page 15

183 5 0
                                    

🅰 *S🅰N🅰DIN GROUP*🙊🙊

*Written by*
 
💅💅 *SADNAF*💞

  *PURE MOMENT OF  LIFE WRITERS*

    _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

*A short story based on true life story*

*Page:-* 15

Manal magana tafara k'ok'arin yi taji kira na shigowa dubawa tayi taga *Daddyn Hanif ke kira* da sauri tace mishi tana zuwa mijinta na kiranta zata kirashi ta katse wayar ta d'aga wayar,Yusuf da ransa a mutuk'ar b'ace yake Dan ya mata miss call wajen goma sha bata 'daga ba,sai gashi ya kirata yaji call waiting,sallama tayi mishi amadadin ya amsa yace

"meyesa nake kiranki baki d'auka ba?

Manal cewa tayi
" Gashi na d'auka  yaushe ka kirani ban d'aga ba",dan ita bata  ma San ya kirata ba, cikin tsananin b'acin rai yace "ki duba wayarki kiga Misscall nawa na miki" ya kashe wayar,da sauri ta duba misscall taga ashe tun 6:30 ya ke kiranta,ya mata miss call har goma sha d'aya,tunanin karyar da Zata mishi ta fara yi,kiransa ya sake shigowa wayar,d'agawa tayi yace "guda nawa kika gani"?

" Daddyn Hanif wlh barci nake lokacin da ka kirani banji ba wlh"

"Barci barci fa kikace Manal" k'irjinta ne yafara dukan uku uku Dan indai ya kirata da Manal to ransa yakai kololuwar wurin b'aci, " yaushe kika fara komawa barci idan kin idar da sallar asuba"

Manal rasa amsar da zata bashi tayi Dan bata komawa barci in tayi sallar asuba,tun a gida,shi yasa ma in yayi tafiya yake kiranta awuraren lokacin kafin yatafi aiki,haka zasu ringa waya daga 6:30 har zuwa lokacin da yara zasu tafi makaranta ta had'asu awaya su gaisa daga nan suyi sallama,Dan babu laifi Yusuf is a caring Husband indai yana da sarari awajen aiki sun tayin waya da ita kenan,Kame kame ta fara yi tana k'ok'arin lalubo amsar da zata bashi Dan bata iya karya ba,katseta yayi yafara magana rai a b'ace

" Manal Wai mai yake damunki ne? kwana biyu bana gane miki Sam,kin chanja ba kamar yanda kike ba,yanzu yaushe rabon Dana ga kiranki a wayata  da sunan ke kika kirani?yaushe rabon Dana ga misscall d'inki awayata? Ina kiraki awaya Allah Allah kawai kike in ajiye wayar,a watsapp ma ina miki magana kafin ki kulani kiban amsa sai ansamu awa d'aya ko biyu alhalin kina online Manal what have come over you,?ko laifi nayi miki kike min haka,banso nayi miki magana ba amma abun na damuna manal,caring d'in dakike nuna min duk kin daina,yanzu in ba ni na kiraki ba bazaki tab'a kirana ba,in ni nakiraki sai kin kawo min excuse din dazai sa muyi sallama,texes d'in da kike turomin suke deb'e min kewa in ina wajen aiki duk kin daina,what change you like this Manal in laifi nayi miki ki fad'amin na baki hakuri,yanzu duba kigani,bakiji muryata ba har 11:30 baki kirani ba,kuma ni na kiraki baki d'aga ba,hasali kina can kina waya ba ki damu ba,Manal ina nan ne zuciyata tana wajenki da yarana,wlh duk abinda nake kuna raina,ba asan raina kuka yi nesa dani ba,badan halak d'ina nake nema ba,babu abinda zai nesanta ni daku, Dan Allah idan  laifi nayi miki, ko wani ke zugaki kiyi hakuri ki dawo yanda kike, Dan canjawar da kikayi ba gani bane kawai har da yarana,sani ne baki yi ba Hanif ya gayamin Last week dazan kaisu gidan Hajiya,yanzu kamar Hanif ma yasan kin canja musu,yaringa cemin in baki hakuri in laifi suka miki,kin daina musu home work Hindatu ke musu,kin daina koya musu karatun Qurani Haba Manal this is not you"

Tunda yafara magana hawaye ya hau zubo mata Dan tabbas ta canja ba haka take ba,Yusuf Nada hakuri,to mai yasa takewa Mijinta uban yayanta haka,mai yasa ta zabi group akan farincikin Mijinta da yayanta,yanzu jiya Manal daddare kafin barci ya d'auketa sai da ta ce mata "Momy yanzu kin daina sona,bakya min wanka bakya min kwalliya,bakya koya min Home work d'ina  Daddy yafi sona idan ya dawo,yana min wanka ya ce in kawo littafina ya koya min home work d'ina Momy mai nayi miki kika daina sona " a lokacin tsaki tayi tace mata ta tafi ta bata guri bata San surutu,ta cigaba da kallon videon dake d'aga mata hankali...........................



*HAUSA NOVELS* 📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

A SANADIN GROUPWhere stories live. Discover now