AN YI SAKE.. 12

19 1 0
                                    

  AN YI SAKE...
       12
Mallakin QURRATUL-AYN.
    NWA©

***
      "Mayar masa za mu yi Mama..! "
  "Wannan ba huruminki ba ne. "
Ta kai maganar tare da miƙewa tsaye ta kwashi sauran ledojin kayan, ta barmin ta maganin a gabana, sai bayan da ta kai daf da shiga ɗakinta sannan ta juyo gare ni da faɗin.
   "Ki tabbatar da cewar ya yi amfani da kuɗinsa a in da ya dace, ba a nan ba. "
   Daga haka ta juya tare da Shigewa turakarta ta barni nan zaune, ina saƙa da warwara na daga rayuwata.
   
Washe gari tun sassafe kafin mu fara shirin karyawa kamar yadda muka saba, Dillaliyar unguwarmu Jamila ta yi sallama, Mama ta karɓeta faram-faram, don ni sallamarta ce ma ta fito da ni daga ɗaki, saboda duk yau  banga alamun wasa a tare da Mama ba, shi ya sa na kame kaina, nan suka zauna tsakar gida bayan su gaisa na leƙo ni ma na gaishe ta, kafin na wuce domin ɗora mana abin kari kamar yadda Mama ta sanar da ni na dafa ruwan zafi, nan na fara kiciyar kunna wutar gawayen da muke girki da shi, a gefe guda na zuciyata cike nake da mamakin abin da ya kawo Jamila Dillaliya gidanmu abin da ban taɓa gani ba ke nan a tsayin rayuwata, sai dai na santa na san kamanninta fiye da yadda ta sanni.
   Mintuna kaɗan Mama ta fito daga ɗaki hannunta ɗauke da ledojin da Yaya Tarik ya kawomin jiya, a gaban Dillaliya ta ajiye su tana faɗin. 
   "Ga shi duba ki gani, duk da dai mun gama magana a waya. "
   Nan ta hau buɗewa tana kallon kayan tare da jinjina kai kafin ta kada baki wajen faɗin.
   "Wannan kaya haka Maman Zahar! Me zai hana ki barwa ɗiyarki ta yi amfani da su, ko banza za ta zame maki jari, domin ki buɗe ido da kyau ki kalli ɗiyar taki irin su ake yayi a wannan zamanin. "
  "Na fi ki sanin hakan Jamila, amma sai dai ni ba irin waɗannan iyayen ba ne, kin ga mu bar wannan maganar mu yi abin da ya kawo ki kawai. "
   Ƙasa-ƙasa suke maganar sai dai hakan bai hana majiyata zuƙomin sautinsu ba, domin ina da baiwar ji fiye da yadda mutum zai yi tunani, gajeren murmushi na yi a daidai lokacin da na kammala hura wutar na  ɗora tukunyar, sai dai duk irin gargadin da Mama ta yi wa Dillaliya hakan bai hana ta sake furta.
   "Cancaɗi wallahi kayan nan kamar don Zahar aka saye su, duka za su amshi jikinta sosai kuma....! "
   "Ba ni kayana na kai wani wajen. "
Maganar Mama ta katse batun da ta faro.
  "Ba a kai ga haka ba, ni gani na yi shawarace, amma Allah ya ba ki haƙuri ga kuɗinki. "
  Nan ta miƙawa Mama kuɗin da ta ciro da cikin 'yar ƙaramar jakarta da ake yi wa kirari da 'Yarlelen hammata, ta miƙa mata, kafin ta hau mayar da kayan tana ci gaba da faɗin.
   "Ƙirga ki gani don kin san yadda shari'ar kuɗi take. "
   Nan take Mama ta hau lissafin su bayan ta gama ta watsa su cikin lalitarta tana faɗin.
  "Sun cika kamar yadda muka yi magana, na gode sai wani lokacin. "
  Dillaliya ta miƙe da ɗaurin ledar a hannunta tana faɗin.
   "To Zahar sai anjimanku. "
"Mu jima da yawa, ba za ki tsaya ki sha shayin ba? "
  "A'a alhamdulillahi na gode kin ji 'yar albarka. "
Nan ta fi ce ta barni nan gaban murhun ruwan zafin ina ci gaba da hurawa.
   "Ko yanzu mutum ya samu ɗan hasafin kashe wasu buƙatun na sa. "
  Cewar Mama ke nan tana gyara zama kan tabarmar kafin akwalar wayarta ta hau kukan neman agaji, da sauri ta ɗauka tana daɗin.
   "Kira da safiyar Allah haka? Akwai labari ke nan? "
  "Me ya faru kuma? Har yanzu dai ba wani labari? Ni kuwa ina wannan almurar matar ta shi ni 'ya su?"
  Ta ɗan yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ɗora da faɗin.
   "A matuƙar tsorace nake wallahi Zaliha, ina cike da taraddadin lamarin nan, kada da komai ya kwaɓe mana daga ƙarshe."
   "A'a wallahi ai dole na samu kwarin gwiwa in dai har ina tare da ke, bari na fito yau da wuri zan biyo ta asibitin, sai mu yi magana gaba da gaba zamu fi fahimtar juna. "
   Tana kaiwa nan ta katse wayar tare da sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya mai sauti, a daidai lokacin da muka yi ido huɗu da ita ta watsomin harara da faɗin.
   "Wato kin kashe kunnuwa kina saurarona ko? "
Kai na girgiza ba tare da na tanka ba, take na ga Mama ta wuce ɗaki ta fito kanta sanye da hijabi tana faɗin.
   "Zan fita da wuri, ke ki zauna ki kula mana da gidan, saboda na yi wa Tarik alƙawarin barinki ki huta na kwana biyu, ki tabbata da kin rufe ƙofar ta ciki."
   "To Mama, amma ba za ki sha shayin ba? "
  "Na sha a can Zahar, sauri nake yi ne. "
Kafin na yi yunƙurin sake furta wata kalma ta yi waje da sauri.
   Nan na buga tagumi ina cike matuƙa da tarawa da ɗebewa a cikin rayuwata, wayar da Mama ta gama yi a yanzu ita tafi komai tasiri a cikin zuciyata fiye da cinikin kayan da ta yi, nan take ƙofofin tunanina suka hau buɗewa wasu da yawa na almarin Mama na yawo a kaina tamkar ina kallo a cikin talabijin, kafin amon maganganun Yaya Auduwa su fara zuba tamkar yayyafi a kwakwalwata, kai ka ce a lokacin ne yake yi mini bitarsu, har ban San lokacin da na miƙe tsaye ba, na kai na kawo tamkar mai safa da marwa, gumi ke yankomin ta kowacce kafa daga sassan jikina, kafin na nemi guri kan tabarma na maye gurbin inda Mama ta tashi na buga tagumi.
   "Me yake shirin faruwa da ni? "
"Ba na tunanin abin da zuciyata ke harƙillo a kai gaskiya ne, to amma me ya sa zuciyata ta aminta da batu masu yawa a kan hakan? "
  "Wacece ni? "
"Tabbas kamar yadda mutane da dama suke buƙatar sanin wannan amsar, ni ma nemanta nake yi ruwa a jallo, amma ta ya ya? A ina? Kuma yaushe ne zan samu wannan amsar? Haƙiƙa idan na ce rayuwa ba ta yi min adalci ba zan iyayin butulci, amma tabbas haka maganar take, sai dai na san cewa da yawa wani duhun na tafiya da ɓoyayyen haske a  bayansa, kamar yadda nake fata wata rana duhun rayuwata zai yaye, tabbas ina cike da Ƙumajin hakan a ƙasan raina, tabbas da buƙatar na yi tafiya da ƙafafuna domin haƙar ramin da ban san da shi ba, zan yi kasada kamar yadda zuciyata ta aminta, sai dai ina buƙatar madogara, waye shi ? Wa zai zame min madogarar tawa..?"
   Firgigit na dawo cikin hayyacina a daidai lokacin da na ji ƙarar shigowar mutum cikin gidanmu, domin ƙofar gidan ba mai sirri ba ce, bare ta sirrantawa mutum a lokacin da ya yi gigin shigowa.
   Sai dai me? Me zan gani? Wa nake gani? Saɓanin tunanin nawa, yauma shi ne ya zo kamar yadda ban yi zato ba, kuma hakan ko a cikin ƙoƙon kaina bai zo ba.
   Tsaye ya yi a kaina da wannan ɓoyayyen kwantaccen murmushin na shi kafin ya furta.
   "Surprise! Bazata!"
Murmushi na yi gajere, ina mai miƙewa daga kan tabarma kafin na ce.
"Sannu da zuwa bismillah zauna. "
Neman guri ya yi ya zauna, kamar yadda na ba shi umarni abin mamaki.
   "Ina kwana, ya aiki? "
Ya amsa a taƙaice kamar yadda na miƙa masa gaisuwar, shiru ya ratsa a tsakaninmu kafin ya katse shirun da faɗin.
   "Ya ƙafar taki?"
"Lafiya ƙalau, ga shi ka zo Mama yau ta fita da wuri. "
"Na san da hakan, kin kuwa gwada kayan da na kawo miki jiya. "
  Mummunar faɗuwar da ta kawomin ziyara a yayin da na ji ya ambaci kaya.
   'Ke nan na ce masa Mama ta siyar da kayan? Ina! Ba zan iya ba, hakan tamkar zubar da ƙima da darajar mahaifiyata ne, to me zan ce da shi?'
  "Kin yi shiru? Ko ba su burgeki ba ne? "
Murmushi na kalato da ƙyar na ɗora a saman fuskata kafin na ba shi amsa.
   "I na gwada, ɗauko maka zan yi? Sai dai Mama ta fita ban san in da ta ajiye su ba. "
"Karki damu da ma tunanina ko ba za su burgeki ba. "
"A'a wallahi sun yi kyau matuƙar gaske. "
Ina kallonsa ya murmusa, kamar yadda na sauke ajiyar zuciya a hankali, ina tunanin ta in da na samu kwarin gwiwar zayyano masa wannan ƙaryar mai lasi da na yi haka lokaci guda.
   "Na tambaye ki wani abu? "
Ya yi nasarar sake katse shirun namu, kai na gyaɗa ba tare da na iya furta masa da baki ba.
   "Amma kafin nan zan faɗa miki wani abu, ina so ki faɗamin iya naki hange da tunanin. "
"Ba matsala ina jinka. "
   "Ɗan jarida nake son zama. "
"Aunty Ummi ta faɗamin. "
Kai ya girgiza da murmushi kafin ya ce.
  "Ki saurare ni kawai, daga baya idan na gama kina da 'yancin faɗar abin da yake ranki. "
Ni ma na gyaɗa masa kai.
  "Wannna ra'ayina ne da kuma mafarkina a kullum, amma gidanmu musamman Abbana burinsa kawai na yi aiki a ƙarƙashinsa musamman Companynsa, sai dai ba ni da ra'ayin hakan ko kaɗan ba kuma na jin sha'awar hakan. "
Ajiyar zuciya na yi kafin na ce.
  "To me kake so na ce? Ai ra'ayinka ne, kuma naga kai kake da 'yancin zaɓar abin da kake so. "
"Duk da haka ki misalta abin a kanki, idan ke ce ya za ki yi? "
Shiru na yi tsayin daƙiƙu kafin na yi ajiyar zuciya na ɗora da faɗin.
   "A ra'ayina idan kuma ni ce zan yi abin da mahaifin nawa yake so ne. "
"Me ya sa. "
"Saboda dalilai da da ma, biyayya ga iyaye ba ƙaramar riba da tasiri ne ga 'ya'ya ba, tun da suka iya shanye wahalar raino ci da sha da sutura ba su gaza ba har izuwa girmanka, a nawa ganin ba kada wani abin da za ka saka musu da shi wanda ya wuce bin umarninsu, domin ta haka ne kawai za ka iya samun dacewa da ci gaban kanka a rayuwa. "
  Koda na kawo nan na yi shiru, kamar yadda shi ma ya yi shiru ya zuba min ido tamkar wata abin kallo, can ya yi ajiyar zuciya mai sauti kafin ya furta.
  "Kin yi gaskiya kuma maganarki na kan hanya, hangenki abin duba ne ga kowa, tabbas ina ji a raina karon farko a rayuwata zan yi abin da zuciyata ba ta yi na'am da shi. "
"Kamar ya ke nan? "
Na jefa masa tambaya.
"Manta kawai, sai tambayarki da na ce zan yi, mene ne gaskiya a kan jita-jitan da yake yawo a cikin unguwar nan taku, bayan Mamanki ta ce mahaifinki ya rasu ne? "
   Take na ji wani mulmulen abu ya tokare ni tsakanin wuya da bakina, yawuna ya yi kauri tamkar na kurɓi ruwan ganda, harshena na ji ya ɗaure tare da yin nauyi tamkar wacce kunawa ta harba, a gefe guda kuma na ji hadarin idaniyata na haɗowa da niyar zubar ruwan hawaye a kowanne lokaci.
   Da ƙyar na yi ta maza wajen ƙoƙarin daidaita nutsuwata don ganin bai fahimci wani canjin yanayi a tare da ni ba, sai dai me? Sautin ƙarar turo ƙofar gidanmu da kunnuwana suka zuƙomin shi ya ƙara dugunzuma hankalina matuƙa, take na ji numfashina na barazanar ɗauke wa lokaci guda, domin tuni magijin kwakwalwata ya fara hasasomin irin tsatstsauran hukuncin da zan girba da hannuna a yau, idan har ta yi tozali da abin da ta gama koramin gargaɗi a kansa daren jiya zaune dirshen a gabana, muna musayar kalamai, me zai faru?

AN YI SAKE..

  

AN YI SAKEWhere stories live. Discover now