1

13 3 0
                                    

*SUN YI MIN ILLAH*


        *SUMMY M NA'IGE*

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


     *SHAFI NA ƊAYA*

Da ma ashe haka duniya take mai halin ɗan mangwaro? Me na yi musu ko sun manta kowa da ƙaddararsa a tsarkakken allo. Ban san inda zan saka raina na ji sanyi ba. Ya zan yi na sauya ƙaddarata ko zan kasance yar adam kamar kowa lallai sun yi mini babbar illa wadda har duniya ta naɗe ba zan daina cin gajiyar raɗaɗin ƙonar zuci ba.

Cikin sauri ta shiga gidan, bayan matar gidan ta karɓa mata sallama sannan ta fito. Gani ta da ta yi ne lokaci ɗaya ta ɓata fuska haɗi da jefa mata  tambaya, "me ya kawo ki gidana?"

Ƙasa ta yi da kanta sai da ta yi raurau da ido kamar mai koyon magana ta ce,

"Daman na zo ne ko akwai aikatau?"

Kallon ta ta yi a walaƙance  sannan ta ya tsuna fuska ta ce,

"Za ki iya wankau na yara kala naire goma!? idan ba za ki iya ba bi ta inda ki ka fito.
Ta faɗi haka haɗi da nuna mata ƙofar fita da yatsa.

Kanta ta yi ƙasa da shi, haɗi da tunanin baya, gashi baya bata dawo wa bare ta yi ƙoƙarin gyara kaddarata, dama duniya haka take me halin ɗan magoro, yaranta da ta tura makaranta ta tuna da su, kuma gashi sun tafi makaranta ba abin da suka ci, sanin suna kan hanyarsu ta dawo wa ne ya sa ta ɗago  kanta cikin hanzari ta ce,

" Zan iya Hajiya".

Tsaki wannan matar ta yi sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko kayan yara masu muguwar dauɗa, kamar waɗanda aka yi wasan tsere da su.

Haka ta duƙa ta fara wankau har sai da hannuta ya ji ciwo, sosai ta sha wuya kafin ta kammala, tana idarwa ta gayawa matar, dubu ɗaya ta ɗauko ta bata, ta ce,

" Ƙuɗinki ɗari uku ne, ki cire kuɗinki ki kawo min sauran canji".

Sai da ta rusunan kamar maroƙi ya je bara sannan ta karɓa haɗi da yi mata godiya. Cikin hanzari ta nufi mai shago, garin kwaki ta sayo iya na kuɗinta sannan ta shiga ta bawa Hajiya canjinta, gab da za ta fito gidan ƙofar gidan ta riƙe ledar garin ya zube ƙasa gaba ɗaya. Lokacin da idonta suka sauka kan abin da ya same ta ba ta san lokacin da hawaye suka sauka a idonta ba, zazzaɓin da take ji ne tun safe ya sake rufeta, da ƙar ta iya tashi ta koma gida cikin tashin hankali. yaran ta tuna me za su ci idan sun dawo? Musamman Afiyya da bata da haƙuri, sosai ta san Afiyya ba ta da hakuri, don  halinsu ya babbanta da na Husnah, kamar yadda sararin samaniya ya yi hannun riga da ƙasa, to haka ta san halin su ya babbanta. duk da wannan halin da take ciki ta yi alƙawarin ba za ta nemi taimakon kowa ba, bale har a koma yi mata lllah.

Tana cikin wannan halin ta ji sallamarsu, cikin hanzari ta  miƙe da ga kwanciyar da ta yi haɗi da goge hawayen da ke mata kwaranya.

" Ammi! Ammi! Ina abincinmu yunwa nake ji ?"
Abin da ta ji Afiyya na faɗa kenan tun kafin ta ƙaraso cikin ɗakin da take.

Cikin ƙarfin hali ta tashi haɗi da faɗar,

" Kun dawo?"

Husnah ta ce,

"Mun dawo Ammi".

Tun kafin Afiyya ta sake buɗa baki ta yi magana Ammi ta ɗau mayafinta ta ce, "zan je na karɓo muku abinci, kar ku fita  kun ji".

Haka ta faɗa  jikinta sai rawar zazzaɓi yake  kamar wadda ta ji tashin gangar makiɗi. Tun kafin su yi magana ta fice gidan, ko da ta fita ta jima tsaye ta rasa ina zata dosa, wa zai taimaka mata ya kawo mata a gaji, duk da ita aka yi wa illah amma  kowa ya gojeta, ko sana'a ta kasa ba mai saye ina zata sa kanta ta ji daɗi. Tafiya take tana tunani har ta kusa fita unguwarsu, a haka aka fara kiran sallah magarb waje ta samu ta rakuɓe ko zata samu ta gabatar da sallah.

SUN YI MIN ILLAHWhere stories live. Discover now