🍇🍇ABRAHAM🍓🍓*WATTPAD*
@NoorEemaanChapter 69-70
A sanyayye Abraham da Aysha suka yi wa kan su mazauni a kan kujerar general falo, domin al'ajabin Madam Gloria bai gama sakin su ba, yayinda su twins ke ta wasan su cike da farinciki hadi da yarinta da kananan throw pillow da suke kan had'add'un kujeru.
Abraham ya fito da wayar sa da bai fiye girma ba, amma sai mugun tsada ya latsa wata number ya kara a kunnen sa.
Bayan an daga, ya bada umarnin wa kamfanin masu decorations da hada daki su zo su hada masa dakin yara da dukkani abun bukatar su na wasa.
Ai kuwa mintuna arba'in na cika suka zo da motar company'n su, dakin Madam Gloria ya nuna musu, sannan yace komai na dakin a fitar su zubar, hatta fentin dakin sai daya sa aka Sanja, sannan suka shiga hada wa su twins daki.
Aikin da ya dauke su awa biyar kana suka gama.
Ya rabb! fadin kyau da haduwar dakin bata lokaci ne, tamkar babu halittar daya taba rayuwa cikin dakin saboda yanda komai ya dawo sabo fil gwanin kyau.Bayan Abraham ya sallami mutanen da huge amount of money da suka chaje shi kana suka tafi.
A lokacin da su twins suka shiga dakin, Abraham ya sanar dasu cewa dakin su ne, suka dinga murna, wanda ya sanyayya ran mahaifin su.
********
Abraham da kanshi yaje nearest boutique ya siyo musu kaya masu kyau duk iri ɗaya, hadi dana bacci, sai kayan shafan su dangin su lotion, hair cream, shampoo da perfume duka na yara.
Aysha ce ta jere musu kayan a wardrobe dinsu, yayin da kayan shafar su kuwa ta jera musu kan dressing mirror.
Daga nan ta wuce kitchen domin ɗora musu girki, saboda yamma tayi sosai.Amma hakan bai hana ta tuka musu lafiyayyen tuwo semovita da miyar ogbono daya sha ụgu,
stock fish, kayan ciki, jan nama da kpomo, tun kafin ta gama k'amshin girkin ya cika falon kasa gaba daya...Tana cikin gyaran kitchen kenan bayan ta gama abinci, ba zato bare tsammani taji an zagaye hannu a kugun ta, saurin juyowa tayi ta ga Abraham ne.
Ajiyar zuciya ta sauke domin ta tsorata, sumba ya manna mata a gefen wuyan ta, sannan yace"my Life"
"Uhmmmm!"
Aysha ta amsa domin ta kasa magana sakamakon hannun sa dake yawo a wasu sassa na jikin ta.
"i love You"
ya fada yana sake riƙe ta da kyau a jikin sa, hadi da birkita mata lissafi, wani yarrrrrrrrrr Aysha taji a jikin ta, duk da bata san me take ji ba, but tana karban sakonnin da yake aika mata.
Ganin yanayin sa ya fara sanjawa, ba kuma ya son ya ya katse mata aikin ta, sai kawai ya barta ya fice, ya koma dakin su Ammar domin suyi wasa. Yana so yaran su shaku da shi sosai, hakan kuma bazai faru ba matuƙar baya jan su a jiki.
*9:21pm*
A daidai lokacin Aysha ta fito daga dakin su Ammar da suka riga suka yi bacci, dama addu'a ta shiga ta tofa musu.
Sama ta hau ta shiga dakin ta.
Bayan nan ta tube kayan jikinta ta daura medium towel, ta saka shower cap, sannan ta shige bathroom ta sakar wa kanta shower, fuskar ta dauke da murmushi...
Farkon haduwar su da Abraham har izuwa yau da suke a matsayin mata da miji ne ke yawo a brain din ta. Ikon Allah da girma yake, komai daya faru yazo karshe kamar bai taba faruwa ba, sai dai labari kuma.Bayan ta fito, oil perfume ta shafe jikin ta da shi kana ta saka riga da wando na bacci masu dan kauri, saboda yanayin sanyin da ake a daren yau.
Tana cikin jera pillow daya dan hargitse ta ji shigowar Abraham, bata juyo ba, ta cigaba da abinda take.
