4

6 1 0
                                    

*SUN YI MIN ILLAH*




*RUBUTA LABARI:-*
     *_SUMMY M NA'IGE_*

  *SADAUKARWA:-*
*RAHAMA SABO USUMAN*
     _(Abar ƙaunta😘)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO..*


       *SHAFI NA 4*



Nurse Ruƙayya na isa office ta kira Dr Rahama a waya. Tashin ta kenan daga bacci, don yau ta makara sosai, saboda ko sallah sai da rana ta fito ta yi, kuma har yanzu idonta taf yake ɗauke da bacci kamar wadda ta sha kayan maye. rurar da wayar take yi ne ya tashe ta, ganin sunan nurse Ruƙayya ne ya sa ta ɗauka cikin hanzari haɗi da karawa kunnenta. Bayan sun gama gaisawa ne  Ruƙayya ke cewa da ita,

"Yau fa zan kai Ammi gida, saboda yanzu ta samu lafiya sosai".

Hamdala ta yi ma Allah haɗi da sauke sassanyar ajiyar zuciya ta ce,

"To Ruƙayya nagode sosai, bani wasu ƴan daƙiƙu yanzu zan ƙaraso cikin asibiti".

" Ina jiranka".
Abin da Ruƙayya ta faɗa kenan a taƙaice.

A gorgoje ta tashi tashiga banɗaki ruwa ta watsawa jikinta sannan ta fito, man shafawa kawai ta shafa sannan ta shirya ta fito. Part ɗin iyayenta ta nufa, zaune ta same Mumy ta tana kalaci, bayan sun gaisa ne ta ke gaya mata inda zata tafi, kallonta ta yi tsaf sannan ta buɗa baki ta ce,

" Na fa gaji da ganinki haka Rahama, kin ce sai kin kammala karatu, to karatu ya ƙare gashi har kin fara aiki, muddin kina son na ci gaba da jin daɗi to ki sani sai ranar da naga kin yi aure, halin da na ke ciki aurenki kaɗai nake son na gani".

"In sha Allahu Mumy zaki gani, fatana dai ki ci gaba da yi min addu'a".
Ta faɗi haka haɗi da tashi ta fice daga falon.

"Shekaran jiya bakin yi baƙo ba? Ko shima kin koreshi?".

Haka maganar ta faɗo mata a kunne daidai lokacin da ta sanya ƙofarta ƙofar fita daga falon.

   Batare da ta juyu ba ta ce,

,"A'a Mumy,  idan na dawo za muyi magana".

Da ido Mumy ta rakata har ta ɓacewa ganinta, ita bata taɓa ganin yarinyar da bata son ko ayi mata maganar aure ba kamar Rahama, ita dai ta na roƙon Allah ya kawo mata agaji acikin lamarin yarinyar.

  Kai tsaye motarta ta shiga ta fice, a hankali ta ke tafiya har ta fice titin unguwarsu tun ranar da ta ji abin da suke cewa take ƙafa-kafa da su.

    Wai yarinyar can ba ƴar maye ba ce".
Cewar wani saurayi da ganinshi kallo ɗaya zaka yi masa ka gane cewa shi ɗan ruwa ne.

" Malamar asibiti ce kar ka yi mata sharri".

"  To tana min kama da wata shugaban masu safarar kayan harka".

Sun faɗi haka daidai lokacin da motarta ta bar titin unguwar. Bata tsaya ko ina ba sai asibiti, ko gaisuwar da ma'akata ke mata bata wani tsaya karɓawa ba saboda Ruƙayya da ke jiranta, ko da ta isa office ɗinsu ta na shirin fita, bayan sun gaisa ne ta ce,

"Ga kayan sawarsu can na zo da su, ki zo na saka miki cikin mota har ma da abin cin su".
Ta kai ƙarshin maganar haɗi da buɗe zip ɗin jikarata, kuɗi ta ɗauko aƙalla za su kai dubu ɗari ta ce,

"Ki haɗa musu da wannan su yi anfani da su zuwa wani lokaci".

Da kallo Ruƙayya ta bi ta, don ita ta san halin Rahama, ba kowa take kulawa ba bare har ta san matsalarsa, amma duba waɗan nan mutane tun zuwan su komai ita ce. "Miye alaƙarki da su?"
Abin da Ruƙayya ta ce da ita idonta cikin nata.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 28, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SUN YI MIN ILLAHWhere stories live. Discover now