𝒇𝒂𝒏𝒔 𝒑𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆

27 3 0
                                    


__𝑨𝑫𝑬𝑬𝑴𝑨__
(𝒓𝒂𝒓𝒆)

_𝒘𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒏 𝒃𝒚 𝒎𝒆𝒆𝒆𝒓𝒂𝒓𝒉_

___نصر من الله و فتح قريب___

GOMBE STATE...

♡REMEMBER INTERNATIONAL ACADEMY ♡

tafiya sukeyi hannun namijin a cikin na macen, macen zatayi kimanin shekaru bakwai, shi kuwa namiji zaiyi sha biyu, gani d'aya zaka musu ka hango matsananciyar shak'uwa dake tsakaninsu, sosai yaran suke da abun Burgewa.

Tsananin kyauwon yaran yasa duk inda suka bi sai an samu wanda yayi musu magana, su kuwa ko kallonsu basayi saboda tsananin tsoron mutane da sukeyi.

Kaf cikin makarantar da sister d'insa mai suna JANNAH kawai yake abota, wacce ta kasance kamar wani b'ari na jiki , zuciya da rayuwar sa.

Ako da yaushe itace karfin guiwarsa, duk da kasancewar su yara, amma idan suna wani abun zaka zaci manya ne.

Sun fito k'ofan gate kenan wani class mate d'insa yayi masa magana, da yake suna d'an mutunci dashi hakan yasa ya tsaya .

Ita kuwa Jannah da batasan ya tsaya ba ta cigaba da tafiya, k'iiiii , mota ya tsaya a gaban ta.

Sosai ta firgita babu shiri ta kwatsa wata iriyar k'arar da yasa ABEER juyowa, ganin an bud'e motan ana shirin Jan ta ciki yasa shi nufosu a gigice.

Jannah, Jannah, Jannahhhhh, haka yaita k'walla kirar sunanta, amma kash lokaci ya riga da ya k'ure mishi.

Koda ya k'araso sun ja motar sun tafi da ita, haka yaita bin motar yana kirar sunanta yana kuka.

Sunyi nisa sosai kawai yaga an jefo da ita daga cikin motar, pass, haka wata motar ta hau kanta ta taka ta.

Cak ya tsaya kaman wani gunki yana kallon yanda motar da wuce tare da Jannah dake kwance sam bazaka ce mutum ne aka taka ba, saboda yanda namar ta yayi rugu rugu.

Suuuuu, haka ya fad'i k'asa a sume, mutanen da suka ga abunda ya faru tun a k'ofar makaranta, haka suka biyo bayansu.

Suna k'araso wa da shi suka fara cin karo, wasu daga cikin su ne suka hangi Jannah a inda mota ya takata.

Sosai hankalin mutanen gurin suka ya tashi , saboda kap d'insu babu wanda ya saba ganin irin wannan bala'i haka.

After some formalities da aka cika agurin police aka kwashe gawar da ba'a ma gane fuskan aka wuce gida dashi da Abeer.

Bayan anyi mata sallah da komai aka kaita makwancinta, har lokacin Abeer bai farfad'o saga suman da yayi ba.

Bayan da ya tashi kuwa sosai abun da yake yi ya bawa iyayensa tsoro da tausayi.

Da zarar yaga wani a inda yake zai fara fad'in, "Jannah na , daman nasan ba abun da ya sameki, kiyi hak'uri na kasa tsayar da wad'ancan mugayen, ai zan rama miki idan nayi kud'i, duk sai nasa ka an d'auresu", yana magana yana kuka da dariya a lokaci d'aya.

Shekaru da dama bayan faruwar haka dakyar aka samu ya dawo dai dai, cause kad'an ya rage mental disorder yayi masa muguwar kamu.

15 YEARS LATER

ABUJA NIGERIA

"Haba mana Abeer wai sai yaushe ne zaka dawo hankalin ka, this girl is already dead, you've witnessed that ".

Shi kuwa Abeer da yake zaune a driver sit ya karkata kansa tare da dubanta.

"Hey girl, fuck of from this car, small bitch", kallon sa tayi hawaye na kwaranya a idanuwan ta, she is tired, shekaru biyar tana bibiyar sa, amma nuna yakeyi kaman bai san da ita ba, gaskiya is high time da ta rabu da rayuwar sa, zuciyar ta na cutuwa.

Bud'e motan tayi tare da ficewa bata k'ara waiwayarsa ba, shi kuwa ko'a kwalar rigar sa, haba yarinya yabi ta ishe sa.

Sai da yayi mintuna sannan kuma yanayin sa ya sauya , farar fuskar sa tayi jazur, hawaye zur suka zubo daga cikin idanuwan sa.

Shekaru 15, shekaru sha biyar da suka wuce sun kasance masa munanan shekaru, gaba d'aya tsayin wannan lokacin yayi shi ne da guilty conscience na cewar shi ne sanadiyyar da ya rasa ta.

Shine dalilin dayasa bata tare da shi, a ransa yana jin kaman har yanzu Jannan as na raye.

Kullum idan ya kwanta sai yayi mafarkin ta, tama ce masa, "Abeer, zan dawo gare ka".

Sosai wannan mafarkin yake k'ara masa k'arfin guiwar ci gaba da rayuwa, da ita ne kawai rayuwarsa take tafiyar masa dai dai.

Idan babu tunanin ta a ransa da a yanzu ya dad'e da barin wannan duniyar da bata da komai sai Memories na bak'in ciki.

InshaAllah yayi wa kansa da soyayyar da alk'awarin zai nemo ta, kuma zasu ci gaba da rayuwar sa da ita kaman baya.

Hawayen fuskansa ya goge yace," muddin rai, muddin mutuwa, muddin duniya, muddin lakhira, zan kasance dake Jannah na, da kina tare da mi bansan bak'in ciki ba, amma da kika barni, har yau ban k'ara farin ciki ba, kina ina ne Jannah?".

GOMBE NIGERIA

Kyakkyawar dattijuwar mata ce zaune a saman bed ta d'aura kywawan idanuwan ta akan beautiful girl d'in dake kwance a saman bed, tana barci hankali kwance.

Yarinyar zata kai kimanin shekaru sha bakwai, kyakkyawa ce musamman ma da take barci .

Gashin kanta duk ya barbazu ya hau mata akan fuska, bayan wani lokaci zufa sosai ya karye mata.

Nan take fuskanta ya jik'e, can ya fara magana k'asa k'asa tana hawaye.

Abeer, abunda ta fad'a kenan bayan ta tashi daga barcin hankali a tashe, da sauri maman ta ta matso tare da rungume ta.

Wannan kaman wani abu ne data saba dashi ko wace safiya dole ne ta kasance da ita.

Ita har tau ta kasa gane meke faruwa da yarinyar ta da take matuk'ar so da k'auna kaman ranta.

Bayan wani lokaci da tayi rungume da ita , sosai natsuwa ya zowa yarinyar, fuskanta ta kalla tace.

"Its fine Jannah , everything will be fine", kaallon ta Jannah tayi da idanuwan ta da sukayi jajur tana sauke hawaye masu matuk'ar sanyi.

Mamma , sai yaushe zan ga Abeer d'ina, wallahi Mamma shid'in rayuwa ta ne, Mamma a sanda muke yara , shine yake bani abinci a baki, yayi mun wanka, wanki na ma baya bari wani yayi , shi yake yimun, Mamma he really loves me ".

Numfashi Mamma ta sauke tace,"Allah shine yasan abun da yake nufi daya raba ku, kuma idan har yaso zaku k'ara had'uwa da juna , ki kwantar da hankalin ki.

BA ZAKU SO A BARKU A BAYA BA, ADEEMA ONE OF BEST PAID BOOKS.

500 NAIRA ONLY

NOTE : EDITED

THANKS YOU MEEERARH

𝐴𝐷𝐸𝐸𝑀𝐴(𝑟𝑎𝑟𝑒)Where stories live. Discover now