AN YI SAKE.. 15

21 3 2
                                    

   AN YI SAKE..
     15
©NWA
Firdausi S. Aliyu (QURRATUL-AY)

  Na ambata a cikin raina, ina mai ƙara ƙoƙari matuƙa wajen daidaita nutsuwata, sai dai na fahimci hakan ya gagara a gare ni.
   "Zahar..! "
Firgit na kai dubana ga mamallakin muryar da na ji ta doki dodon kunnena, da murmushi fal a kan fuskarta kamar yadda naga fuskar Momi ta yalwata sai dai kowanne murmushin yana da banbanci da yanayin kwanciyarsa a saman fuskokin su.
    Har a wannan lokacin da nake ɗaga ƙafafuwana da ƙyar ina ƙara kusantarsu, idanuwanta bai ɗauke daga gare ni ba, sai a lokacin hotunan kamanninta suka ƙara suffatuwa a cikin idanuwana, amma na yi ta maza na kanne kamar yadda na ga ta yi.
   "Ina kwananku Momi? "
Muryar Momi da ta likitan na ji sautin amsawar su kawai, kafin na sake ɗorawa da faɗin.
   "Ya jikin Aunty Ummi?"
"Jiki da sauƙi za a ce dai Zahar, ina Maman taki?"
  "Na barota a kicin. "
Daga haka shiru ya ratsa tsakaninmu, kafin ta gama yi mata allurai da sauran aikin da ya dace, tana faɗin.
   "Allah ya ƙara lafiya, idan ruwan ya ƙare sai a cire mata, ni zan koma saboda a bakin aiki nake, ina fatan dai tana kiyaye dukkan dokokin da suka hau kanta?"
   "Gaskiya Ummi na da ƙoƙarin kiyaye ƙa'ida sosai ma kuwa, sai dai da ke ciwo ba mai sawwaƙe shi, sai wanda ya ɗora maka. "
"Haka ne Allah ya ƙara mata lafiya."
  Muka amsa da amin, kafin ta haɗa kayayyakinta ta yi hanyar fita suna sallama da Momi, Momi tabi bayanta tana ambaton.
  "Muna godiya sosai Zaliha..! "
'Zaliha..! Tabbas ita ce, idan har zan iya tuna ranar da na fara tozali da ita a cikin rayuwata, dole na tuna da wannan sunan da na ji Mama ta ambata a ranar da ta zo gidan mu, me hakan yake nufi? Ta sanadiyyar gidan nan suka san juna, ko kuwa akwai dalili?' gabana ya faɗi a daidai lokacin da na tuna irin hirar da na ji suna yi sama-sama, duk da ban ji su sosai ba, amma tabbas a kwai wata ƙasa.
   
   "Tunanin me kike yi haka? "
Tambayarsa ta yi nasarar farauto ni daga duniyar tunanin da na faɗa, a hanzarce na dube shi tare da ambaton.
  "Babu komai. "
Kai kawai ya girgiza, na san hakan ba ya raba nasaba, da rashin yarda da amsar da ba shi ne bai yi ba.
   Miƙewa ya yi tsaye yana dubana, kamar yadda ni ma na kasa ɗauke idona daga kansa.
   "Ki kawomin Breakfas ɗakina, don ban karya. "
Bai jira jiran amsar da zan ba shi ba ya fi ce daga ɗakin.
   Tagumi na yi a yayin da zancen zuci yake ƙoƙarin mamaye zuciyata, na yi ta maza wajen ya ki ce shi, ina mai miƙewa da sauri na fi ce daga ɗakin, don tun shiga ta Aunty Ummi bacci take yi, to har a yanzu da na fito ban ga alamun tashi daga gareta ba.
     Kai tsaye madafa na nufa wato kicin, na isar da saƙonsa ga Mama a kan kai masa abincin karinsa.
    Ko kallona ba ta yi ba, ta fara ƙoƙarin shiryamin kayan abincin a kan babban tire, kafin ta kalle ni a karo na farko lokaci guda na ji saukar muryarta cikin majiyata.
    "Ruwanki ne ki riƙe da kyau, ko ki zubar, amma ki tabbatar da kin dawo da wuri, don ba na son wannan liƙe masa da kike yi, tsabar rashin kamun kai, kuma na san kin kwan da sanin zan je unguwa. "
   "Ina za ki je Mama? "
"Wani sabon tsari ne ya zo miki na cewar duk in da zan je dole sai kin sani? "
Ta kai maganar tana mai tsayar da ƙwayar idanunta a kaina.
   "A'a Mama, na dai tambaya ne ko wani zai tambaye ni?"
  Na ba ta amsa a daburce, wani dogon tsaki ta ja, tare da juya min baya ta ci gaba da abin da take yi, ko tantama ba na yi, na san idan zan ruɓe a tsaye ba kuma tankamin za ta yi ba, hakan ya sa na kinkime kayan abincin na yi hanyar sashen Yaya Tarik, a yayin da nake ƙara jefa ƙafa a sannan bugun zuciyata yake ƙara tsananta, kusantar wajen nake yi, amma ina ji kamar ana nisanta ni da sashen ne, sai da na yi ta maza wajen dakewa kafin na sadu da ƙofar falon nasa, ba buƙatar na ƙwanƙwasa ƙofar domin na lura da cewar a buɗe take.
   Da sallama na sanya kai cikin ɗakin, ina mai neman wajen tsayuwata, na ja na tsaya kamar yadda ya shatamin layi.
   Zaune yake kan ɗaya daga cikin manyan kujerun falon, yana duba wannan abin da Aunty Ummi ta ce min sunansa laftof, kafin ya bar abin da yake yi ya dube ni da faɗin.
    "Kawo min nan. "
Da ɓarin jiki na ƙarasa gare shi, na russuna tare da ajiye tire ɗin a gabansa na ja na tsaya.
   "Zauna mana. "
  "Na'am."
Na ambata duk da cewar na ji me ya ce.
  "Na ce ki zauna, ko domin tsayuwa aka yi ki? "
"A'a, gani na yi..! "
"Na ce ki zauna. "
Ya katse ni, ba musu na nemi guri na tsuguna kamar mai biɗar neman gafara.
   "Zauna sosai, magana za mu yi da ke, kuma maganar na buƙatar nutsuwar gaske. "
  Gabana ya faɗi tun kafin ma na ji wacce magana ce, amma a can ƙasan raina addu'a nake yi, tare da fatan Allah ya sa ko ma wacce magana ce zai yi da ni kada ya buɗo abin da ya shafi shafin rayuwata.
   "Kafin nan fara da wannan. "
Ya katse ni daga tunanin da nake yi, a hankali na kai maganaina gabana, na yi tozali da kofi cike da ruwan shayi mai kauri, a gefe guda kuma zubabben kayan ciki da soyayyen kwai da kaza, cikin mazubi daban-daban, ido waje na bi shi da kallo, a yayin da alamomin tambaya suke ƙara bayyana daga gare ni.
   "Ki ci mana, kafin mu yi magana. "
Ya ba ni amsar tambayata tun ma kafin na yi tambayar, da rawar baki na furta.
   "Amma Yaya.. "
"Shishshsh."
Ya ambata, bayan ya ɗora yatsansa ɗaya akan leɓansa, kafin ya ce.
   "Ba na son musu, ki ci kawai tun muna mu biyu. "
Kai na girgiza, tamkar wata ƙadangaruwa, kafin na hau kokawa  da kwai, saboda tsabar ruɗewa, ina ƙokarin gutsura yana yi min taurin kai, ban yi aune ba, sai ganin hannunsa na yi cikin kwan, ya gutsura tare da miƙomin, ba tare da ya yi magana ba, ni kuwa na kafe shi da ido kamar ban fahimci abin da yake nufi ba, murmushin gefan baki ya saki lokaci guda ya nufo bakina da wainar kwan, cikin sauri na sanya hannu na karɓe, tare da dannata a bakin nawa ba tare da na shirya ba, wannan lokacin murmushi ya yi bayyananne har sai da haƙoransa suka fito fili.
   Haka na yi ta ci gaba da cusa kwan ina kurɓan ruwan shayin tamkar magani nake jinsu, duk kuwa da irin daɗin su, saboda yadda ya kafe ni da idanuwa ba tare da ƙiftawa ba, shi yake ƙara daburtar da ni.
  "Kin san Dakta Zaliha ne? "
Tambayar da ta yi sanadiyyar dawo da naman kazar da na gutsura a lokacin, na ji kamar an sanya hannu biyu an shaƙe ni, lokaci guda na hau kakari tamkar raina zai fita, da azama ya ɗauko ruwan gora da ke kusa ya nufi bakina da shi, ba musu na karɓa na hau ƙyanƙyama kamar ba gobe, har sai da tarin ya lafa sannan ya cire min ya koma ya zauna, yana mai ci gaba da kallona, ni kuwa har da guntun hawaye, abincin da na ji ya fita a kaina ke nan, na ture gefe ina faɗin.
    "Alhamdulillahi! Na ƙoshi Yaya, bari na je kada Mama ta ji ni shiru. "
Da kallo ya bi ni kawai, sai da ya tabbatar da gaske tafiyar zan yi, kafin ya ce.
  "Kin manta me na ce miki? "
"To ai ban ji ka yi maganar ba ne, na ɗauka wasa kake yi? "
"Ita tambayar da na yi miki ba magana ba ce? "
  Shiru na yi a wannan lokacin, ina mai bin zanen kafet din wajen da kallo.
   "Ki ba ki amsa mana. "
"Ni fa ban santa ba. "
"A'ishatu!"
Ya ambaci sunana take na ji jinin jikina ya tsinke, yana kai kawo tsakanin dukkan jijiyoyin da suka yi wa sassan jikin nawa ƙawanya, bai damu da amsawata ba, ya ɗora da faɗin.
   "Har yanzu ba ki yarda da ni ba? Har yanzu ba ki tsayar da ni a matsayin wanda zai iya shiga rayuwarki ba? Me ya sa? Me ya sa kike min kallon mutum kamar kowa? Duk da cewar ƙwayar idonki na ƙaryata abin da zuciyarki ke raya miki? Ki yarda da ni don Allah, domin ina da tabbacin za ki same ni cikakken ɗan adam, amma ba butulu ba, zan yi miki dukkan halaccin da kike fatan samu a kullum, da sannu ina da yiƙinin dawwamuwar farin ciki a cikin rayuwarki, daga ranar da na fara ganinki har izuwa ƙarshen numfashina, Aisha wannan alƙawarina ne! Don Allah yau ya zama na ƙarshe a kan dukkan abin da za ki gayamin ya kasance gaskiya ne, ki dinga yi min magana da dukan gaskiya da yardarki, zan sake tambayarki a karo na biyu ba tare da gajiyawa ba, shin kin san Daktar Zaliha? "
    
   A take na ji maganganunsa a gare ni sun bi dukkan zaren jijiyoyin jikina sun ɗaure ɗam, har ina jin yadda harshena ya yi nauyi matuƙa a wajen ƙoƙarina na yunƙurin ba shi kishiyar amsar tambayar da yake jifana da ita, sai dai kuma kallon ƙwayar idanuwansa da na yi, hakan ba ƙaramin tasiri ya yi ba, wajen daƙile kalmomin da nake yunƙuri wajen shiryawa a cikin raina, domin kuɓuta daga sauran tuhumarsa a gare ni.
   Amma kuma mai zai faru?.

  TSOKACI.

Kada ku ga ina rubuta muku wasu kalmomi da tsagwaron Hausa, maimakon rubutun su da Turanci, idan har ba ku manta ba Zahar ba ta yi karatu ba, don haka ba ta da ilmin yim amfani da yaren da ba na Uwa ba, kuma wannan labarin muna saurarensa ne kai tsaye daga gare ta, domin Bahaushe ya ce, waƙa a bakin mai ita tafi daɗi.

Na gode sosai masoyana, da ƙoƙarin juriyar bibiyar wannan labari nawa.

QURRATUL-AYN

AN YI SAKE..
#NWA
#comment, like, share.

        
  

   

     

AN YI SAKEWhere stories live. Discover now