KUSANCINMU 12

46 1 0
                                    

✨   *KUSANCINMU*   ✨

   ~Na Fateeey Tambary~✨
     {The lazy writer✍🏽}

    
_"Oppression will be a darkness on the Day of Resurrection." - Prophet Muhammad_
  

  ~Comments dinku shi zai sa yawan adadin post kan lokaci, shirunku zai iya sa na zama relax da typing. Bunch of love..~

        *PAGE 12*  ✨

    Ciro wayar yayi ya ƙarasa bakin motar ya bude tare da receiving call ɗin ta tare da cewa "Hajia masu duniya an ganki an barki an buga dake an barki, kina lokacin ki ya hajjajunah..."

  Murmushi tayi iren na tattatun ƴan duniya sannan tace "Honeyboy kana sha'aninka fah, ka gujeni haka ma ka ƙi ni dai honey boy,ba waya balle nasa ran in ganka gidana dai.."

  Murmushi noorudeen yayi sannan yace "hajia kenan, ai kece sai da wuta, idan kika sa mutum a gaba ya boni da kanshi sai ya nemi mararraba dake akan...

  Bai ƙarasa ba ta katse shi da cewa kai din ne zuma ga zaki ga harbi, nidai ba ma wannan ba yaushe zan sa ran ganin ka a gidana ne?, ina kewarka sosai plz kar kace min bazaka zo ba...

  " Nawa gidan sai nayi yaya dashi hajjaju, saninki ne sarai komai dare sai na kwana ciken iyalina.."

Dariyar rainin hankali tayi mishi sannan tace maida wukarka mana ni bance kazo ka kwantar mini gida ka bar naka gidan ba kaji, ina dubinka da sauraren ka...

  Bata tsaya sauraren mai zaice ba ta katse wayarta, shima kwafa yayi yace aiken banza wama zai sake bata lokacinsa kanki ga kananun yara sai ka zaɓa ma balle ke da kika kora ai yaci ace bariki ma ta juya maki baya by now..!

  Kunna motarsa yayi sai gidansa, mamakin duniya ya kama ni yau noorudeen ne da wuri haka a gida yaushe rabo ni ai nama manta saboda bazan iya cewa when last ba...

  Kwafa yayi yace lafia kin wani tsare ni da ido sai kace kinga sabon abu ne?

Shu'umin murmushi nayi nace abinda mutum bayayi ai dole a cika da al'ajabi da mamaki kuma a wani fannin ba abin mamaki bane mutum shi da gidansa..!

  Ina kaiwa nan nayi murmushi na tashi shima murmushin gefen baki yayi wanda shi ƙadai yasan ma'anar sa....!

 

   _share_
  _Your comment determine how to make post..._

KUSANCINMU Where stories live. Discover now