Yar mace shi ne sunan da mutanen unguwarmu suke ba da kwatance na ga kowa, sai dai ban taɓa ɗauka sunan wani giɓi na rayuwata ba, domin a iya wayo da tunanina ina ganin kowanne ɗa ko 'ya dukkan mu 'Yayan mace ne, domin mace ce ta durƙusa akan guiyoyinta tsayin awanni ko kwanaki kwatankwacin tsayin wahalar da Ubangiji ya yanka mata kwatankwacin azabar ciwon da ta shanye kafin zuwanmu duniya, bayan tazarar shuɗewar watanni tara mun rayuwa a cikinta cikin wahala da juriyar ciwo kala-kala, kafin girma da mallakar hankalin kanmu ta jure faɗi tashi na wahala damu tsayin shekaru ba tare da gajiya wa ba, a ganina idan har ba a kiramu da 'Yayan mace mun amsa ba da wane suna za a kiramu mu amsa? Saɓanin nawa sunan da ya dinga amsa kuwwa kafin ɓulluwar wannan, wato Shegiya ko 'Yar shege ba laifi don mutane sun rasa sunan da ya da ce su kira ni da shi duk da cewar ina da sunan yankan da aka ba ni kamar kowanne ɗa a duniya mene laifina don na rasa adon sunan Uba a gaban sunana kamar kowanne cikakken mutum na duniya? Mahaifiyata wacce ta durƙusa ta kawo ni duniya ba ta taɓa ba ni damar sanin ko ni wacece ba, a karan kaina ina tambayar wacece ni? Amsa ni baiwa ce.
19 parts