BABI NA TALATIN DA UKU

448 125 17
                                    

BABI NA TALATIN DA UKU.
M. GOBIR
Bayan shekara daya, masarautan ta zama masarautan mafi karfi a cikin nahiyoyin baki daya, domin idan aka kai da zancen mulki ne tsagoran Jarumai da yakine sai da ta mamaye manya da kananun yanki tsabar karfin mulki, ya kasance a lokacin babu wani wanda ya isa d'aga musu murya ko musa musu idan suka ce suna son abu, a haka a cikin masarautan zaluncin da ake ya fi kome dagawa bayin Allah hankali, gashi dai babu Sarki Bello babu Aminatu sai da suka yi danasanin hada kai domin cutar da Bello, ana cikin wannan yanayin aka nemi Baffa'm aka rasa, babu Sarkin Gida babu labarin shi,
Da wannan aka shafe tarihin shi dama Aminatu ta gaya mishi soyayyar su, tarihin su watan wata rana zasu zama tarihi toh kuwa sun zama, domin babu ma wanda yake iya tunawa da shi. Shi kan shi Waziri Zakaria sai da yayi da gaske domin an so a mishi tawaye, Allah ya taimaka shima ba sakarai bane..
A bangaren Bingel, itama tana tsoma musu baki a sha'anin shugabanci masarautan, duk da sun fahimci so take mulkin ya dawo wurin danta, amma basu yi yunkurin mata kome ba, domin ko sun so haka, dole suke hakura dan a shirye suke ita da danta dan shekara biyu, dan haka ita ce macen da ta rage na Baffa'm, waziri Zakaria bai yi kasa a gwiwa ba, idan aka fara magana yana tuna musu ita ce take da ikon akan mulkin masarautan dan haka su gama abinda xa su yi dan ta shi zai maye gurbin Sarki nan gaba, tunda shima Yakubu ai rikon kwarya ne, da wannan dayawan mutanen fadar suka bazama niman Sa'a. A cikin wadanda suke faffutukar mulkin ya dawo hannun su, har da Chiroma dan haka zama yayi a gaban wata yar bori.. bayan ta gama haukata da faduwa a kasa ta kalle shi sannan ta ce mishi.
"Dukkan ku ba zaku iya ba, kuma ba zaku tab'a cimma matsaya ba, Aminatu da Bello sune kawai zasu iya, toh kun Kore su. Mulki kuwa tana tafe ne d zuciyar mutum Yakubu mutum ne a badili a zahirin shi kuwa fitanannen kuke gani ba, Gara shi dan haka ko ka hau mutuwa ce zaka samu madadin mulki magadan masarautan suna nan tafe. Lokacin kukan ku ya fara kayi fatan mutuwar ka kafin isowar Zakin fama, an haife su ne domin tabbatar da adalci, a dare mafi girma da albarka, dan haka kamar yadda kuka saka iyayen su kuka haka zasu saka ku kuka, ganin su kawai sai ya haifar muku da hargitsewar hantar cikin ku.
Sautin takun su, kawai abin a gudu ne, iya su kawai gayya ne a filin yaki dan haka kuyi ta kanku."
"Ban gane me kike nufi ba?" Ya tambaye ta, kallon shi tayi tare da kallon tukunyar sidabbarun ta, sannan ta girgiza kai kome ya shafe bayanan da ta samu sun B'aci, kafin ta tattaro wasu bayanan sai shake mata wuya aka yi. Ta shiga kakari da kyar Allah ya kwace ta, cikin masifa ta ce mishi.
"Fita min a bukka, ka tafi ka nimo. Aminatu ita ce zata iya taya ka samun mulkin ba kowa ba" zaro idanu yayi taya haka zai faru, bayan shi ya kitsa yadda kome zai tafi domin cimma manufar su ta son mulki duk da shima yana da na gaba da shi. Baya shi ya kitsa kome ba, shima haka aka turo mishi ya aiwatar, toh ya gaji da yiwa wani bauta ne, yake son ya ci gashi kansa. Haka ba zai samu ba sai ya zama sarkin gobir..
*
Borno
Bayan shekara daya.
Innayoh ce ta tallafo, Gidado da jikin shi yayi laushi. Lamido yana kwance shima amma jikin shi bai kai na gidado laushi ba. Wanka tayi mishi da ruwan magani, sai kuka yake. Sannan ta mika shi ga Mahaifiyar shi.
"Innayoh bakin shi ya feso da wasu kuraje fa"
"Eh haka bakon dauro yake, gashi kin ga Lamido kamar bayi ciwon ba, ta Gidado ce tayi yawa." Saka mishi mama tayi a baki ya dawo da maman yana kuka,
Jakadiya Baabaghana ce ta shigo ta zauna tana faɗin.
"Fulani bani shi na wanke mishi bakin nan da yake darewa, haka kawai yaro ya koma wani iri."
"Toh ni kan ba zan iya ganin yadda zaku dauki alhakin Uban ɗakina ba" inji Innayoh ta dauki Lamido suka fita, haka Baabaghana ta wanke bakin Yaron nan tass, har yana jini. Dake a shekaran an samu yawaitar cutar bakon dauro, shine fa Yaran suka kamu da shi, Lamido Hassan ya fara yi amma bai wani jima ba, sai ga shi Gidado Husaini ya kama, shima.

Haka aka yi ta jinyar su, har tsawon wata guda, kafin suka warke sai dai baya magana, baya hum baya uhum. Aikuwa Aminatu tayi kuka a lokacin. Mai Martaba da kan shi ya tura su, har Chadi, aka duba shi anan aka fahimci zai yi magana kawai cutar da yayi ne, ya taba wuyar shi dama bakon dauro yana wannan illar wa yara. Haka suka dawo. Idan Aminatu ta kalle shi kuka take baki daya sai Tausayin shi da kaunar shi ya danne soyayyar Lamido Hassan. Shima ganin yadda Mahaifiyar su, bata ta shi yasa ya koma jikin Innayoh abin shi, karshe shi kan bai wani sha mama har aka iyaye su ba, shekara daya da wata biyu ya daina amsar mama, dan wani lokaci idan yazo shan Maman, yana kamawa Gidado zai taso, ya kama shima, shi kuma Allah ya daura mishi son aba shi abu shi daya, duk abinda suke Innayoh tana lura da su, shi Gidado son dan uwan ne yake saka shi Yana ganin zai yi sha sai shima ya taso ya ce zai sha wani lokaci ba shan yake ba, kallon dan uwan yake yana mishi wasa, amma dan baten da buje, sai ya bata rai kamar ba shi ba, da wannan yanayin ya barwa Gidado nonon baki daya, har Aminatun tana kai karan shi wurin Innayoh aikuwa ranar ta sha mita a wurin Innayoh ta ce mata.
"Tunda Yarima Gidado ya samu matsala kika manta da biyu kika haifa ba daya ba, soyayyar ki ta uwa da kulawa kin daura akan Gidado, shi kuma ko oho, ba dole ya hakura ba, lokacin da xai sha shi kuma dan nime me kama da Bororoji ya taso yace zai sha, ya bar muku kayan ku ya kama hatsi sai kuyi ta dama da shi"
"Ayya ayya Innayoh"
"Ba wani Ayya ayya" da haka suka bar zancen. A hankali Yaran suna tasowa so da kaunar junar su, yana kara bayyana domin tun daga ranar ta hade kan Yaranta, a hankali suke kara girma kamar su da mahaifin su yana kara bayyana, har ma sun so zarce shi kyau sabida hasken fata da kuma siririn hancin irin na Mahaifiyar su.
Duk da haka sai da Lamido yayi dan duhu kaɗan. Ba kamar Gidado da yake da hasken fata sosai ba.
Rashin maganar Gidado shi ya haifar da rashin maganar Lamido, dukkan su suka taso ba su magana, sai tsabar rashin jin. Musamman Lamido, duk inda ya zauna sai ya takalo fada. Yayin da shi kuma Gidado idan ya zauna zaka samu ko yana cikin matsanancin farin ciki, ko kuma ya ga abu yana burge shi.
Suna da shekara bakwai a duniya, wani abin mamaki ya faru bayan sun dawo daga karatu a wurin mai Martaba, sun zo zasu wuce aka samu labarin wani mahaukacin doki ya tsinke a cikin barga, kowa gudu yaƙe dan har an je kiran Madawaki, wato sarkin dawakai, ga Sarkin gida da Sarkin yaki, da wasu dakaru a tsaye aba tattauna yadda zasu kama shi, kutsa kai yayi cikin su ya tsaya yana sauraron yadda xa a tare dokin, aikuwa ya wuce ta cikin mutane har wurin bargan, ya tsaya kamar wanda aka tura shi, hawa yan itaccen da aka yi bargan da su yayi, sai lokacin Jama'a suka hango shi, kafin su dakatar da shi Lamido ya daka tsalle akan dokin nan, tare da fisgar linzamin dokin, suka ficce daga cikin masarautan, sai yakuwa Mutane suke. Sai da ya nufi can bayan katangar masarautan, kafin ya ja linzamin dokin suka fadi baki dayan, lokacin labari Ya same su ita da Innayoh. Shi kan Gidado bai san yadda zai bata labari ba, tunda ya samu damar fisgar sunan Lamido da doki bai kuma cewa kome ba, sai kwatance yake mata da hannu, dake sun saba da bayanin shi sosai musamman Innayoh da Lamido. Idan ranta yayi dubu sai da ya B'aci, koda aka tafi wurin su, tashi yayi yana karkade jikin shi, sannan ya ratsa tsakanin mutane ya wuce kamar ba shi ba, idan ka ga yadda yake turnike fuska sai ka rantse da Allah ba shi yayi wannan takadarirrancin ba, a hanya suka hadu da Sarkin yaki ya ce mishi.
"Yarimar Gobir zaka iya bani damar baka horon yaki?" Kallon gefe da gefe yayi, sannan ya sadda kan shi kasa.
Shima kuma Sarkin yaki cikin girmamawa ya zube a gaban shi yana faɗin.
"Ina farin cikin bawa Jinin Gobirawa horon yaki, ka Amshi haka a matsayin kyautar abin da ka min" kallon shi yayi sai kuma ya samu kan shi da gyada kai.
Dan haka Sarkin yaki yana baya, Lamido ka gaba suka isa bangaren su, sannan ya juya, shi kuma ya shiga cikin gidan, kamar bai yi kome ba. Kallon fuskar Innayoh yayi ya fahimci ran Ammyn shi a bace yake, da gudu Gidado ya so wurin shi. Cikin maganar shi ta kurame ya ce mishi.
"Lamido ya aka yi ina dokin?"
Saka hannun shi yayi a kan daya sannan ya juya hannun ya ɗan yarfe, wato yana nufin.
"Ai ya mutu na fitar da shi daga cikin bargan"
Cikin zakuwa Gidado ya kuma watsa hannayen shi dukkan biyu yana cewa.
"Kai da gaske ya mutu?"
Wani hade fuska yayi ciki ciki, kamar ba shi ba, take Gidado ya sake murmushi yana girgiza kai tare da saka hannun shi a kunne yana motsa bakin shi.
"Tuba nake Yayana, tuba nake Hassan dina, Tuba nake Lamidona" sai a lokacin ya ɗan sake murmushin gefen baki iya, ai kuwa Gidado ya fashe da dariya, yana murna tare da dannewa bayan Lamido aukuwa ya dauke shi, har zasu shiga sai ya sauka.
"Karka shiga ran Ammyn ya b'aci" ya fada mishi da hannu, sunkuyar da kai yayi kafin ya cire takalmin shi, ya shiga cikin dakin, tana nan inda ya saba ganin ta rike da wani farin gashi bai san na meye bane amma yana da yakinin abu yana da daraja a wurin ta, a wayo da yayi duk lokacin da ya ganta ta kebe shi yake jan hannun Gidado su fita bayan son Gidado yaga kukan ta. Shiga yayi ya zauna a gaban ta, har lokacin kuka take sosai. Bai ce kome ba dan dama bai cika sakewa da ita yayi magana ba, abokiyar maganar shi ce kawai take iya isar da sakon shi wurin ta, wato Innayoh idan kuma ta shiga irin wannan yanayin shi yake koran su ya ce a barta tayi kuka, Allah yayi mishi kaifin basirar da yasa yake gane yawan kukanta ba wai yana ta'alaka bane akan su, akwai ciwon da yake damun ta, shi yasa idan zata yi kukan shi daya yake zama a kusa da ita, idan ya ga taki shiru sai ya fita ya nufi bayan tagarta ya zauna, tare da ɗaukar wani sarewan da Mai Martaba Sarki Muhammad Omar, ya kawo musu daga Saudiya yayi ta busawa. Har sai ta tura a kira shi. Yau ma haka ce yake shirin faruwa. Dan haka ya mike zai fita sai lokacin ta ce mishi.
"Lamido!" Cak ya tsaya,
"Karka sake shiga cikin gidan sarautar nan da sunan wani taimako idan ba so kake na mutu ba" kamar wanda ta zuba mishi ruwan sanyi haka ya juya yana kallon ta. Lumshe idanun ta hawaye suka zubo mata, tare da gyada mishi kai. Lashe bakin shi yayi sannan ya gyada mata alamar yaji.

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now