8

265 23 6
                                    

#NoorEemaan

🍇🍇ABRAHAM🍓🍓






*WATTPAD*
@NoorEemaan

Banyi editing ba🤒

Chapter 15-16

Asalin Abraham dan kabilar igbo ne na jihar imo state, haka zalika iyayen sa, mahaifin sa (Patrick Samuel) shahararren dan kasuwa ne, wanda duniya ta San da shi, inda ya hadu da mahaifiyar Abraham (Victoria) a wani bussiness trip daya je Canada, inda ita kuma Victoria tana hada master's dinta ne a lokaci, inda ita ma yar mai kudi ce domin mahaifinta babban lawyer ne.

Basu dauki lokaci me tsayi ba suka fahimci Juna, Bayan ta gama hada masters dinta ta gabatar da Patrick ga iyayen ta, inda ba a samu wata matsala ba iyayen ta suka amince kasancewar suna kaunar farincikin  diyar su, sannan kuma Patrick ya kwanta musu a rai kasancewar ya hada dukkanin quality's din da suke so ga namijin da zai auri 'yar ta su, traditional wedding din su aka fara yi, inda aka gudanar da dukkanin Wata al'adar su a yayin biki.

Bayan Wata daya aka daura musu aure ma'ana dai suka yi Church wedding, farinciki da kwanciyar hankali hadi da zallan kauna ne yake wanzuwa a gidan Patrick...

Auren su na da wata bakwai Victoria ta samu shigar ciki, inda ba karamin farinciki Patrick yayi ba, son duniya suka d'aurawa cikin, in da suke a K'age Dan ya fito duniya suyi tozali dashi....

Bayan wasu Watanin Victoria ta haifi santalelle kuma lafiyayyen dan ta, sosai murna ya karu a gidan Patrick, in da suka dora son duniya ga yaron, ranar suna yaro yaci suna ABRAHAM kamar yadda Patrick yaci burin saka wa dansa matuk'ar yayi aure ya haihu...

*************************

*10 Years Later*

A kwana a tashi babu wuya wurin Allah, domin shekarun Abraham yanzu goma cif,  ya gama primary school a wani tsad'add'en makarantar private dake imo, inda baya taba zuwa na biyu a school dinsu saboda tsananin kwazon sa...

***********

Bayan an gama bikin birthday dinsa da kwanaki  iyayen sa suka yi masa rakiya zuwa England inda zai cigaba da karatun sa har jami'a kamar yadda Patrick yayi masa sha'awar yin karatu a waje, aka kuma yi sa'a ra'ayin su yazo daya da Abraham, duk da Victoria bata son danta yayi nesa da ita amma babu yanda ta iya domin tafi kaunar farincikin sa fiye da nata.

Sai da suka tabbatar komai yayi daidai kana suka dawo Cike da kewar tilon dansu, a rana sai su yi video call dashi sama da goma, as time goes on suka fara sabawa da rashin sa a kusa, inda duk bayan Wata hudu suke zuwa duba Abraham....

*Bayan shekaru biyu*

Patrick na hanyar dawowa gida daga ma'aikatansa ya ga Kiran Victoria ya shigo wayar sa, inda take sanar dashi kanta na ciwo sosai bata samu yi masa girki ba, kuma ta San baya son abincin yan aiki, Sannu yayi mata cikin kulawa, gama wayar su ke da wuya ya hango wani gidan Abinci, umarnin ya bawa driver kan su karasa gidan abincin, sauka yayi ya nufi cikin wajen  da kan sa inda ya samu Wata budurwa Wacce take bangaren serving din mutane, kallo daya mutum zai mata ya karanci cewa ta Bude ido da yawa, ga iya kissa, Gloria Kenan...

Fried rice with chicken da hadin salad partrick yace ta hada masa takeaway ba tare da ya lura da karairayen da take masa ba, ita kuwa Gloria lokaci daya taji ya tafi da ita, bata bari ya tafi ba sai da tayi iya yinta ta samu number'n wayar sa.

12:05am

Kwance suke suna bacci su cikin kwanciyar hankali Kiran Gloria ya shigo wayar Patrick, wanda hakan yasa ya farka a zabure domin wayar na saitin kunnen sa, saurin danna answer yayi, zai yi magana Kenan yaji Gloria tace "Am so sorry for calling you at this time, is just that I couldn't help i......" kit ya kashe wayar gabadaya, domin ya gane matashiyar gidan Abinci nan ce, banda bata da tunanin a wanna daren zata kira shi, ko da bashi da aure bare yana da, ko meya shiga kansa har ya dauki number ya bata oho ya fada a ransa yana Jan tsaki, mai da kallon sa ga Victoria yayi yaga bacci take, ajiyar zuciya ya sauke ya koma ya kwanta.....

ABRAHAM Where stories live. Discover now