Zuciyanta ta fasa yakeyi cikin bacin rai ta kauda kanta dasauri bhaila ta gaida sarki amsa wa yayi dasauri tafita harta wuce yana kallonta.
Cizan bakinsa yayi kafin yajuya kan gimbiya maha. Kauda kanta tayi. Tunda yaga ba kowa anbarsu. Zama yayi yariko hannunta binta yakeyi da kallon yadda tayi ado ga sarka ga gashinta yazubo har tsakiyan bayanta.
Gimbiya maha fushi kikeyi dani . Kallon mamaki take masa dama haka yake duk lokacin dayake neman abu agunta zai sauke murya kasa. Ta dade bata gansa ba rungumesa tayi ta lumshe ido.
Kafin sarki mulk ya saketa. kallonsa takeyi saikuma ta tuna da abunda yafaru jira kawai takeyi sarki yafita taga bhaila tashigo tamata abunda batayi sammaniba.
Bhaila na fita zuciyanta yana tsinkewa wnai irin kallone sarki ke mata.
Girgiza kai tayi dadi taji ko ba komai moolah bamai ganeta.Dukawa tayi ta gaidasu . sarauniya neemah da yayanta mata ta dan daga kanta
Kallonta sukeyi kafin suka dauke abunda sukeci suka zubda shi kasa. . Zaki iya dauka ki kwashe kuje kuci
Ahaka suke fashe da dariya. Shiru bhaila tayi zuciyanta na radedi ta kwashe ahankali.gimbiya maha nifa wannna baiwar da nake kallo duk da ita baiwa ce surar ta ta dabance amman da alama bayin wani gari ne ko?
daga giranta gimbiya naeemah tayi ko wani sura gareta kowace masarauta take ahaka dai zata kare da bautanci kaman yadda tayi yanzu.
fashewa da dariya sukayi dukkansu.
cikin radadin zuciya bhailah ke tafiya tana tuna abunda yafaru yaushe ne zasu bar wannna masarautar gashi abu sai kara gaba yakeyi lumshe ido tayi ta hango moolah zaune
Shiru moolah tayi tana zaune tana kallon rayuwansu kallom duk yadda bayi suka zauna suke rayiwansu haka suma zasuyi rayuwa haka suma zasu zama.............haka zasu ta bauta ana wulakantasu. fashewa da kuka tayi kafin bhaila tazo dawuri ta rungumeta tana sharemata hawaye.
kiyi shiru bhaila kidena kuka kinji girgiza mata kai moolah tayinamiji ba ya kuka.
inji jakadiya sarki ta fada tana kallon moolah dasauri bhailah ta gyara ma moolah tufafin dake jikinta .meyasa kake kuka kasan da cewa kowanni namiji anan mai shekarunka bayi ne ko gasinan anan harsun saba kaima ahankali zaka saba.
tafada tana karema bhailah kallon munafurci. shiru bhailah tayi
kima dan naki magana kar garin ragaucin nasa yasaka dan sarki jalal yasaka a zanesa.
ahaka tafita tabar gurin.
ajiyan zuciya tayi ahaka shafiq yakawo musu abinci suka ci suka wanke hannunsu.
_____
lumshe idanuwansa yayi yana kwance tare da kulle idanuwansa. ba zai iya cewa tunda yake arayiwansa yana yawan tuna abu fiye da wannnan yarinya dake kokolwansa ba. anya mutum ce kuwa kodashike yakuma riko hannunta ba yadda za ayi ace ba daidai ya kalleta ba.
idanuwanta kawai ke yawo idan yakulle idonsa.ahankali moolah tashigo fannin dan sarki jalal. ahankali take lekawa kafin nan ta tsaka dayan kafanta tana tafiya tanan ganin baya gurin inda yake shan tea dinshi tayi gaba tana ajiyan zuciya zata juya tatafi taji murya abayanta.

YOU ARE READING
BAIWA CE
RomanceAll right reserved © 2019 She was a slave without a choice Life without a freedom and Love without a destiny Meet moolah facing a life of a slavery at a young age of her life update once a week. ____ ©