chapter 2

33 1 2
                                    

*_A ZATO NA_*🧏🏻‍♀️
 
 
 
 

 
✍🏼✍🏼✍🏼 By *Zainab yerima* AKA *_ZEETY_*
 

_MARUBUCIYAR_
●ANEESATY
●HASKEN RAYUWA TA
●BAZAN BUTULCE BAH
●ACIKIN RAYUWA
●MURADIN RAI  

 
 
 
wattpad @Zeety-AZ
 
 
 
 
_Wannan littafin sadaukarwa ne ga *Fatima kole* maman Iman the owner of SKOLE collection_
 
 
 
 
 
*for advert contact 08080691306*
 
 
 
 
*2*


Yadda Ahmad ya ɗau wanka bazaka taɓa cewa tela bane, gashi dama fari ne sol kuma kyakkyawa ga iya kwalisa idan yashiga kaya ko dan gomna ne akace ma zaka yadda,haka ya shiga wajen yana dan bata rai kamar wanda hasken rana yayiwa yawa a ido, a asalin wayan shi tecno me torch yaciro yakirata, tana dauka daga dayan bangaren tace sorry gani nan daf da wajen…

huh toh shikenan idan kin shigo ki duba ta hannu daman ki zaki ganni…

da sauri ya maida wannan wayan aljihu, ciro wata scraf din iPhone 12 da akasawa case ya rike a hannu shi…

Bawani gaye me tsanani tayi ba, irin turkey gown din nan tasa da gyale akan ta sai babban sunshade a idon ta, fara ce sosai wanda daka ganta kasan tana cikin hutu… siririya ce amma tanada shape, dan duddubawa tafarayi ta ina zataga Ahmad…shi kuwa tun shigowan ta yaganeta amma tuni yayi mutuwar zaune don ko kadan bai dauka takai haka haduwa ba, tana juyowa gefen shi, ya daga mata hannu, karisowa tayi tareda murmushi a dauke a fuskar ta…

Tashi yayi yace mata barka da zuwa sayyada sarauniyyar yan mata, murmushin ta tafadada sannan tace godiya nake yarima na…

Aranshi yake cewa gaskiya wannan karon yayi babban kamu saboda daga ganta kasan yar masu kudi ce, wannan karon yasamu matar aure bazai bari ta subuce mishi ba…

Bai ankara ba yajita tana cewa tunanin me kakeyi haka? Lumshe ido yayi ya bude sannan yace kyakkyawar halitar kice ta susutar dani…

Waiter ne yazo yace meza a kawo muku?

Ita tafara cewa Chapman kawai takeso…

Ahmad kuma yace duk abunda ta zaba nima shi za’a kawomin…

hira suke taɓawa sosai taji ya kwanta mata arai duk da yau suka fara haɗuwa ba taki ace acikin satin nan a ɗaura musu aure ba, Ahmad baisakejin ya ruɗe ba saida yaji tana waya da babanta yaji suna UK wai sunje hutu, kuma dama wani abokinshi yagaya mishi babanta yana daga cikin masu kuɗin garin.

koda suka gama sam tahana shi biyan kudin acewar ta wai ai wannan haduwan natane don haka ita zata biya kudin komai, yadan ja kadan saboda kartayi tunanin bashida kudi ta raina shi, amma data dage sai kawai yabar mata....

bai kara susucewa saida yaga motan da yazo daukan ta a karo na biyu kuma firgita yayi daganin sojojine bodyguard dinta...

juyowa tayi takaleshi tace in raka ka wajen motan ka inga tafiyan ka tukunna... a dan dibibice yace a ah no baza ayi haka aini yakamata inga tafiyan ki don haka muje, nuna mata hanya yayi da hannun shi...

bata musa mishi ba illa tayi gaba yabita, har jikin motan yakaita soja ya bude mata tashiga...

Ahmad ya tsorita sosai amma a zahiri bazaka gane hakan ba... kallon  ta yayi ido cikin ido yace ki kulamin da kanki please murmushi ta mishi tace you too...

**Tunda fati ta koma gida babu abunda takeyi sai sakawa da warwarewa, kwance take akan maceccen katifan ta, juyawa tayi tace gaskiya fahad ya hadu, ga kyau ga gaye ga nutsuwa uwa uba ga kudi wani ihu tasa tareda tashi ta zauna.

inna ce ta leko tace ihun meye kuma kike mana a gida, yanzu ke fati shikenan kin fitsare kafan ki, shikenan kin daina daga ko cokali a gida nan saidai kawai kiyi wanka kifita a dafa kici… gunguni tafara tanacewa ni wlh inna badama kuganni ina zaune duk sai a faramin gorin aiki baga bilkisu kullum tana wanke wanke da shara ba…. inna wallahi idan ina aiki hannu na kai harma da jikina zai nuna wahala duk wanda yaganni zai gane ni yar talakawa ce kuma kinga hakan zaisa inrasa cika buri na, inna idan fa na auri mekudi Allah har kuma zaku huta kinga gidan nan rushewa zanyi in gina miki gidan sama in zuba miki ma'aikata...

katseta inna tayi ta hanyar cewa dalla rufemin baki bakida aiki sai dogon buri, fatima fa kifa kiyayi kanki kibi duniya a sannu.....



*Oumm Ameen*💞
 

A ZATO NAWhere stories live. Discover now