𝒇𝒂𝒏𝒔 𝒑𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓

7 1 0
                                    

_𝑨𝑫𝑬𝑬𝑴𝑨__
(𝒓𝒂𝒓𝒆)

_𝒘𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒏 𝒃𝒚 𝒎𝒆𝒆𝒆𝒓𝒂𝒓𝒉_

_ 𝒇𝒂𝒏𝒔  𝒑𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_

_ 𝒑𝒂𝒊𝒅 𝒃𝒐𝒐𝒌_

___نصر من الله  و فتح قريب___

Suna zaune a gurin both thinking of what to do next,  suka ji an banko k'ofa da matsanancin k'arfi.

"O my God",  Abeer ya faďa ganin Fattoush tsaye a k'ofa hawaye na rolling akan beautiful face ďinta.

Shifa duk da bayya sonta amma bayya son ganin kukanta cause ai ko babu komai ta nuna mishi so da tsantsar k'auna.

Nan take Jannah taji zuciyar ta na dukan tara tara, Dan sosai ta tsorata da yanayin da taga Fattoush.

Suna a gurin ta k'araso ta samesu, batayi wata wata ba ta lafkawa Jannah wani mahaukacin Marin da ya saka ta kwatsa k'ara da k'arfin gaske.

Tun da take a rayuwar ta ba'a tab'a dukan ta ba, amma wannan yarinyan tana da guts ďin saka hannu fa mare ta.

Tashi tsaye tayi Abeer yayi saurin rik'eta yana faďin ,"sorry Jannah ", murmushi tayi tace " babu komai fa maybe nayi Mata laifi bari naje",  "Office dinki shine wancan dayake cikin Office ďina, k'ofa kawai ta rabamu".

Ya fad'a yana murmushi mai tsananin kyau, Wanda yasa Fattoush ta k'ara rikice wa ta nufi Jannah a harzuk'e.

Hannu Jannah ta saka a kafaďanta ta tura ta baya tace, "easy girl, zan iya yi miki dukan mutuwa idan kika sake hannun ki ya k'ara tab'ani".

Baki sake Fattoush take kallon Jannah, wannan yarinyan iya kacin ta 17 or 18yrs , amma tana da bakin yi  mata rashin kunya .

Kallon Abeer tayi da zimman ko zai ďauki mataki, amma sai taga ya zauna a seat ďinsa yana harkokinsa kaman bakisan da zamansu ba.

Itama Jannah tuni ta shige cikin Office ďinta da yake ďauke da kayan more rayuwa so casual ba irin na k'yalk'yalinnan ba.

Zama tayi a seat ďin ta wanda ajiye wani golden platter an rubuta sunanta da manyan bak'i.

"JANNAH  RAHEEM FATAH "

Ta faďa tana sake murmushi, sai can kuma ta ďaure fuska tunowa da Fattoush dake tsaye a Office ďin Abeer.

Juyo wa tayi, aikuwa ta hangeta ta glass tana nan tsaye har yanzu, buďan bakin ta tace," mayyar banza kawai, ba'a sonta amma sai ta lik'e".

Dariya ta kumayi tace, "ji ni kaman nasan abun da yake tsakanin su", tashi tayi ta fito ta nufi Fattoush a harzuk'e.

Tana k'araso wa hannun ta taja tare da nufan k'ofan Office ďinta da ita, shi dai Abeer kallon ikon Allah kawai yakeyi.

Yarinyar nan babu abun da ya raba ta da Jannahn shi a gurin halaye.

Bayan sun shiga Office ďinta , zaunar da ita Jannah tayi tare da durk'usa wa a gabanta ta fara magana.

"Am sorry akan abun da ya faru, duk da ke kika fara Jan maganan, amma don't worry,  na yafe ki, abun da zan fa'da miki abu biyu ne, na farko kar kisaka wani abun a ranki dan kin ganni tare da Mr Abeer,  he is just my superior,  na biyu kuma, kar ki sake kishi ya miki illa, sabo da da alamu kina da zafin kishi".

Tana faďin haka ta mik'e ta koma seat ďin ta ta fara duba files dake gurin.

Ita kuwa Fattoush,  mamaki ne ya bala'in kama ta, this small girl dare to tell her what to do.

Amma kuma data ce babu komai a tsakanin ta da Abeer sosai taji dad'i,a ranta tace , zanyi maganin ki k'aramar 'yar iska , a fili kuwa ta juya ta kalli Jannah tace.

"Bitch,  zan yi maganin ki, dani dake mu zuba mu gani", har ta juya zata tafi ta juyo ta kuma ďauke Jannah da mari.

Duk da Jannah ta ji zafi amma sai ta b'oye jin zafin tayi murmushi tace, " ranar da zan rama zata zo karki damu,".

Murmushi Fattoush tayi tace, "k'aramar marar kunya,  ai na zaci rama wa zakiyi , wallahi yau da se kin nunamun ubanki a k'asarnan".

Kallonta Jannah tayi cike da jin zafin maganar, haka dai ta k'ak'alo murmushi ta tashi ta k'araso gaban ta.

Hannunta taja in cautions, ta jata da k'arfin gaske ta fice daga Office ďinta,  da sauri Abeer ya tashi ya nufo su da zummar raba Hannun ta dana Fattoush.

Jaye ta bayan ta tayi tare da k'ara sauri sabo da bata so Abeer ya shiga tsakani , taga alaman matar batta da mutunci.

Wajen Office ďin ta jefa ta tare da rufe k'ofar ta rufe saboda batta ma son Abeer ya fita.

Yana kawowa k'ofar ta duk'ar da kanta tace, "Dan Allah Mr Abeer kayi hak'uri,  ka bari ta girbi abun da ta shuka".

"Koda ka fita ka rarrashe ta baza ta bar abun da take yi ba, na tsani mutum wanda bai san dara jar iyaye ba".

Numfashi ya sauke tare da Jan hannun ta suka nufi Office ďinta da shi, a haka suka k'ara sa ranar babu wanda yayi wa wani magana .

Ita kuwa Fattoush tayi awanni a k'ofa zaune ko zai fito, amma kuma sai taga sab'anin haka.

Haka ta tashi jiki a mace hawaye na kwaranya a idanuwan ta ta fice daga companyn gaba d'aya.

Bayan an tashi daga Office dakyar Jannah ta yarda Abeer ya kai ta gida, ya matsa akan shi zai kaita.

A hanya hannun cikin hannu suke zaune a cikin motar, he just can't help, but to hold her hands.

Itama ta kasa hanashi wani kalan deep affection take ji a jikin ta a game dashi,
Ita fa bata k'i su dawwama a haka ba.

Amma idan ta tuna cewa shi mai gidan ta ne sai taji dan nauyi, amma still she rather be with him always.

Ganin ya dauki hanyan Asokoro dake cikin garin Abuja ta juyo ta kalleshi fuskan ta da alamun tambaya.

Am taking you home, to see my parents,  nan take taji zuciyar ta ya buga, not knowing what to do ta sauke ajiyan zuciya.

Murmushi yayi ya ci gaba da driving  , a bakin wani Bungalow white house mai girman gaske yayi horn.

Bayan an bude gate ya tambayi mai gadi if his parents are around, colin girmamawa mai gadin yace ,"basu daďe da fita ba, sun tafi Gombe saboda wani abu ya taso a can family house ďinsu".

Cikin mamaki Abeer yace "ok", sannan ya k'arasa ciki gidan, nan take zuciyar Jannah ya buga da k'arfi.

Tunda ance mishi basanan ba sai ya mai da ita gida ba, or is he planning something .

Da sauri tace no no babu abun da yake planning,  maybe he just want to show her around.

500 NAIRA ONLY

#MEEERARH

𝐴𝐷𝐸𝐸𝑀𝐴(𝑟𝑎𝑟𝑒)Where stories live. Discover now