2

12 2 0
                                    

*SUN YI MIN ILLAH*

   
  
    *RUBUTA LABARI:-*
       *_SUMMY M NA'IGE_*

*SADAUKARWA:-*
*RAHAMA SABO USUMAN*
          _(Abar ƙaunata😘)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*



      *SHAFI NA 2*

Cikin hanzari ta isa wajen da ake parking ɗin mota motarta ta buɗe ta shiga, sai wani zarar ido take kamar an kama ɓarawo a gidan biki. Cikin mutuwar jiki ta kunna motar, da mugun gudu ta ja motar kamar wadda za ta je wasan tsere.

Gudu take kan titi hankalinta bai jikinta, wani gumi ke zubar mata kamar wadda ta yi wanka jego. Iya ruɗu ta shige shi, sautin muryar Ammi ke mata amo a dodon kunne, a haka har ta isa titin unguwarsu, gab da za ta shiga kwanar gidansu sai ta ji ta bige wani abu da ƙarfi, idonta ne suka sauka kan wata rantsattsiyar mota sabuwa dal, irin ɓarnar da ta yi wa motar ne ya sa ta dawo duniyar tunanin da ta tafi.
Hannu ta ɗaura saman sitarin motar haɗi da faɗar, " Yau naga ta kaina".

Gabanta sai dukan uku-uku yake, hawayen idonta sun ƙafe, tsananen baƙin ciki ya hana ma hawayen sauka, kallo ɗaya zaka yi mata kasan tashin hankali ya zarar da ita kamar mage ta kama ɓera.

Hayaniyar mutanin unguwarsu ne ya ƙara tayar mata da wani tashin hankalin da take hango ina ma a ce za ta mutu yanzu. Wallahi kar ka haƙura don yarinyar nan bata da mutunci ko kaɗan ba ta san girmma muta ne ba sai masifar girman kai, kullum haka take gudu kan wannan titi kamar jami'in tsaro ya biyo ɗan maye. Haka kunneta ya ji mata abin da ƴan unguwarsu ke faɗa.

Saitin zuciyarta ta dafe dake mata falfalniya kamar za ta  fito waje.

Duk inda ranshi ya kai ya ɓaci, ayi masa ɓarna amma dan rainin hankali har an ɗau lokutta ba a zo bashi haƙuri ba! Wani mutum ne mai sun barin numfashi cikin ƙanƙanin lokaci, lalle ko wanene ya ɗauko ruwan dafa kansa.

Irin yadda mutanen unguwarsu ke masa magana ne ya sa ya fito don ya ga wani ɗan girman kai ne, don wallah ko wane raƙumi ne  bai isa ya ja da kura ba. Ba abin da ba su ce da shi ba don kar ya barta, shi ma a yanzu ranshi ya yi mugun ɓace.

Gabanta ne ya yi muguwar faɗuwa lokacin da ta ɗago kai idonta suka sauka kan mamalakin wannan motar, kallon da ta yi masa kaɗai ta gane cewa shi ɗan masu yatsu da yawa ne. Motarshi ta sake kai duba gare ta, ta san ko ana muzuru ana shahu ba za ta iya sayin motar ba, amma ta fauwalawa Allah komai, duk hukunci da ya ga ya dace da ita zai iya yi mata shi. Ta na cikin wannan tunanin ta ji wani kamshi turare mai sanyaya ruhi ya ziyarci ƙofofin hancinta, "Ya Allah".

Ita ce kalmar da ta fito bakinta ".

Bata kula da shi ba idonta na rufe sai tunanin ƙurar da ta tunkaro ta take, ina za ta sa kanta, lallah ya yi mata illah da har mutuwarta ba za ta daina jin raɗaɗin ƙonar zuci ba. Mutsin da ta ji ne yasa ta buɗe idonta haɗi da dawo wa duniyar tunanin da ta tafi.  Rau-rau ta yi masa da ido lokacin da suka yi ido huɗu da shi mamalakin motar da ta yi ma ɓar na, sai a lokacin ta ji saukar hawaye a idonta, kanta ta yi ƙasa da shi don ba ta san mi zata ce da shi ba, a  halin yanzu ko baki bazata iya buɗewa ta yi magana ba, da zaran ta yi yunƙurin buɗa baki ta yi magana sai ta ji kamar ta amayo zuciyarta saboda ɗacin rai da tashin hankali.

Sosai jikinshi ya yi sanyi lokacin da suka yi ido huɗu da ita, saboda tsaf ya hango damuwa da gagarumin tashin hankali a ƙwayar idonta, haka kawai sai ya ji ta bashi tausayi. Motar ta ya duba ya ga ko ita duk ta samu rauni a motar,  don haka bai ce komai ba ya ɗau waya ya ƙira. Ba ta ji abin da ya ce ba sai sunan unguwar da ya faɗa, aikuwa ƴan unguwar na ji ya faɗi sunan unguwar suka fara murna don sun haƙiƙance cewa jami'in tsaro ne ya kira. Ko ita da ta ji haka ta saduda Jami'an tsaro ne ya kira.

SUN YI MIN ILLAHWhere stories live. Discover now