Hateful

196 26 10
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2021.

      *♡KALLO YA KOMA SAMA¸.•💥*
        _((SHAHO YA ƊAUKO GIWA))_

'''#ƊAN MACE AGAIN'''
         
            

   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*WATTPAD LINK:* https://www.wattpad.com/story/231697613?utm_medium=com.whatsapp&utm_source=android&utm_content=story_info

                            02

#Hateful

       After few hours jirginsu Jay yayi arriving,he first stop a Lagos state,sanda yayi changing flight sannan suka nufo Kano,tunda Jay ya taho bai kira kowa a gida ya sanar yana hanya ba,duk da tsayin lokacin da ya ɗauka rabonsa da zuwa,sanda jirginsu yayi arriving airport na Malam Aminu Kano International airport ya fito ya nemi cab da zai kaisa gida,a hanya suna tafiya ya fara ƙoƙarin kiran Khaniiy,wayar yana shiga ta ɗauka da sanyin murya tace "assalamu alaikum!" A hankali Jay ya lumshe idanuwansa yace "wa'alaikumus salaam.. How are u? Hope Baby na ba ya takura ki" dariya tayi mai sauti tana shafa cikinta tace "i'm fine.. Sai kewarka da nake ji yana zagaya every vein ɗina" yayi sanyayyan murmushi kafin yayi magana tace "har kun sauka?" Yace "yeah! Not too long" ta gyaɗa kai tace "maa sha Allah.. Kun je lafiya?" Yace "alhamdulillah! Where's my boy? Ban jisa ba? Bai zo tayaki hira ba?" Tace "yana can gurin Ammi" ya gyaɗa kai yace "okay! Za muyi waya idan na ƙarasa gida,muna hanya yanzu" a hankali tace "tou! Allah kaiku lafiya" yace "ameen!" Calmly tace "bye" yace "bye.. I love u" tana sakin sanyayyan murmushinta tace "love u too" sanda ta masa kiss then ta sauke wayar daga kunnenta tana sauke numfashi. Murmushi Jay ya dunga zubawa idanunsa a lumshe a haka suka dunga tafiya,sanda suka hau Emir palace road,gaba ɗaya zuciyarsa wani irin rawa ta dunga yi,ya daure yana karanto different addu'o'i a ransa idanuwansa a lumshe,har driver yayi parking bai sani ba sai da yace "mai gida mun ƙara so,sai da ka sauka a nan,ka san dogarai baza su barni na shiga ciki ba" a hankali Jay yake buɗe idanunsa sanda ya sauke su kan babban building ɗin da suke tsaye gabansa mai wani irin ƙaton ƙofa dake ɗauke da tambarin sarauta,jikinsa a sanyaye ya buɗe ƙofar motar ya sauka,ya fara sallamar mai cab then yaja luggage ɗinsa walking slowly,sanda yake shiga ƙofofin da suke buɗe yana tafiya kan lafiyayyen titin daya ratsa ya shiga cikin gidan,almost 20 dogaran da suke tsaron ƙofar suna ganinsa suka fara masa barka da zuwa,yayi murmushi yana amsawa,wani dogari dake sanye da kaya irin nasu na bayi green and red ya taso da gudu² ya karɓi luggage ɗin ya bisa da shi,duk inda suka wuce bayi ne suke zubewa suna gaishesa da yi masa barka da zuwa,Jay sai kallon gidan nasu yake yi saboda yanda akayi masa gyara sosai,an sabunta gininsa ya dawo modern building,sun yi tafiya mai nisan gaske kafin su fara shigowa asalin gidan,babban traditional building irin na gidan sarauta mai ɗauke da apartments masu mugun yawa,can wani apartment da yafi kowanne haɗuwa a ciki zanen sarauta ta ko'ina suka nufa,sanda suka shiga harabar gidan,Jay a forefront yayi sallama bakin parlon kafin ya shiga,daga cikin babban parlon can gefe gurin da yake shimfiɗe da kilisai da manyan tumtum na alfarma wata kyakkyawar mata fara dake kishingiɗe ta ɗago fuskarta ɗauke da fara'a ta amsa sallamarsa,kana kallonta ka ga Jay because they look alike,takalminsa Jay ya tsaya cirewa,da hannu ta yiwa kunyangin da suke kewaye da ita alama su je,cikin sauri duk suka tashi za su fita,sanda suka ƙarasa inda Jay yake suka gaisheshi,ya amsa ya ƙarasa gurin da mahaifiyarsa take ya zauna gabanta yayi flexing legs ɗinsa a hankali idanuwansa a ƙasa yace "barka da hutawa Mami na" kallonsa take fuskarta ɗauke da annuri,duk irin fushin da take yi da shi,gaba ɗaya ta kasa ɓoye farin cikinta tace "kana lafiya?" Yace "alhamdulillah! Mami na,na same ku lafiya?" Tace "lafiya alhamdulillah,kun sauka lafiya?" Yace "lafiya lau" tace "maa sha Allah! Ya hanya?" Yace "alhamdulillah Mami" ɗan shiru suka yi tana kallonsa,ganin yanda yayi wani fresh ya yi ƙiba,tana murmushi irin na su na sarakai tace "da alama ƙasar nan yana maka daɗi,tunda ka iya mantawa da mu" Jay yayi murmushi yana shafa sumar kansa shyly yace "ba haka bane Mami,yanayin aikin ne yasa ba na samun lokaci nazo" Mami tana girgiza kai tace "Haba *MUJAHEED* ni fa na haifeka,ba kai ka haife ni ba,wani aiki ne haka da ba'a samun lokacin yin ziyara? Kada ka manta every year kuna ɗaukan hutu,amma yaushe rabonka da zuwa ka duba mu? Sai dai ka kira mu a waya,shima ba sosai ba da mun fara magana za kace kana da uzuri,kamar wanda yake kan ƙaya,anya Mujaheed hanyar da ka ɗauka zai kai maka?" Kan Jay a ƙasa yace "I'm sorry Mami,na san na yi laifi.." A hankali ta girgiza masa kai tace "it's okay! Ka shiga ka huta,za'a kawo maka abinci,an jima sai muyi hiran" jikinsa a ɗan sanyaye ya amsa ya tashi yana tafiya,Mami ta bisa da kallo har ya wuce ya shiga wani ƙofa. Sanda ya wuce wani parlon kafin ya shiga corridor,a nan ya sake bi ta wani passage da ya kaisa wani underground part,yabi stairs ya sauka,sanda ya tsaya gaban only door dake gurin yasa key ya buɗe ƙofar ya shiga,a hankali ya sauke nauyayyan ajiyar zuciya ya ƙarasa cikin haɗaɗɗen parlonsa da yaji wasu irin chairs na alfarma komai na ciki silver ash sai ƙamshi da sanyi da suka cika parlon,walking happily ya wuce ya nufi ɗaya daga bedroom ɗinsa,shima dai ba'a cewa komai saboda tsaruwarsa,komai na ciki white colour,arean makeken royal bed ɗinsa ya ƙarasa ya sauke jacket ɗinsa ya zube wayoyinsa,ya kwance agogon wrist da neck tie ɗinsa then ya fara cire sleeve shirt dake jikinsa,slowly yake tafiya kamar wanda yayi loosing kuzarinsa ya wuce bathroom,ruwa ya fara sakarwa jikinsa kafin ya ɗauro alwala ya fito,cikin nutsuwa ya gama shiryawa cikin wani Men jallabiya mai haɗe da wando milk colour,ya zura ƙafafunsa cikin half cover shoe irin na saraki mai taushi da aka yi adorning da feathers,a nutse yake takunsa ya fito parlonsa,here yaga luggage ɗinsa ajiye a gefe bawan da ya rakosa ya ajiye saboda ba kowane bawa ne yake da damar shigar masa bedroom ba,bai fara nufar gurin ba ya fita yana haurawa sama,sanda ya nufo parlon Maminsa ya tarar da ita tare da hadimanta suna hira,ta ɗago ta bisa da kallo fuskarta da murmushi,shi dai Jay gaba ɗaya ya kasa haɗa ido da mahaifiyar tasa,sanda ya ɗan tsaya da tafiyar a hankali yace "Mami zan shiga gurin Hjy Babba na dawo" tana kallonsa tace "abincin fa?" Yace "idan na dawo zan ci" tace "okay! But za ka je ku gaisa da Mai martaba ne?" Yace "ai ban san inda yake ba.." Tace "apartment ɗin Gimbiya Habibah" Yana girgiza kai da sauri yace "a'a.." Mami dake kallonsa tace "ko saboda me?" Da sauri yace "Mami bari dai naje na dawo" tace "tunda fita za kayi ka ƙarasa ɓangaren gimbiya Habiba ka gaisheta.. Definitely na san za kaje ka gaishe da Fulani,ka tabbatar kafin ka dawo ka je ka gaisheta" saurin waigowa yayi yana kallon mahaifiyar tasa,fuskarsa babu wani walwala yace  "Mami kin san fa ba na son zuwa apartment ɗinta" tace "kuma ya zama dole kaje ka gaisheta,saboda baza ka janyo min magana ba" a hankali ya gyaɗa kai yace "shi kenan" ya juya ransa a ɓace ya fita,ta ɗauke kai tana cin yankakken fruit dake gabanta,sanda ya fito a fusace yake tafiya,a hanya bayi sai gaishesa suke bai iya amsawa ba sai dai ya ɗaga musu hannu ya wuce,sanda ya ƙaraso wani apartment sak irin na mahaifiyarsa yayi sallama bakin ƙofar shiga,kai tsaye ya wuce bai jira neman izini ba,kunyangin da suke ɓangaren suna masa barka da zuwa,ya amsa fuskarsa a ɗaure yayi sallama ƙofar shiga parlon haɗe da tsayawa kaɗan,wata baiwa ta leƙo da alamun itace sabuwar jaadiyar da akayi bayan rasuwar wancan,tana ganinsa ta zube tana gaishesa,a dake ya amsa yace "Abba fa?" Tace "yana ciki,bari a sanar masa" yace "okay" yana tsaye gurin ta fito tace "kana iya shiga" bai jira ba ya wuceta,da sallama ya shiga kansa a ƙasa,su biyu ne a parlon dattijon ɗan kimanin 84yrs sai wata mata dake gefensa mai dark skin da baza ta wuce 57yrs ba,dattijon kawai ya amsa sallamarsa fuskantarsa da fara'a,yana kallon Jay da izza irin ta sarakai a maganarsa yace "kamar Mujaheed nake gani.. Ko dai mafarki nake yi?" Jay ya ƙarasa kusa da Abbansa ya zauna a hankali yace "nine Abba" Mai martaba yana kallon ɗan nasa yace "sai yau ka iya tunawa muna nan a raye,kaga ya dace kazo ka ganmu?" Jay ya sake yin ƙasa da kai yace "I'm sorry Abba" Mai martaba yace "idan ban yi haƙuri ba ya kake so nayi dakai Mujaheed?" Jay yayi shiru,Mai martaba yace "yaushe kazo ƙasar?" Yace "not too long" jinjina kai Mai martaba yayi bai dai ce komai ba,a hankali Jay yace "barka da yamma Abba" Mai martaba yace "muna lafiya?" Jay yace "lafiya lau Abba" yace "ya aikin?" Jay yace "alhamdulillah Abba" Mai martaba yace "kun samu hutu ne?" Kai ya gyaɗa kaɗan yace "ehhh Abba" Mai martaba yace "maa sha Allah,Allah taimaka,amma dai Mujaheed ya kamata ka yiwa kanka faɗa,ko dan ganin mun zuba maka ido kana abunda kaga dama shisa baka damu da zuwa ka duba mu ba?" Kan Jay a ƙasa yace "ayi haƙuri Abba" nasiha sosai Mai martaba yayi masa,ta gefen ido Jay yake kallon matar mahaifin nasa,sanda Mai martaba ya gama masa faɗan cikin tausasa murya,then Jay ya juya fuskarsa ɗaure yace "ina yini?" Tana yatsina fuska ta amsa a daƙile "lafiya.." Daga haka Jay ya tashi yace "sai an jima Abba" Mai martaba yace "baza ka tsaya muyi hira ba?" Ɗan murmushi yayi yace "zan je mu gaisa da Hjy Babba,daga can zan shiga gurin Fulani da sauran mutanen gidan" Mai martaba yace "tou shi kenan,ka gaisheta" daga haka yayi masa sallama ya fita ɓangaren,wani apartment dake can gaba ya nufa,yayi sallama ƙofar parlon,tun kafin ya ƙarasa shiga Dattijuwar mai tarin shekaru ta amsa tana faɗin "lale marhabun da Mujaheed" sai lokacin ya saki fuskarsa ya ƙarasa ya zauna a gabanta a kan ƙafafuwansa with full respect,matar mai cikar kamala ta kai hannu ta dafa kansa tana faɗin "Allah ya yi maka albarka,ya tsare min kai ya raba ka da dukkan abin ƙi,ya kare ka sharrin mutun da aljan.." Jay ya amsa da "ameen" kansa a ƙasa yace "barka da hutawa Kakata abar alfahari na,matar sarki,kuma mahaifiyar sarki.. Kin ga zamanin ki,kinga na ƴaƴan ki da jikoki,saura na ƴaƴansu.." Tayi murmushi irin nasu na masu mulki,tace "wata rana idan Allah ya nufa ina da tsayin rai sai naga ranar da za ka zama sarki kuma.." Murmushi yayi sosai yace "a'a Hjy na haƙura a bawa wani" tace "ka taɓa ganin inda mutum yake ƙin gadon gidansu?" Yayi murmushi yace "ni dai Hjy mu bar maganar nan,kada ki ɓata min rai daga zuwa na" da idanu ta bishi tace "kai fa ba ka son gaskiya Mujaheed.. Shin idan Ubangiji ya nufa za ka hana haka faruwa ne?" Yayi shiru bai ce komai ba,tace "ka gama duk gudun naka,idan Allah ya tsara za kayi mulki babu yanda za kayi dole ka karɓa" Jay dai baice komai ba,here suka fara hira irin na yaushe gamo,a nan tasa aka jera masa kayan abinci da cinye² iri²,sai da aka fara kiran maghreb sannan yayi mata sallama ya fita masjeed,daga can ko da ya fito ya shiga apartment ɗin Fulani,sun jima suna hira cike da barkwanci then yayi mata sallama,sanda yayi sallar ishaa sannan ya shiga apartments ɗin baffaninsa,daga nan ya wuce apartment ɗinsu,ya samu Maminsa zaune tana lazimi,ya zauna saman armchair ya miƙe ƙafafuwansa a kan coach har sanda ta idar then suka gaisa,tana kallonsa tace "sai na jika shiru kuma da ka fita" yana sakin murmushi yace "Hjy ta riƙe ni da naje gurinta" Mami ta gyaɗa kai tace "abinci fa?" Yace "na ci a can" ta gyaɗa kai tace "dama na san za'ayi haka.. Ka shiga kun gaisa da baffaninka?" Yace "ehh! Daga can nake" tace "maa sha Allah" nan suka ɗan taɓa hira,around 9pm ya tashi yayi mata sallama yace "Mami zanje na kwanta sai da safe" tace "Allah ya tashe mu da alkhairi" yace "ameen.." Dai² lokacin yana shiga bedroom ɗinsa kiran da akayi masa yana katsewa sai haskenta ya gani,ya buɗa idanunsa da sauri ya ƙarasa ya ɗauki wayar yana duba tarin missed calls da Khaniiy tayi masa,komawa yayi ya zauna saman resting chair then ya shiga kiranta,wayar yana shiga tayi picking up haɗe da fashewa da wani irin kuka,hankalin Jay a tashe ya buɗa idanunsa yace "what happened Khaniiy? What are u crying for?" Bata iya bashi amsa ba sanda tayi mai isarta tana sauke ajiyar zuciya tace "Jay ina ka shiga ka manta da ni?" Ajiyar zuciya yayi cikin sanyin murya yace "I'm really sorry Khaniiy.. Ba mantawa nayi dake ba,kin san babu yanda za'ayi na manta  dake,u're the source of my happiness,and my everything,na shiga cikin gida muna gaisawa da Uncles ɗina,and na bar wayoyina a ɗaki ban fita da su ba" wani sanyayyan ajiyar zuciya tayi tana goge hawaye tace "dan Allah Jay kada ka manta da ni ka ji?" Yace "yeh kya hai Khaniiy? (What's this Khaniiy?)" Tace "tun kafin ka tafi jikina yake sanar min wani abu zai faru,no matter what kada ka barni Jay,ba zan iya jurewa rashin ka a kusa da ni ba,promise me u won't leave me" murmushi Jay yayı yace "i promise i won't leave u" tace "thank u Jay.. Thank u for loving me,and da aurena da kayi" sanda ya kwantar mata da hankali then suka fara hira tana tambayarsa Nigeria da mutanen gida,yace "duk suna lafiya" sun ɓata lokaci mai tsayi kafin yace mata zai je yayi wanka idan ya fito zai sake kiranta,suka yi sallama tana tsokanarsa ko tazo ta tayasa? Yayi murmushi yace "ki gama tsokanata duk sanda muka haɗu u'll avenge me" sanda suka ajiye wayar Jay ya tashi yana sakin murmushi ya fara cire kayansa ya wuce bathroom,yana fitowa ya shirya cikin pyjamas ya haura gado ya kwanta,ya ɗauki wayarsa ya sake kiran Khaniiy video. Lokacin Khaniiy tana kwance rungume da Aslam da yayi bacci tana shafa sumar kansa,kiran yana shigowa tayi saurin ɗauka tana kallonsa tayi masa murmushi tace "assalamu alaikum" yace "wa'alaikumus salaam,aap kaise hain?" Ta lumshe idanu tace "main theek hoon,kai fa?" Yace "alhamdulillah.. Na gaji sosai ina son yin bacci but na kasa yin hakan" murmushi tayi tace "ohh! Gashi ba gari ɗaya muke ba" yace "haan! Me za kiyi min da zai sa nayi bacci da wuri?" Tace "komai kake so zan maka" yace "na yarda dake shi yasa ba na shakka akan ki,komai za ki iya yi min" hira irin na masoya suka sha sai da suka raba daren kafin suka yi sallama,nan da nan bacci ya ɗauke Jay. Da asubah kusan makara yayi,lokacin da ya farka ana kiran assalat,a gaggauce ya sauka daga gadon ya wuce bathroom,sanda yayi wanka ya ɗauro alwala then ya fito,sweet pant yasa yasa jallabiya ya fesa turare ya fito ƙafarsa sakaye cikin slippers ya fita masjeed,da aka idar da sallah bai dawo gidan ba sai da gari ya fara haske sannan ya shigo,bayan ya tsaya gurin Mami sun gaisa then ya wuce part ɗinsa,Khaniiy ya fara kira to make sure ta tashi ta yi sallah on time,sannan ya koma ya sake kwanciya,ba shi ya farka ba sai around 10am,sanda yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya ya fito gurin Mami,a nan yayi breakfast sannan ya fita ya shiga gurin Hjy Babba suka gaisa then ya koma apartment ɗin Mami ya sanar mata zai fita duba gidan gonarsa ya dawo,tana kallonsa tace "amma baza ka bari ka huta ba daga zuwanka za ka ɗauki ƙafa ka fara yawo" yayi murmushi yace "Mami bazan jima ba zan dawo" ta gyaɗa kai tace "shi kenan Allah tsare hanya" ya amsa da "ameen" ya fita yana cewa sai ya dawo,a hankaya yana tafiya yaga ƙannensa ƴaƴan gimbiya Habiba,da na gurin Fulani,kasancewar shi kaɗai ne namiji gurin Abbansa,sauran da suke binsa da wanda yake bi duk mata ne daga wanda suke uwa ɗaya har wanda suke uba kawai suka haɗa,babu wanda ta gaisheshi ya wuce bai damu da ko kallonsu yayi ba,yana tafiya bayin gidan sai gaisheshi suke,babban parking spot ya wuce ya buɗe wani Prado ya shiga,ya yiwa motar key ya fice daga gidan,duk da glasses ɗin wasu tinted amma hakan ba ya hana bayi gaisheshi ba,tafiyar almost 40 minutes yayi ya iso wani mararraba,sanda ya sauka daga main road ɗin ya ɗauki hanyar shiga garin,duk da rashin hanya mai kyau bai fi tafiyar mintuna 5 yayi ba ya tsaya wani get mai ɗauke da symbol dake nuni da gidan gona ne gurin,yayi horn dai² get ɗin,da gudu² mai gadi ya fito ya buɗe masa,ya sauke glasses ɗin ya yiwa dattijon sallama suka gaisa,yana masa barka da zuwa,Jay ya wuce ya shiga,daga get ɗin sai da yayi tafiya mai nisan gaske kafin yayi reaching manyan ɗakunan kiwonsa,girman gurin kansa abun kallo ne,korayen ciyayi da suka yi shar sun yi adorning gurin,fitowa Jay yayi bayan ya gyara parking yana amsa gaisuwar da masu kula da gurin suke masa,da fara'a yake tambayarsu aiki,then wanda yake shugaban gurin yayi masa jagora yana nuna masa ci gaban da aka samu,part daban² na gurin duk sai da ya shiga ya duba,kama daga ɓangaren kaji,talotalo,shanu da kifaye,tunda yazo gurin suke waya da Khaniiy ya ɗauki pictures ya tura mata tana ta masa dariya ganin yanda yayi shiga kamar shi ne yake aikin kula da dabbobin nasa,sanda suka yi sallar zuhur ya yiwa ma'aikatan nasa alkhairi then yayi sallama da su ya shiga mota zai tafi,fiye da rabin ma'aikatan gurin mazauna ƙauyen ne ya ɗebo ya basu aiki a gurin,har baƙin mota suka rakosa suna masa addu'ar sauka lafiya,sanda ya baro gidan gonar sai da ya tsaya ya siya zuma a hanya then ya nufo gida,yana shigowa yayi parking yasa hadimai su shigo da manyan jarkokin fresh milk da ya taho da shi,a ɓangaren Maminsa ya samu Mai martaba,ya ƙarasa da fara'a a fuskarsa ya zauna kusa da shi yana gaisheshi,cikin kulawa Mai martaba ya amsa yana dafa kansa,ya gaisar da Maminsa dake kallonsa tace "ka dawo?" Yace "ehh Mami" Mai martaba ya kallesu yace "wani waje yaje ne?" Tayi murmushi tace "ya je duba gidan gonarsa" Mai martaba yayi murmushi yace "ina fatan ka taho min da tsaraba ta?" Shafa beard ɗinsa yayi yace "Abba ai baka bada sautu ba" Mai martaba yace "wasa kake,ko ban baka sautu ba ai ka sani" murmushi Jay yayi kafin yayi magana hadimai suka shigo da jarkokin fresh milk ɗin da yazo da shi,sai wani na pure zuma da ya siyo saboda mahaifin nasa,Mai martaba ya kalleshi yace "ka mayar da ni abokin wasan ko kou?" Jay yayi dariya bai ce komai ba,Mami ta tashi ta ɗauki wani mug ta cikasa da fresh milk ta kawowa Mai martaba,take ya shaye yayi hamdala ga Ubangiji yana sanyawa Jay albarka,a nan ya shiririce suna hira da iyayensa cike da farin ciki. Kwanan Jay biyar da zuwa Nigeria,amma gaba ɗaya sau ɗaya ya shiga apartment ɗin Gimbiya Habiba saboda rashin shirin da suke,apartment ɗin Fulani kuwa kullum ne sai ya je sun yi hira,ko Abban nasa yana ɓangaren Gimbiya Habiba ba ya zuwa sai ya daidaici lokacin fitowarsa sannan yake zuwa su gaisa,ranar yana shiga apartment ɗin Hjy Babba ya hango Gimbiya Habiba zaune gaban Hjy,ɗan dakatawa yayi yana kallon yanda ta nutsu kanta a ƙasa tana yiwa Hjy Babba magana,lokaci ɗaya yaji ransa ya ɓaci da sauri ya juya da niyyar komawa,Hjy Babba data hangosa ta kirasa *"MUJAHEED!"* Cak ya tsaya a gurin sai dai ya kasa juyawa,tana kallonsa tace "kiranka nake dawo maza kazo ka same ni,magana nake so muyi da kai.." Juyawa yayi yana kallonta ya kasa ɗaga ƙafarsa ya ƙarasa gurin da suke,ganin haka Hjy dake kallonsa tace "ko ubanka na kira bai isa ya tsaya yana kallona haka ba bare kai" wasu irin saliva's ya haɗiye yace "Hjy bari naje na dawo" tace "cewa nayi kazo ina son magana da kai ban ce ka ba ni uzuri ba" babu yadda zai yi dole ya fara takawa ya nufi gurin da suke zaune ya zauna yana kallon matar mahaifin nasa ta gefen ido,yace "ina yini?" Kamar wanda aka yiwa dole ta amsa tace "lafiya.." Daga haka bai sake cewa komai ba ya kalli Hjy yace "ga ni Hjy" tace "ehhh! Na ganka mana dama.. Tou wai kai Mujaheed sai yaushe za ka fitar da mata kayi aure ne?" Wani faɗuwa gabansa yayi ya ɗago da sauri yace "aure kuma Hjy?" Tace "ehh aure mana?" Wani gumi yaji yana tsatstsafo masa,tace "kai nake sauraro,ko baka da niyyar yi ne?" A rikice yace "zzz.. Zan yi Hjy" tace "sai yaushe?" Yace "soon in sha Allah" tace "atooohh! Gara dai ka yima kanka ƙiyamul'layli ka fitar da mata kafin ka sake kaɗawa ka bar ƙasar,mu da ganinka kuma sai bayan shekaru,gara ayi auren ka ɗauki matar sai kaje can ku ƙarata" kallonta kawai yake tunda ta fara maganar,sanda tace "toh! Kana da matar auren ma kuwa?" Yayi shiru ransa duk a ɓace yace "za'a samo" tace "tou Allah ya taimaka" yace "ameen" ya tashi ya nufi ƙofa,can ƙasan throat ɗinsa yace "sai an jima" yana fita Gimbiya Habiba tayi saurin kallon Hjy tace "Allah yasa ban miki shishshigi ba Hjy" Hjy dake kallonta tace "akan me?" Tace "lamarin Mujaheed ni dai ina hasashen kamar akwai abunda yake ɓoye mana wanda bamu sani ba" Hjy tace "kamar wanne?" Ajiyar numfashi Gimbiya Habiba tayi tana gyara zama tace "Hjy baki kula da shi ba duk lokacin da za'ayi masa maganar aure shi kenan kamar an ambaci maƙiyinsa,ni dai ina ganin idan ba aljana ta auresa ba tou gaskiya yana tattare da wani matsala wanda muka kasa gane kansa" shiru Hjy tayi tana nazarin maganar ta,can tace "tabbas Habiba wannan maganar taki tana kan hanya,nima na jima ina tunanin haka,saboda duk lokacin da akayi amsa maganar aure da zaran ya sa ƙafarsa ya bar ƙasar nan sai ya ɗauki shekaru bai sake waiwayar mu ba.. Kou me haka yake nufi Allahu a'alam" Gimbiya Habiba ta sake yin ƙasa da kai tace "ai ni dama dan kada na faɗa ne ace ina jifansa da mugun nufi shisa nayi shiru ban taɓa faɗa ba sai yanzu,shima karambani kawai nayi saboda zaman tare bai ce haka ba.. Idan ma wacce zai aura ɗin ne baida ita ai bazai gagara ba,sai a nemo masa" sosai Hjy ta aminta da maganar Gimbiya Habiba har tana mata godiya,sanda ta tashi tafiya ta yiwa Hjy sallama kafin ta fita ɓangarenHjy take cewa "dole yau nayi magana da Abduljalal a san yanda za'ayi a nemi mafita,kafin al'amarin ya sake kwaɓewa.." A kan idanun Jay Gimbiya Habiba ta fito part ɗin Hjy tana sakin murmushi,tana ganinsa ta ɗaure fuska tana jifansa da kallo cike da tsana,shima fuskarsa a ɗaure ya ɗauke kai yayi wucewarsa...


       #Afwaan Habibties jiya network ya hana ni yin update

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

KALLO YA KOMA SAMA!Where stories live. Discover now