Fleeing

126 9 2
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2021.



*♡KALLO YA KOMA SAMA¸.•💥*
_((SHAHO YA ƊAUKO GIWA))_

'''#ƊAN MACE AGAIN'''



*HAWWA MUH'D USMAN.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

05

#Fleeing

Cikin wani irin ɓacin rai Mami dake fitowa part ɗin Jay ta nufo parlon da take sa rai da samun Mai martaba,tun daga nesa take kallonsa tayi masa sallama,sanda ta ƙaraso ta zauna trying hard to control her temper tace "yallaɓai ina son magana da kai,ina fatan za ka yiwa maganata kyakkyawan fahimta.." Ko tari Mai martaba bai ba bare tasa rai zai kulata,ta haɗiye abunda take ji ya tsaya mata a wuya tace "ba na tunanin abunda kake ƙoƙarin yi zai kawo masalaha tsakaninka da ɗanka.. Idan har ace aure kake so Mujaheed yayi,think ba ta wannan hanyar za kasa ya amince ba,yana da kyau ka bashi dama da lokaci ya kawo maka wacce yake so,idan bai da ita ko ka bashi lokaci bai kawo ba,a nan kana da damar zaɓa masa ko wace ce ka aura masa.. Maganar gaskiya aure tsakanin Mujaheed da yarinyar baiba,saboda ya faɗa maka ba ya sonta,shin ba ka tunanin hakan zai iya janyo wani matsalar,na san family ne amma idan ya cutar musu da yarinya me kake tunani zai iya faruwa? Kai kanka ba tsira za kayi ba,dole sai an zageka ace ka san haka zai faru,and ni ban ma taɓa ji ko ganin inda aka yiwa namiji auren dole ba.. Dan Allah ba don ni ba,ka taimaka ka bar maganar auren nan,tunda ya fito ya nuna maka ba ya sonta,ka bashi dama ya kawo wacce yake so,dan Allah.." Wani murmushi Mai martaba yayi ba tare da ya kalleta ba yace "kin gama?" Mami tayi shiru bata ce komai ba sai dai kallo ɗaya za kayi mata ka gano tsantsar damuwar da take ciki,mai martaba yace "duk damuwar da Mujaheed zai shiga bazai dame ni ba,yayi ya gama aure ne tunda na furta babu fashi,sai dai idan an ɗaura auren ya mutu,dan na rasa shi ba wani abu bane,Ubangiji ya azurtani da wasu ƴaƴan,so ko da suke mata ina son su haka nan.." Mamaki ne ya hana Mami cewa komai,sanda ya gama tace "ranka ya daɗe wannan al'amarin fa ba ƙarami bane,ya kamata ka duba irin matsalar da zai iya faruwa.." Mai martaba yace "Mariya.. Na faɗa miki ko me zai faru baza'a fasa ba,so gara miki ki yi shiru da maganar nan,ba na son jinsa,saboda yana ɓata min rai,ni ne mahaifin Mujaheed kou? Tou ina so ki zuba min ido kawai" Mami ta gyaɗa kai tace "okay! Amma yana da kyau ka tuna cewa ba kai kaɗai kake da iko da Mujaheed ba,nima ina da iko da hakki akansa.. Idan har kai a matsayin ka na mahaifinsa baka damu da farin cikinsa ba,ni na damu,idan sonsa ne ba ka yi,ni ina son sa,idan kana yi masa haka ne don ka ƙuntata masa,tabbas ni zan tsaya bayansa,zan kasance tare da shi cikin tsanani da daɗi.. Kana matsayin shugaba,wanda yake kulawa da talakawansa,amma matsalar gidanka ma ka kasa sanin yanda za kayi da ita? Da wannan abun da kake ya fi maka ma ace sauka kayi daga mulkin,dan bai dace da mutum irinka ba.." Lafiyayyen marin da ya tsika mata,yasa Mamin Jay yin shiru ta dafe cheek ɗinta na wasu daƙiƙu,sanda ta ɗago tana kallon Mai martaba da ya kasa kallonta saboda kunyar abunda ya aikata,ta ɗago palm ɗin ta tana kallo kamar da shi aka mareta tace "yau ni ce ka fitar da hannunka ka mara,saboda na faɗa maka gaskiya? Tsayin shekaru 35 muke tare da kai,baka doke ni tun da yarinta ta ba,sai yau da girma na? Kawai saboda na faɗa maka gaskiya akan son zuciyarka? Shi ne har ya kai ka mare ni?" Da sauri Mai martaba ya juyo zai riƙeta,tayi maza tayi baya tana karkaɗa masa hannu,wasu hawaye masu zafi da ƙuna suna saukowa cheecks ɗinta ta kai palm ɗinta ta goge tana jinjina kai tace "na gode kwarai.. Yau ka tabbatar min da wane ne kai,ka tabbatar min nan gaba kaɗan har bulala za ka iya sawa ka doke ni,amma ina so ka sani ba a bola ka ɗauko ni ba,nima ina da gata na,kamar yanda kake taƙamar kai ɗan asali ne,nima haka nake ji da gani.. Sai dai ina son sake tuna maka,idan zama da nine ba ka so,ko ka gaji da ganina akusa da kai,yana da kyau ka fito ka sanar min,tun wuri na kama hanyata,na tabbatar iyayena/yayyena da family na basu gaji da ni ba.." Wani kallo Mai martaba yake mata cike da nadama yace "Mariya.. Kiyi haƙuri don Allah,raina ne ya ɓaci amma ba da niyya na mareki ba" cikin rauni da karyewar zuciya tace "saboda ranka ya ɓaci sai ka mare ni? Idan ba gajiya kayi da ni ba,me yasa za ka doke ni,kawai saboda na nuna maka kuskuren da kake ƙoƙarin yi? Shi kenan,babu komai na gode.. Amma wallahi² ka ji na rantse maka,ɗa na bazai auri mata irin wannan ba,zan yi duk yanda zanyi na ganin na dakatar da auren.." Daga haka ta juya tayi tafiyarta ta barshi tsaye ya rasa ma me zai sake cewa,sanda ta shiga bedroom ɗinta kuka sosai tayi mai ciwo,ko yaya ta tuna wai ita Mai martaba ya mara sai ta sake fashewa da kukan baƙin ciki,ganin abun take kamar a shirin film,sanda tayi mai isarta kafin tayi shiru ta kwanta lamo tana jan istigfar. Wani irin runtse idanunsa Jay da komai ya faru a kan idanunsa yayi,marin da Mai martaba ya yiwa Maminsa sanda ya dafe cheeck ɗinsa a tunaninsa shi aka mara ba ita ba,duk sa'insar da suka yi babu wanda bai ji ba,Mami tana barin gurin ya juya shima da sassarfa ya nufi part ɗinsa,sanda ya shiga ya kulle ƙofar ya sulale ƙasan gurin,kamar mace haka hawaye suka dunga sauka fuskarsa,tun da ya taso zai iya cewa bai taɓa ganin sanda iyayensa suka samu saɓani ba,amma yau a dalikinsa har ta kai ya janyo an mari mahaifiyarsa,idan haka ne shi mene ne amfaninsa? Mene ne amfanin duk wannan damuwar da faɗan da ake yi akansa? Ya yiwa iyayensa adalci kenan? Wani irin miƙewa yayi da sauri ya buɗe ƙofar ya fita,sanda yake tsallake stairs ɗin har faɗuwa ya kusa yi,bai tsaya ba ya fito part ɗinsa,direct ɗakin Maminsa ya wuce,ya buɗe ƙofar da sauri ya shiga,har lokacin tana kwance kan gadonta idanuwanta a lumshe hawaye suna sauka fuskarta,da ƙarfi Jay ya kwanta jikinta ya fashe da kuka yana faɗin "I'm so sorry Mami,forgive me Mamina,duk laifina ne da na yarda haka bazai faru ba,pardon me please Mami,zan je na faɗawa Abba na yarda na amince zan aureta.." Saurin buɗe idanuwanta tayi tana kallonsa da wani dasashen murya tsabar kukan da tayi tace "Mujaheed! Me yake faruwa? Why are u crying?" Yace "Mami it's all my fault,da na yarda na amsa tun farko there's no reason da Mai martaba zai ɗaga hannunsa ya sauke a fuskarki.. Idan akwai wanda ya kamata ya doka,bai wuce ni da nayi masa musu ba,me yasa sai ke? Me yasa zai doke ki? Ai baki masa laifin komai ba.." Tunda ya fara magana take binsa da wani kallon tsoro,tace "Mujaheed! Ya akayi kasan ya doke ni?" Da ƙarfi yace "Mami i just saw and heard everything.." A tsorace Mami tace "ka ji komai?" Yace "ehhh Mami na san komai" saurin share hawayenta tayi ta ɗagoshi tana goge masa fuskarsa tace "ya isa haka Mujaheed,stop crying son.. Tashi ka sanar min da gaske kake ka amince?" Ya gyaɗa kai yace "Mami na yarda,ya aura min whomever he wanted to zan karɓa" tunda ya fara magana Mami take kallonsa tace "me yasa ka amince yanzu?" Yace "Mami ba na son ganin ku a irin yanayin nan,bazan so a dalilina ace haka ya faru ba.. Sam ba na jin daɗi ace akaina iyayena suna samun saɓani.." Murmushi Mami tayi me ciwo tana kallon Jay tace "kana so kace min ka yarda za ka auri Atika?" Ya gyaɗa kai a hankali,Mami tana masa wani kallo tace "bazai yiwu ba,idan ka amince za ka aureta,ni ban amince ba,saboda sam Atika ba matar ƙwarai bace,ɗa na bai dace da mace irinta ba,haka nan jikokina za su tashi marasa ɗa'a da tarbiyya,sanadiyyar rashin uwa ta gari.. Bazan taɓa amincewa ka aureta ba Mujaheed,sai dai duk abunda za'a yi ayi.." Yace "but Mami" kai ta kaɗa masa tace "ka barni Mujaheed,i'll handle it.." Jikinsa a sanyaye yace "tou Mami.." Tace "ka fara shirin komawa India.." Yace "in sha Allah Mami.." Daga haka suka yi shiru kowanne zuciyarsa cike da tunani. Tunda Mami ta bar Mai martaba tsaye ya kasa motsi,mamakin yanda ta iya sa'insa da shi duk ya cikasa,wai shi ne yau Mariya take yiwa rantsuwa akan baza ta bari Mujaheed ya auri ƴar ɗan uwansa ba? Tou shi kuwa zai ga yanda za'ayi a fasa auren,tsakanin shi da ita zai ga mai cikakken iko da Mujaheed,ko da ya fita part ɗin gaba ɗaya ya samu Sarkin dogarai ya sanar masa yana so su bazu cikin gidan su tabbatar sun sakawa Mujaheed ido,da duk wani motsinsa,ko fita akaga zai yi ayi maza a sanar masa but kada su bari ya gane. Sanda labarin auren da shirin Mai martaba yake akan Jay yazo kunnen Mami tayi wani dariya tace "uhmn! Za mu gani.." Around 1am lokacin sahu ya ɗauke,Mami ta fito bedroom ɗinta ta wuce ta nufi part ɗin Jay,sanda tayi knocking Jay dake zaune ya kasa bacci,yayi saurin tashi ya nufo ƙofar yace "who's there?" Mami yace "open the door" da sauri Jay ya buɗe yana kallon Mami yace "tum? (Ke ce?)" A dake Mami tace "take ur belongings and follow me" a tsorace yana kallon Mami yace "Mami where?" A fusace tace "ka ɗauko kayanka nace,tafiya za kayi ka bar musu gidan,idan sun tashi sun ga ba ka nan sa aurawa wani" da sauri ya gyaɗa kai yace "tou Mami" ya juya da sauri ya ɗauko luggage ɗinsa dake ajiye,sanda ya kwashe wayoyinsa da passport ɗinsa ya fito da sauri,basu tsaya kulle part ɗin ba,Mami ta kama hannunsa suka fito,cikin sauri suke tafiya sanda ta kaishi har parking spot,Jay ya kalli mahaifiyar tasa hawaye suna sauka fuskarsa ya rungumeta da sauri,yace "Mami i don't want to go,please let's go together" tace "no Jay,ka tafi idan na bika muka tafi za'a fahimci mun haɗa baki ne,amma idan ina nan babu wanda zai yi zargin da sa hannuna ka bar gidan,kaje Allah ya tsare min kai,idan ka sauka ka kirani,duk inda kake zan samu lokaci nazo.. I love u son" yana kuka Mami tana yi,da sauri ta raba jikinsu ta turasa mota tace "maza kaje,kada ka tsaya Mujaheed,bazan so ganinka cikin damuwa ba,ka tafi kayi nisa da garin" da sauri ya gyaɗa mata kai yace "i love u too Mami" daga haka ya shiga mota ya tayar,Mami tana tsaye tana kallonsa ya figi motar da mugun speed yana waving mata,itama tana yi hawaye suna sauka fuskarta,sanda taga ya fice ba ta ko ganin ƙurar motarsa then ta juya da sauri ta nufi part ɗinta. A bakin babban ƙofar fita gidan sanda Jay ya tsaya yana kallon yanda yake a rufe da sauri ya sauka motar bai rufe ba yaje gurin ya zare manyan sakata da aka rufe ƙofar,sanda yake sassarfa ya dawo ya shiga mota ya nufi ƙofar gadan²,yana daf da fita Mudi dake cikin bayin da suke tsaron ƙofar ya fito banɗaki jin ƙarar buɗe ƙofa da fitar mota,da ƙarfi ya rafka salati yana kiran sauran bayi ƴan uwansa,here wasu ciki suka shiga motoci suka bi bayan Jay,kan kace me labari har ya isa cikin gida,ran Mai martaba ɓace cikin daren haka ya fito ya nufi part ɗin Jay,yana shiga ya tarar da part ɗin a buɗe,sanda yasa aka gama bincike kaf gidan babu Jay,Mai martaba ya zauna parlour yayi shiru,ransa ya yi mugun ɓaci da al'amarin ya tashi ya nufi bedroom ɗin Mami. Mami kuwa tun fitar Jay daga gidan sanda ta dawo tana shiga ɗakin nata ta wuce bathroom tayi alwala ta tada sallah,lokacin da Mai martaba yayi knocking jin shiru ba'a yi magana ba ya tura ƙofar,sanda ya shiga yaga ɗakin da duhu,sai lampshades kaɗai ya ƙarasa ya kunna haske,here yaga Mami tana sallah,tunda tayi sujadda take kwararo addu'o'i,ya nemi guri har ta idar,bata damu da irin kallon da yake mata ba ta ɗauke kanta tana lazimi,Mai martaba ya zuba mata idanu har sanda ta idar ta tashi ta naɗe abun sallah ta kashe hasken then ta haura gadonta tayi kwanciyarta,gyaɗa kai kawai yayi yace "Mariya kin san magana nazo muyi dake,amma kin yi banza da ni baza ki iya tambayata me ya kawo ni ba a irin lokacin nan?" Mami bata tashi ba tace "kana iya faɗar abunda ke tafe da kai ai" Mai martaba yayi shiru yana kallonta ta cikin shade da ya haskata trying hard to control his temper yace "kin san inda Mujaheed ya tafi?" Tace "kamar ya kenan,wane Mujaheed?" Yace "wane Mujaheed kike zaton zan tambayeki?" Tayi masa shiru ta ƙi cewa komai,yace "ina tambayarki ina Mujaheed yake?" Cikin jin haushi tace "wai Mujaheed ɗin nan nono yake sha ne da za ka min tambayar yana ina? Ka je part ɗinsa baka sameshi ba,da za ka shigo min tsakiyar dare ka tasa min tambayar yana ina? Goyasa zanyi ko ciki zan mayar da shi?" Tashi kawai Mai martaba yayi ya fita saboda ya gama karantar yanayin ta,it was there yayi waya yace a sanarwa wanda suka bi Jay su dawo su rabu da shi. A haka sanda gari ya waye cikin gidan babu lafiya,sai ƴan gulmace² ake da ƙananan maganganu akan abunda ya faru daren, around 10am kaf family sun haɗu suna zaune suna jiran fitowar Mai martaba saboda meeting ɗin gaggawar da ya kira,manya da yara kaf sun tattara parlonsa,sanda ya fito Mami ce kawai babu,Hjy Babba ta kalli cikar gurin tana jinjina al'amarin da ya faru tace "tou ita wancan hamshaƙiyar ba ta zuwa ne,kowa an aika kiransa ya zo cikin daɗin rai,shi ne ita tayi zamanta saboda ta mayar da mu gantalallu" Mai martaba da fitowarsa kenan yace "ku barta dama ban sa a kirata ba" Hjy Babba tace "iiihhhh! Saboda me za'a barta? Ta fi kowa ne? " Mai martaba yayi shiru bai ce komai ba,ya zauna wani kujera na alfarma haɗe da yin sallama duka suka amsa,sanda ya ɗanyi shiru yana kallon occupants ɗin gurin then ya fara jawabinsa...

#Afwaan habinties ban samu charge ba sai yanzu,so ban samu na yi typing In-laws ba,kuyi min haƙuri please.

*This book is not for free,it's #300 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ku iya tuntuɓar wannan number +22770766074.*

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

KALLO YA KOMA SAMA!Where stories live. Discover now