yace"to Abba..Saida safe"..daga haka ya fice daga parlon feeling extraordinary Happy...shi kuwa Abba binshi yayi da kallo..yaji yana Kara son yaron sosae..ya tabbata Kuma bazasuyi Dana sanin bashi auren Amal ba Bi'iznillah...a waya ya Kira Amal din yace tazo suyi sallama da Basheer...ba musu ta fito tana sanyeda katon hijabinta...tana zuwa parlor Abba yace"Yana waje"..batace komai ba ta kama hanyan wajen...can ta sameshi tsaye jikin motanshi...ta karasa wurin da murmushi kan fuskanta..tun kafin tayi mgn yace"hearty guess what?.."tace"what?.."Saida ya rungume hannayenshi a kirji fuskan nn kmr gonar auduga sbd fara'a yace"Abba yace Kuna dawowa zaayi fixing date din bikinmu..ohh I just can't wait hearty..am super excited"..itama rungume hannun nata tayi tana dubanshi da murmushi tace"shine kaketa washe mana baki kmr gonar auduga"...yayi shiru yana kallonta kafin ya gyada kanshi yace"it's ohk ba laifinki bane..duk kika kuskura kika shigo hannuna wlh no mercy..ko kadan bazan tausaya maki bane"..ya karasa mgnr da wani shegen murmushi kan face dinshi..ita Kuma  Amal dan tabe baki tayi tana cewa"Kai dai bakada kunya wlh"..ya Mika hanu zai kamota taja baya da sauri tana hararanshi..shi Kuma yana murmushi ya bude mota ya shiga..yayi winning glass yana kallonta kasa kasa yace"to bazaki zo nayi maki kallon karshe ba?.."tana murguda baki tace"as if idan na tafi bazan dawo ba"..ya wani karya wuya yace"to nidai come close in ganki plss"..tace"a nan din baka ganina ne"..yace"no..I want to smell your perfume..kinga idan kuka tafi duk ba ganinki zan nayi ba"..tayi kmr bataji ba ta dauke kanta gefe..ya sake narke Mata yace"kinji Meeno plss..Dan Allah"...a hankali tayi taking two steps forward..tana kallon yanda duk yayi da face dinshi kmr wani baby kawai sai tasa dariya..tana girgiza kai tace"kasan wani abu hearty?.."ya girgiza Mata Kai a hankali..ta sake taking steps forward kafin tace"you haven't become a man yet..you are still a child"..ya murguda Mata baki yana cewa"naji..just continue calling me a child zakisha mamaki na watarana..duk kika shigo hannuna I bet bazaki sake cewa am a child ba daga ranan".. girgiza kai kawai tayi kafin tace"to sai da safe"..yace"Allah ya kaimu"...daga haka bata sake yin mgn ba tajuya ta wuce ciki..tasan idan tacigaba da biye mishi sai su sake daukan wasu awannin suna abu daya..batasan meyasa maza basuda kunya ba wlh...

Team#AmBash❤️🔐this one is for you🥰

Mum Ashraf ✨

🤍 INA ZAN GANTA..?🤍Where stories live. Discover now