KUSANCINMU 04

64 4 0
                                    

✨   *KUSANCINMU*   ✨

   ~Na Fateeey Tambary~✨
     {The lazy writer✍🏽}    

    

          "There is no compulsion of religion. Verily, the right path has become distinct from the wrong path. Whoever disbelieves in 'Taghut' and believes in God, then he has grasped the most trustworthy handhold, that will never break. And God is All-hearer, All knower."
(Q2:256)..!

    ~Comments dinku shi zai sa yawan adadin post kan lokaci, shirunku zai iya sa na zama relax da typing, bunch of love..~

        *PAGE 04*  ✨

     Yana office yana aiki duk tunani ya adaddabeshi ya kasa tab'uka komai, Ya rasa menene firdausi ke bashi a drink dan hankalinsa ya gushe a duk lokacin da zai dawo gidansa, gashi salma yanzu wani raini ne ya qulla alaka tsakaninshi da ita.

  Sai karfe hudu na kare lecture, ina karewa gidanmu na nufa kasancewar na kwana biyu banje ba, na tarar da kowa a gidan gwanin ban sha'awa har 'ya' yan anty asma'u, sosai mun shagala ana ta fira har ban san lokaci ya ja haka ba sai da naji mama tana salati ta na fad'in '' salma me kikeyi a gidan da baki wuce gida haka bane, iyyeh'' cunno baki nayi ina kai mama daga mutum yazo sai ayi ta korashi kamar ba' a sonsa kuma, rike baki tayi tare da  cewa ungo naki nan, ey ba'a sonki ne shiyasa aka kora ki din, Allah ya kaddari babanki ya sameki a gidan ya miki tas, ja'ira
Kawai...

  Da gunguni na, na fara shirin tafiya ciken ban so ba kannena na min dariya wai ta kwab'e mana ni da mama, kyalesu nayi na wuce abina...

  A bakin gate naci karo da babanmu mu ka gaisa, yace '' a'ah kakata yaushe aka zo mana ne? ", murmushi nayi nace wuraren biyar na shigo baba, dan yau na fita makaranta ne, murmushinsu na manya yayi sannan yace Allah ya taimaka kakata a cigaba da hakuri kinji, komai a rayuwar bawa jarabawa ce kuma idan akayi hakuri sai aci riba kinji, Allah yayi maki Albarka kuma in da matsala karki ji nauyin gayamin because I'm your best friend kinji salma, murmushi nayi nace toh babanmu Allah ya kara tsawon rai ya bada lafiya da arziki mai amfani,da amin ya amsa ya zaro kudi a aljuhunsa yace na rike sai ya min aike, godia na masa sosai sannan na shiga motata na wuce gida...

  Kwance na isko shi ciken gida, mamaki kamar ya kasheni dan bazan iya ce muku ga iya adadin rabon da ya dawo gida time din ba, har na manta kuwa.

  Sharesa nayi na shiga daki na nayi wanka nasa light abu a jikina kasancewar garinmu garin zafi ne, kitchen na nufa domin na girka wani abu mai sauki ince, ina tsaka da aiki sai na tsinkayo muryarsa yana cewa "daga gidan ubanwa kike"?.

  Juyowa kadan nayi nace daga gidan ubanda ka aikeni nake, murguda masa baki nayi na cigaba da aiki na...

  Tsawon minti biyu yayi yana nazarina sannan yace '' keh dan ubanki naga raini ya shiga tsakaninmu koh, toh bari kiji zan lallatsa ki ne son raina ba mai rama miki ko waye ubanki wallahi...

  Juyowa nayi na kalle shi, shi kansa ya tsorata da kallonda nake masa amma ya dake kasancewar namiji ne, dakata malam idan kana iskancin ka daina sako mahaifina dan naga alamun kai baka san dararjar masu dararja ba, baka san dararjar alkhairi ba, baka san dararjar maida alkhairi da alkhairi ba sai akasin haka, ka kiyayeni noorudeen kuwa shiru shiru na kar ka dauka wai kyaleka nakeyi ina tsoronka ne a'ah ina kyaleka ne saboda nasan kaina amma ka ci gaba da kaini zaka gane through colour dina ne kuwa...

  Iyyeh yarinya kinyi bakin da zaki ta sani a gaba kina fada min magana fah, bravo yarinya zaki san kina sa in sa da noorudeen kuwa, yana gama fadar haka ya wuce....

     
   _share_
  _Your comment determine how to make post_

KUSANCINMU Where stories live. Discover now