AN YI SAKE....01

79 2 2
                                    

AN YI SAKE...
       SHAFI NA ƊAYA.
Mallakin FIRDAUSI S. ALIYU.

     DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI.

***
    'Yar mace shi ne sunan da mutanen unguwarmu suke ba da kwatance na ga kowa, sai dai ban taɓa ɗauka sunan wani giɓi na rayuwata ba, domin a iya wayo da tunanina ina ganin kowanne ɗa ko 'ya   dukkan mu 'Yayan mace ne, domin mace ce ta durƙusa akan guiyoyinta tsayin awanni ko kwanaki kwatankwacin tsayin wahalar da Ubangiji ya yanka mata kwatankwacin azabar ciwon da ta shanye kafin zuwanmu duniya, bayan tazarar shuɗewar watanni tara mun rayuwa a cikinta cikin wahala da juriyar ciwo kala-kala, kafin girma da mallakar hankalin kanmu ta jure faɗi tashi na wahala damu tsayin shekaru ba tare da gajiya wa ba, a ganina idan har ba a kiramu da 'Yayan mace mun amsa ba da wane suna za a kiramu mu amsa? Saɓanin nawa sunan da ya dinga amsa kuwwa kafin ɓulluwar wannan, wato Shegiya ko 'Yar shege ba laifi don mutane sun rasa sunan da ya da ce su kira ni da shi duk da cewar ina da sunan yankan da aka ba ni kamar kowanne ɗa a duniya mene laifina don na rasa adon sunan Uba a gaban sunana kamar kowanne cikakken mutum na duniya? Mahaifiyata wacce ta durƙusa ta kawo ni duniya ba ta taɓa ba ni damar sanin ko ni wacece ba, a karan kaina ina tambayar wacece ni? Amsa ni baiwa ce, dole na ce baiwa mana domin tun bayan buɗe ido da yin wayona a duniya babu wani karatu da ƙwaƙwalwa da gangar jikina suka yi haddarsa sama da bauta, har takai ta kawo wasi-wasi na bilin-bituwa a cikin kaina na cewar anya kuwa Mama ita ta haife ni? An ya ni ba 'yar tsuntuwa ba ce ko kuma shegiyar kamar yadda sauran mutane suke faɗa? Idan har ita ce mahaifiyata mene ya sa ta ƙi ba ni dama na rayu kamar sauran 'yaya? Mene ya sa ta hanani soyayyarta? Mene ya sa taƙi jinin ganin farin cikina a duniya? Kowanne rai na duniya yana da buri a rayuwarsa amma ni babbar burina bai wuce na samu hutun 'yan sakanni na zauna ina tunani irin tunanin da Bahaushe ke kira da wasikar jaki ba, idan akwai abin da nafi kauna kuma yake sani farin cikin to wasiƙar jaki nake karantawa a kaina, kwakwalwata ita ce abokiya kuma aminiya a gareni, saboda ba ni da wanda zan raba farin cikina da damuwata biyu na ba shi rabi sai ƙwaƙwalwata, ina aiki da abin da ta karanta min sosai fiye da abin da na gani a zahiri ko na ji sautinsa cikin majiyata.

"Zahar.. ! Ke Zahar wai ba da ke nake magana ba? Uban me kike yi ne kina ji ina magana.?"
  Tabbas sunana Zahar, Zahar shi ne sunan da ya da ce na ji sautinsa a kullum fiye da wanda nake jin ana ambata mini sau dubu a kowacce rana, firgigit na farka sai a lokacin na lura da ledar omon da ke hannuna a tunanina kayan wanki na saka a cikin ruwan kumfar, sai dai saɓanin tunanin nawa omon na juye kaf a cikin ruwan.
   "Na shiga uku..!."
Na faɗa ba tare da sanin iyakar inda sautin nawa ya kai ba.
  "Ai ba ki ga shiga uku ba sai na zo na iske ki a gaban wankin nan, idan ban da raini ya fara ratsa tsakanin mu har yaushe zan ta kwaye murya ina rafka muki kira kina ji na Zahar."
   Maganganun Mama na jiyo suna kara kusantowa gare ni da sauri na dulmiya hannuwana a cikin ruwan da na fita tun asubar fari na ɗebo shi bokiti ɗaya kafin su ɗauke ban damu da ɓacin ruwan ba na yi wajenta da gudu saboda fargabar idan ta zo ta tarar da aika-aikar da na yi na kaɗe na bushe har guntun kashina.
   Ina isa bakin ƙofar ɗakin tana sanyo kai ita ma da zummar fitowa,  kallon-kallo muka hau yi tsayin lokaci ina wurwurga ido alamun rashin gaskiya ƙarara sun bayyana a tare ni.
   "Kin gama wankin.?"
Ta ambata tana yi mini wani irin kallo mai ɗauke da alamun tuhuma, da sauri na girgiza kai maimakon ba da amsa da ba ki, ta watsomini ragowar kayan wankinta da ke rike a hannunta akan fuskata suka zube ƙasa.
   "Ungo nan wato kema ƙanƙanuwarki da ke kinsan takan ha'inci ko.?"
  "A'a Mama bangansu ba ne wallahi."
Maimakon ta ba ni amsa harara ta wurgomini na amsa tare da sunkuyar da kaina ƙasa, domin ko tari Mama ta yi nasan abin da take nufi da ni ba iya harara ba, jikina na rawa na hau tattaro kayan da ta watsomin a kasa, kafin na tsinkayi sautinta a cikin kunnuwana sautin da ke firgita tunanina ya kuma hautsina dukkan nutsuwar kayan cikina.
   "Ki yi ki gama na gaya miki yau tare da ke zamu je gidan Ad.."
  Ta ɗan ja tsaki mai sauti kafin ta ɗora "Gidan Alhaji Adam, domin kema ƙarfinki ya kawo gara na kaiki ko na samu ragautar wasu ayyukan."
   "To Mama bari na yi sauri na gama."
Na juya da sauri har ina ɗan cin tuntube, duk da ban juya ba nasan kallona take yi,  kafin ta koma cikin ɗakin ta ci gaba da abin da take yi, Gidan Alhaji Adam gida ne da Mama ta shafe tsayin shekaru wanda ba zan iya ƙididdiga wa ba tana aikin bauta a cikinsa, mai kuɗi ne na bugawa a jarida, don ni buɗar ido na yi na ga tana aikatau a wannan gidan wanda da ɗan abin da ake biyanta duk ƙarshen wata take kore mana wasu ɓukatu na yau da kullum, sannan kuma a kullum Mama ta dawo za ka ganta ɗauke da ɗan ragowar abinci ta taho mana da shi, saboda ɓangaren girki Mama take aiki, bansan ƙudirin Mama na kai ni gidan aiki ba, amma a tunanina hakan ba ya raba nasaba da nacin son karatu da nake yi, tun ina ƙarama ta kafin kawowar wayona ina kaunar duk safiya na fita ƙofar gida nakan ɓata lokaci wajen kallon yara sa'annina har ma da manya suna ta layin tafiya makaranta, da na fara tasawa kuma da gayya nake sulalewa na tafi primary na laɓe jikin taga ina leƙen abin da malamin yake koyarwa a kowanne ajin da Allah ya ba ni iko a ranar, haka idan yamma ta yi Islamiyar unguwarmu har ƙasan layi babu wacce ban sani ba, duka kuwa babu kalar azabar da jikina bai ɗauke ba a kan hakan, ban manta wata rana da wani malami a she yana ankare da ni a kullum a Islamiyar yadda nake laɓen taga ina tsintar karatu, a ranar ya ce na zo, ba tare da tsoro ko fargaba ba na zagaya wajensa gaban aji, take ya yi mini wasu 'yan tamboyi na amsa har da cewa na kawo haddarsa da ya bayar a satin na alƙur'ani a take kuwa na kawo ba tare da gyara ba, a ranar har gidanmu ya je yana roƙon Mama ta bari na dinga zuwa makaranta, idan ma kuɗi ne matsalar shi zai ɗauke nauyin komai, Mama kuwa ta rufe ido ta zazzagawa malamin nan ruwan rashin mutunci ta kore shi, a ranar na tabbatar da cewar na zo duniya, domin azabar da na sha ta shafe dukkan wacce na kwashe tsayin shekaru ina girbarta, kuma duk da haka ban daddara ba sai idan har Mama ba ta aike ni ba, amma tabbas da na ga ƙafa sai na je, ta haka ne na ɗan samu ilimi akan yadda zan ɓautawa Ubangijina da sauran ɗan abin da ba a rasa ba, yanzu ma nasan kaini gidan aikin yana da nasaba da ƙin jinin karatun nawa da Mama ta yi, wanda na rasa dalilin hakan.
   A gaggauce na kammala wankin cikin ƙanƙanin lokaci, saboda ban ba wa ƙwaƙwalwata damar da za ta shagaltar da ni ba a wannan lokacin, kai tsaye ɗaki na koma cikin 'yan mintuna na kammala shiryawa muka fice, Mama na shirin kulle ƙofar gidan na dubeta a hankali duk da yadda zuciyata ke bugun goma-goma da irin gargaɗin  da  take yi min ban  saurareta ba, cikin irin salon muryata mai rauni na furta.
   "Batun karatun kuma fa Mama.?"
A take ta ɗauke wuta daga abin da take yi ba tare da ta dube  ni ba, ni kuma har bayan fitar tambayar daga bakina zuciyata ba ta tsagaita bugu ba tamkar ana dukan ganga, na dauka za ta ce wani abu ko kuma ta rufe ni da duka domin babban abin da yake jamin wahala a wajenta to halina ne na kafiya da taurin kai, amma abin mamaki sai ta ƙarasa kulle gidan tare da jefa makullen a 'yar guntuwar fatattakakkiyar jakarta kafin ta ce "Wuce muje."
  Ba musu na bi bayanta tamkar raƙumi da akalarsa, muna tafe ina aikin da na fi kwarewa a kansa wato rubutun wasikar jaki, kamar daga sama na ji saukar muryata a kunnuwana.
  "Zahar."
Ta kira sunana, ba tare da jiran amsawata ba ta ɗora da faɗin.
   "Ban san wanne irin na ci da ƙulafici ne a ranki na son karatu ba, amma dai koma mene ne ba a ce dole sai mutum ya yi karatu ne kadai zai rayu a cikin al'umma ba, mu marasa karatun me muka nema muka rasa? Don haka ki ajiye batun karatu a gefe ki rungumi talauci da matsayinki."
  "Amma Mama karatun yana da amfani sosai kuma zai taimakemu zuwa gaba..!"
"Zahar ba za ki taɓa yin karatu ba a duniya, ki ma ajiye wannan tunanin a gefe tun da wuri, aikatau shi ne gadonmu shi ya dace ki yi kuma shi za ki yi."
   Kalaman Mama na ƙarshe suka daskarar da ni tare da sanya ni shan jinin jikina, lokaci guda na dauke wuta ban ƙara cewa komai ba har muka isa kofar gidan Alhaji Adam, take na manta da batun wani karatu,
   Tun daga bakin ƙatuwar ƙofar gidan bango guda naga duniya, naga inda kuɗi suke magana da bakinsu, a she banga komai ba sai bayan da idanuwana suka yi tozali da uwar dukiyar da aka narkar a cikin falon, na yarda da maganar mutane da suke faɗin aljannar duniya, tabbas akwai ta duniya kamar yadda na yi tozali da ita a yau, na zama tamkar zuwan ƙauye, domin yawanci a ƙauye ne ake samun Bagidajiya sai dai ga inda 'yar birnin ma ke nuna gidadancin na musamman, ni dai tun da na shiga bakin ƙofar falon na sanƙame ban motsa ba, illa kawai na ga Mama ta kama hannuna zuwa tsakiyar falon a yayin da na yi nutso da ƙafafuwana cikin wani irin kafet mai shegen taushi da laushi na zauna kamar yadda naga Mama ta yi, lokaci guda wani irin sanyi ya fara ratsa fatar jikina har wani sanyi-sanyi na fara ji, kafin na hangi tahowar wata mace zaune akan kujera irin wacce guragu ke hawa amma ita wannan ba irin wacce na saba gani ba ce, tana tafe ne tana danna wani abu a jikin hannun da kanta kujerar ke tafiya har ta ƙara so gare mu.
   'wannan ita ce matar gidan? Ita ce wacce Mama ke durƙusawa har ƙasa? Idan kuwa haka ne me zai sa Mama take kirɓata kamar mai shirin matsar mai a jikin tunkuza kuma ta zo nan ta na bautatawa sa'ar 'yar cikinta?.

Wace ce Zahar ne?.
Me kuke tunani a kanta?.
Kun yi tunanin dalilin  Mama akan Zahar?.

Amsar dai na cikin littafin AN YI SAKE... Ku biyo ni.

AN YI SAKEWhere stories live. Discover now