KUSANCINMU 19

23 1 0
                                    

✨   *KUSANCINMU*   ✨

   ~Na Fateeey Tambary~✨
     {The lazy writer✍🏽}

    Allah makes up for your difficulties with blessings. You just have to open your eyes enough to see what they are...!

    *Page 19* ✨

  Ta gefen firdausi bayan fitar sa wata iren dariya tayi, tabbas taga weak point dinshi, ta Ƙuɗura a rai sai ya zame mallakin ta...

  Ashe dawowanshi ma mutanen gidansa basu san da zuwan sa ba, sai da dare tukun yaje ya gaida iyayensa, shi kam baban ma iren sauye sauyen Noor yake ta mamaki, amma ya bar hakan a rayuwar sa sai ya samu hujjojin da zaiyi amfani da su bayan ya gama nazartarsa...

  Bayan sun gama gaisawa da baban ne, ya tafi wajen mamansu, baiwar Allah nan ta rufe ido, abinka da tunani iren namu na mata, nan inda take shiga ba ta nan take fita ba, ta nuna masa lallai sai ya sake aure tunda ni na kasa haihuwa, wanda a zahiri ni lafiya ta qalau amma sonkai iren na iyayenmu mata duk ta ɗora min laifin duka, shi kam ma kasa ce mata uffan yayi, saida ta gama sannan ya tashi ya fice abinsa, dama iren matsalolin nan ne da suƙa kunno kai shiyasa ya shafawa kansa lafiya da son zuwa gida yanzu, shi kam bai shirya haihuwa ba shiyasa ma ya daina shiga sabgogina ashe ya tsiri wasu muna nan halayyarsa...!

  Nikam ma Allah ya cire min shi kab a rai, hidimar gabana ce ta sha min kai, ga shi mun kusa fara final year exams, ga project nan ya taso ni gaba kuma so nake na kammala kafin exams dinmu, shiyasa ban damu da lamurransa ba Sam, haka Shima so yake ya gama da matsalar firdausi data mamanshi, sai na samu lafiya..!
   Har yayi zaman dai zaiyi ya koma wurin aiken sa bamu da lokacin junanmu, sai ma sako na tarar, bawan Allah nan zaman sa Kaduna ya bashi freedom sosai, ya taka macce ko wace iri ce, kai su ma suke kawo kansa gareshi, a can ne ya samu wata da ta liƙe mashi kamar firdausi wai kuma ita sai ya aure ta fa, mutumin nan ya rasa ya zaiyi da ita, shi kansa yasan karyanshi ya ce ma mahaifinshi yana son sake aure, yasan yayi karya kuwa...
   Kuma a hakan wayar firdausi bata yankewa, duk tayi sha'awar kasancewa dashi to sai kawai ganin ta zaiyi, da abin ya ishe shi ya zauna da ita, yace" firdausi ko ce maki nayi zan aureki to tabbas kin san yaudara ta shigo ciki, dan Allah ki shafawa kanki lafia dani kaina mu yanke alaka, tabbas zamu rabu kuma muna kusa da yi, kar kiyi tunanin zaki iya daukar mataki kamar yanda kika fara zuwa gidana, mahaifina akan matata baya da sauki, aminci me girma ne tsakanin mahaifinta da nawa, ko mahaifiya ta bata isa ba, sannan kin dai san ba tsarar aure na ce ke ba haka kuma wannan shashancin da muke dole watarana mu daina shi ko da son rai ko babu son rai, ina rokon ki dan Allah mu rabu da juna mana.. "

Vote
Comment
Share

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 21, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KUSANCINMU Where stories live. Discover now