BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

376 144 16
                                    

BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

*Mun gode sosai da addu'ar ku Allah ya bar zumuncin*

Inna Marwa bata yarda zai iya daina zuwa fada ba, sai da aka kawo mata karan shi, kamar tayi ihu a nan ne tasa aka kira shi tayi mishi fada, tana kawo zancen Bingel ya kalle ta, sannan ta ce mata.
"Inna Marwa kyamarta nake ji, wallahi ba zan iya mu'amala da baiwa ba, kazamtar ta nake gani don Allah kar ki takura min"
Shiru tayi tana kallon shi, jinjina kai tayi sannan ta ce ya tafi.
Bata wani Jima sosai ba, ta koma sokkoto. A wannan lokacin ne wasu abubuwan marasa dadi suka fara kunno kai, tsakanin yan majalisar shi, akan na lallai sai dai ya san yadda zai yi da aminatu ko ya sauka akan kujeran da yake, bai yi musu ba, suka ga ya fara kokarin mikewa suka ce sun dakatar da shi, amma zasu kai hari masarautan Gombe.

Ya zata wasa suke mishi sai da takai ta kawo wata ranar laraba ta fito taga ana shirin yaki.
A lokacin labarin ya isa ga Fulani Aminatu, za a yaki masarautan ta domin sarki yaki mu'amala kowacce mace sai ita, ba mamakin anyi mishi asiri ne tunda sun san cewa bata haihuwa. Fitowa tayi ta nufi shashinsa, yana sanye da kayan yaƙi.
"Ina zaka? Wannan ba kome bane idan ka dauki shawara na matsalar zata wuce, na had'a ka da Allah ka amshi Yahanasu. Wallahi bana jin kome akan ta, nayi imani da Allah ba zai tab'a wulakanta ni ba"
A fusace ya juyo tare da wani matse ta.
"Haka kika son nayi mata?" Ya fada da mugun karfi.
"Ya xan yi? Kana zaton zasu kyale koda yaro me shan mama ne a cikin masarautan ne? Ina son ka amma yakin da za ayi da ahalina ba abu ne mai sauki ba, don Allah ka yafawa zuciyar ka ruwan sanyi. Babu abinda zata dauka a jikin ka" ture ta yayi domin ran shi ya gama ɓaci, ya nuna mata ta fita. Gidan galadima ta nufa wannan shine karon farko a rayuwarta ta tab'a fita. Tana shiga cikin gidan yana tsaye da matan shi, ta zube akan gwiwar ta.
"Idan nice bana Haihuwa zan iya hakuri da duk bukatar ku, amma tab'a ahalina shine abinda ba zan iya dauke kai akan shi ba, don Allah ka roke shi ya amshi ya hannu'" babu d'igon kwalla a idanun ta, sai ma wani irin hakuri da juriyar da Allah ya daura mata a ranar.
Shigowa yayi ya kai hannun shi dukkan biyu ya d'ago ta. Sai lokacin ta fashe da kuka, kamar ranta zai fita.
"Don Allah Baffa'm kayi yadda suke bukata wallahi idan ta kama ka kara aure ne na yarda"
Bakin shi ya kai kunnen ta.
"Karki damu na amince na karɓe ta" kuka take kamar ranta zai fita, Abinda ya faru bayan fitar ta. Nufi gidan Chiroma dama abinda yake bukata kenan, ya cusa tsoro a zuciyar Aminatu, yadda zata d'agawa Sarki Bello hankali shi ya amince da bukatar shi. Ya kuma tako yazo har gidan ya nime Alfarmar akan lallai ya amince da Yahanasu.
Lokacin da ya shiga gidan babu kayan sarauta daga shi sai kayan shi. Na zaman rubutu ya shiga cikin gidan, kallon Chiroma yayi, sake bai shiga da fushi ba.
_(Note asalin damuwar da yake cikin labarin da wasu kananan fitintunu wallahi ya faru a daular Gobir, labarin ya faru da gaske akan sha'anin mulkin su, don haka ba wai dan yana gidan sarauta ba, a'a da wannan yanayin aka ragewa daular karfin mulkin ta a nahiyar Afirka baki daya. muje zuwa)_

Cikin sanyin murya ya ce mishi.
"Ban san me natsare maka ba, bayan haka bani da wata manufa da kai, Chiroma nayi Imani da Allah kana barci da zuciyar ka, domin idanun ka basu barci. Ban zo dan na gaya maka zan amshi kwarkwarah ba, naso da naga Aminatu anan sai na yanke kan ka daga jikin ka zai Allah ya kwace ka, tsohon kawai
"
Dariya yayi sannan ya ce mishi.
"Ba zan yi fada da kai ba, amma nasan lokaci na zuba da zan yi fada da kai" bai saurare shi ba, ya bar zauren.
Gidan galadima ya nufa yaji yadda take rokon kar a tab'a ahalinta. Wani irin tsanar Bingel da yaji da shi ya kudiri Aniyar sai ya saka mata wani irin tsoron shi. Dan haka yana mai da Fulani Aminatu sashin Taz ya gayawa Innayoh bukatar shi, bata yi musu ba ta saka aka shirya Bingel aka kaita wurin shi. Dake ran shi ta gama ɓaci gashi dai an janye yakin baki daya dan haka cikin fushi da fusata, ya daure ta, sai da ya gana mata azaba bayan ya rufe mata bakin ta, ba duka ba zagi daura ta yayi ya a daure na tsawon kwana biyu cur ba ruwa ba abinci. A ranar na ukun ne bayan ya dawo fada, ya kunce ta ya zuba mata abinci a ƙasa, haka yayi ta cin abincin tana kuka. Wani irin kyamarta yake ji shi yasa ya gaza kome da ita, tana gama cin abincin, ya farmata mata kamar tsohon zaki babu d'igon imani kamar yadda ta saka iyayen ta da matar shi kuka haka yake far mata, yana gaya mata magana masu zafi tare da alwadar din ta, duk wani cin zarafin da ya dace ayiwa mutum ya mata. Sai da ya kai wani lokaci yana mata wani mugun aikin da bata san tana duniya ba ko tana lahira bane, dama sabida haka ya sha maganin kara kuzari da lafiyar shi ma ya aka kare balle ya kara da wanda ya kara haukata shi.

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now