#NoorEemaan
🍇🍇ABRAHAM🍓🍓
*WATTPAD*
@NoorEemaan*I dedicated this page to my anty, Anty hawwa(TM@shoprite ) a very nice woman with a heart of gold, duk da girman matsayin ta bata da pride*💞
Chapter 17-18
Wa'alaikumu Salam Inna ta amsa tana leken mai shigowar kana tace "a'a wa nake gani kamar bintu?"
"Nice Inna wuro" matar ta fada da murmurshi saman fuskar ta.
Lale maraba, sannu da zuwa karaso ki zauna, idanki Kenan?" Inna ta fada tana k'akk'abe saman tabarman wa bintu domin ta zauna...
Zama bintu tayi kana suka gaisa da Inna cikin yaran fillanci, Jim suka yi babu wanda yayi magana tsawon mintuna uku kana bintu ta muskuta tace "ya muka ji da hakurin rashin baffa? Ashe baffa ya Riga mu gidan gaskiya, zuwa na gida jiya na samu labari, Kin San wannan aikin namu Bamu ba lokaci gashi ba a kusa ba, Allah ya masa rahama"
Murmurshi mai ciwo Innah tayi kana ta amsa da ameen tana kokarin mayar da kwallar daya cika idanun ta, tsaf bintu ta lura da ita, amma bata ce komai ba, domin wani kukan ma rahama ne, gashi kuma ta ga alamun sauyin Rayuwa a tare dasu Inna, girgiza kai tayi cikin tausayin su, yayinda hirar da suka yi da matar da ta tace ta nema mata yar budurwa mai tsafta domin gyara dakunan su da yin girki, ko da bata iya girki ba za a kawo k'wararriya domin koya mata, burin matar dai yarinya mai tsananin tsafta take so.
Hakan nan Indon ta fado mata a rai, kallon Innah tayi tace " kiyi hakuri Inna wuro idan na yi miki shishigi naga kamar kuna cikin wani hali na rashin babu, gashi kuma can kaduna kusa da gidan da nake aiki ana neman 'yar budurwa irin su Indo, duk da dai na kwana biyu ban gan ta ba, amma nasan ta kara girma. Da' yar gidan garko zan kai, amma na fasa, domin ban ma sanar musu ba, ya kika ce innah wuro? Kinga kudin zai taimaka muku kwarai wurin sauyin Rayuwar ku fiye Dana baya" bintu ta karasa tana kallon innah, tare da fatan samun amincewar ta.
Bata rai Inna tayi kana ta girgiza kai tace "a'a bintu bazan iya ba, bazan iya tura 'yata kwalli daya aikatau ba, me mutanen gari da yan'uwan mahaifin ta zasu ce? Baz....."
"innah!"
Indo dake tsaye tun dazu a gefen su ba tare da sun lura bata ta fada.A tare suka mayar da duban su daga inda amon muryan indo ya fito, karasawa Indo tayi gaban Inna ta tsugunna, riko hannun ta tayi, hawayen zallan tausayin kansu ya zubo mata tace "innah ta! ki amince dan Allah, ki amince, kinji? zan iya yin komai matuk'ar halal ne domin mu samu sauyin Rayuwa, meye amfani na idan ban taimaka miki ba Inna? Alhalin zan iya yin hakan? A Rayuwar nan idan mutum zai yi abu kar ya duba abinda mutane zasu ce? Sati daya kacal ya ishe su yin duk wani surutun su da gulma su hakura, da Muke shan wahalar mu waya tallafa mana?, ki bani umarnin yin aikin nan Innah, ina ji a jikina cewa akwai alkhairi a tafiya ta aikatau dinan, dan Allah Innah" ta karasa cikin Sanyi murya mai cakude da Kuka wanda ya sanya innah yin laushi"
"tabbas Inna wuro abinda Indo ta fada gaskiya ne, kuma sanin kanki ki ne Inna cewa bazan taba bari tarbiyyar indo ya lalace ba, zan dinga shiga ina duba ta, tun fa ina karama Muke a amatsayin makotan juna, kin San halina, banda mutuwar Ashiru mijina da yanzu ina tare daku a kauyen nan, amma gashi yanzu da kudin aikatau din nake kula da yarana da kuma iyayena, dan Allah innah ki amince in sha Allah baza kiyi nadama ba.
Numfashi Innah ta ja, gabadaya jikin ta ya mutu, a sanyaye kana cikin mutuwar jiki tace "na amince Allah yasa hakan shine mafi alkhairi Nagode miki bintu"
"ameen Innah wuro, ai yi wa kaine Karki damu" bintu ta fada cikin farinciki da sakin fuska kamar yadda ya kasance nature dinta ne yawan fara'a.
"gobe zan wuce in sha Allah sai ki hada kayanki mu tafi ko indo"
