BABI NA HAMSIN DA BIYAR

379 127 25
                                    

BABI NA HAMSIN DA BIYAR

Wani irin zaburar dokin yayi, tare da kaiwa Gidado cafka ya sha gaban shi.
"Insha Allah zan nima maka, amma da sharadin zaka kula Fulani Bintu domin ta cancanci zama wata alkaryar agefen ka"

Dariya yayi ya kara a guje, yana me kallon Lamido har suka bar masarautar, sai da ya raka shi wajen gari lokacin an fara sallah asuba suka tsaya suka yi,sannan yana kallon Lamido ya bar kasar borno,cike da kewar juna. A hankali ya juya baya, yana jin kamar ya bi dan uwan shi.

Shi kuwa Lamido ko juyawa bai yi ba, domin yana jin yadda dan uwan shi yake kallon shi yasan kewar shi yake ji, dan haka yaki juyawa shima ai kewar Gidadon yake ji.
Haka yayi ta tafiya sallah da cin abinci yake tsayar d shi, sai da yayi tafiyar wuni guda. Kafin ya yada zango ya kwanta.
**
Wannan abin da ya faru sai da yasa Anum ciwo sosai, domin ko magana bata yi, muryan ta ya dishe ainun bata ko iya wani motsin kirki jikin ta kamar an kareraye ta, idan ka ganta akwance kamar danyen nama, ga masifar Inono, ga fitinar matan gidan su.
A hankali tayi ta ja da ciki domin yunwa take ji, tura kofar karanta tayi ta hango Dadah tana ta kokarin sauke dafaffen madara, sako kai tayi tana kallon ta. Hawaye na zuba daga idanun ta, yunwa take ji kamar tayi ihu, amma ba a jin me zata ce. Dan haka ta daura kanta a dokin kofar, tana kuka a hankali, wani irin Haushin Mamanta take ji akan me bazata tafi da ita ba, ina ma take yanzun,gashi Abbanta ya rasu bata da kowa sai Allah.
Kamar ance Dadah ta juya, idanun ta ya sauka kan Anum da take kwance. Komawa daki tayi ta dauko fura ta dama sannan ta zuba zuma a kai, sannan ta zuba dafaffen madara, ta kawo mata. D'aga ta tayi sannan ta yi ta bata da bakin ƙwaryan anan ta fahimci ciwon Anum har da yunwa, dan tana bata,ta shiga sharbe zufa.
"Me yasa wannan ranar kika fita cikin dare?"
Kurawa Dadah idanu tayi sannan ta ce mata.
"Nima Gwaggo Bingel ce ta saka aka tafi da ni" sanin halin Anum bata yarda da kowa ba, balle har tayi magama da kai, sannan yarinya ce da tun tafiyar Mahaifiyarta duk abin da zata fada gaskiya ne, bawai ta yarda anum ba zata mata karya bane, amma bata san lokacin da zuciyar ta ya amince da abin da Anum din ta fada mata ba.
"Kiyi hakuri kin ji, haka Allah ya halicci wasu da son zuciya, nasan Barkindo baya cikin masu irin wannan yanayin don Allah ki kaunace shi"
Hawaye ne ya zubo mata, ta kauda kan ta sannan ta ce mata.
"Daadah ina niman wanda zai kare rayuwa ta ne ba wanda ni zan bashi rayuwa ta ba, Daadah hawai na rena tayin bane Wallahi sam bai min ba, ina son shi amma ba zumunci, ban da son soyayya da za a gina rayuwar aure akan su ba."
Cike da mamaki take kallon Anum gashi dai gaskiya ta gaya mata, amma ya zata yi da Bingel da ta matsa lallai ta nima mata yardan Anum.
"Baki ganin shi din sarki ne gaba" goge bakin ta tayi tana kallon Daadah sannan ta tattaro hankalin ta baki daya ta Zubawa Daadah.
"Daadah shi mulki jarumi ake nima, wanda zai gyaran murya jikin kowa ya dauki rawa ba Lusari ba wanda da shi da babu ɗaya ne"
Murmushi Daadah tayi tana faɗin.
"Mulkin baya gabanin kenan?"
"Eh Daadah" ta fada lokacin da ta hada karfi da karfe ta mike, ta fita waje.
"Toh yar iska kin samu lafiya daga yau ba zaki kuma fita domin aikin wasu ba, su shanun da Ubanki ya bar Miki mune zamu miki kiwon su?" Tura baki tayi tana faɗin.
"Idan aka ce na tafi da su kiwo ai ba zan ki tafiya da su ba, da sai an hada da Ubana da yake kabarin shi bai ji ba bai gani ba, Insha Allah yau babu me shan ruwa cikin salama" ta fada kasa kasa,tana nufar waje bayan ta dauki tulun diban ruwa, tun da tafiya ta tafi bakin rafi ta zauna tana kallon ruwa, a hankali ruwan ya shiga rinewa zuwa jajjur kamar ruwan jini, ita kanta idanun ta wani irin rinewa yayi kamar yana ci da wuta, Murmushin keta tayi tana faɗin babu me shan ruwa cikin salama sai kun ji a jikin ku.
Sannan ta dauki tulunta ta tafi bakin rafin ta shuri ruwan, aikuwa inda yake ya sauya zuwa ruwa me kyau da ɗaukar ido, diba tayi da saka akan.
"Naga wanda zai sha ruwan nan"
Haka kawai take jin yin mugunta, tana tafiya aka yi dace wasu tsuntsaye suna ihun su na alamar a firgice suke, d'ago kai tayi ta Kalle su, murmushi tayi aikuwa suka fado suna me ci da wuta.
Tsabar masifar da take ji a ranar duk in da ta saka kafarta, wuta ne yake kama wurin yayi bakikkirin.
(Wannan shine yanayin da Baffa'm yayi kokarin hana Aminatun shiga idan har ta kai yanayin haka amadadin alkhairi a ranta amfani da baiwar ta zata yi tayi tana cutar da mutane, a binciken da aka yi wani cibiyar nazarin ilmin dan Adam, sun gano kowani dan Adam yana da Super natural,shine ake kiran shi da Kambun baka, kuma kowa yana da wannan baiwar sai dai wasu kalilin ne nasu yake fitowa, wasu kuma idan ya bayyana iyayen su na maza a boye musu dan kar ya zama tashin hankali a gare su da Al'umma)

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now