chapter 8

15 0 0
                                    

*_A ZATO NA_*🧏🏻‍♀️
 
 
 
 
 
 
✍🏼✍🏼✍🏼 By *Zainab yerima* AKA *_ZEETY_*
 
 
 
_MARUBUCIYAR_
●ANEESATY
●HASKEN RAYUWA TA
●BAZAN BUTULCE BAH
●ACIKIN RAYUWA
●MURADIN RAI  
 
 
 
 
 
wattpad @Zeety-AZ
 
 
 
 
_Wannan littafin sadaukarwa ne ga *Fatima kole* maman Iman the owner of SKOLE collection_
 
 
 
 
 
*for advert contact 08080691306*
 
 
 
 
*8*


Shago ya shigo yana yan wake waken shi….. 5k ya direwa abokin aikinshi a gaban keken shi tareda cewa malam haruna gashi kaima ka d'ana arzikin masu arziki…

'Dagawa haruna yayi yana cewa ban gane ba?

Zuwa yayi ya zauna akan kujeran d'inkin shi, ya d'aga kafa sama sannan ya bushe da dariya… yace bakai kullum kana dauka na mahaukaci ba…. Muna nan dakai wataran zakaga yadda zan fantama in auri yar masu arziki…

Kaidai yanzu kadafe wannan, inaji ajikina fa na kusa arziki…

Haruna soke kud'inshi yayi a aljihu yace toh Allah ya tabbatar da alkhairi…


**Zama tayi a d'akinta tanata kallon wayan ta…. Murmushi tayi tace ashe dama zan mallaki ire iren wayannan nan kusa, ikon Allah dama fa haka Allah yake ikon shi, nikaina nasan inada kashin arziki, yanzu dai bari inkaiwa Aziza karamin wayana ko zata samu na rage zafi, tashi tayi ta d'auki jalbab d'inta tasa. Ba laifi fati tanasa kaya masu kyau saboda duk abunda tacewa ya yunus tanaso yana kokarin saya mata badon komai ba sai don karta na sa’ido a abun mutane…

Inna tasamu a d'aki tace mata inna zanje gidan su Aziza zan bata karamin waya na…

.
Kallon ta kawai inna tayi tace toh kina bata kidawo karki dad'e, tace toh ta fita…

Majalisan samarin anguwan su suna hango ta kowa yayi shuru, ba karamin burge yan anguwan su takeyi ba saidai babu wanda ya isa yazo wajenta, saboda duk masu ji da kansu a anguwan sunzo ta koresu, wasuma kamar ta musu duka tsabar bakin ciki….

Tace ai haife ta a anguwan ta tashi tareda su cikin talauci sannan suce suna sonta, in banda hassada irin na dan Adam so sukeyi ta mutu a geto area ita sam bazata iya soyayya da yan anguwan su ba, yaran da ba arabi ba boko karshe in sun tashi aure a basu ciki da falo a gidan gado, ina ita bada ita za’ayi wannan abun bauch.
Tana wucesu wani a wajen yace billahillazi yarinyan nan girman kanta yayi yawa ita babu wanda ya isa ta gaishe shi a anguwan nan saboda tana ganin ta girma ko?

'Daya daga cikin su yace, kaga laifin tane? Ai kune da laifi, ku kuka dinga bibiyan ta dayan bayan daya wannan yaje wancan yaje ba dole ta raina ku ba, kuma ni tamin daidai saboda da dama batayi kallan geto ba…. To da kaketa wani goya mata baya basai kaje kai ka gwada sa’ar ka ba….

A ahh ni wa? Aini dama nasan tafi karfina shiyasa ma banje ba, kuma tana birgeni na tabbata idan naje takini nima haushinta zan faraji kamar yadda kukeyi kuma ni banason inji haushinta inason inci gaba dayi mata fatan alheri… haka dai sukayi tayi duk wanda ya kusheta ta ya tareshi.
Tana shiga gidan gidan su Aziza bayan ta gaida maman Aziza dakin Aziza tawuce tana shiga ta cila mata wayan ta tsoho tana juya ido tace gashi kema kici arziki…

Tashi Aziza tayi tana washe baki tace aikuwa nagode… kinga dama inada sim sakawa kawai zanyi…

Ai kuwa gwara kisa ko zaki fara daraja a idon samari, nifa Aziza bansan ko rubutun farin jini zan fara karbo miki a wajen malami me tsangayar anguwan nan, ace wai ko irin gajojin anguwan nan babu Wanda ya taba tayaki saikace ansa miki hannu…

Murmushi Aziza tayi tace karki damu kawata lokaci ne idan lokaci yayi dole miji na zaizo..
Tabe baki fati tayi tace toh ai saikiyita zaman jiran lokaci…
Yauwa dan Allah fati inason baki shawara, nifa inaga Fahad din nan kamar dagaske yake sonki, mezai hana ki janye kudurinki na mishi karya ki nuna mishi asalin gidan ku…
Bude baki fati tayi sannan tace lallai Aziza kinfara haukacewa, toh ke angaya miki dayaga lungu shiga gidan mu kadai da tuni ya gudu, ai yanzu anashi tunanin ni yar gidan Alhaji isa ne, kuma idan ma dagaske yakeson aure na wallahi ingaya miki bazai taba sanin gidan mu ba sai ya aureni….
 
Yana shiga gidan su da babban ledan shinkafa tun daga nesa mamansu take washe baki kasa hakuri tayi ya kariso daga nesa tafara cewa a a ahh mesunan Alhaji, yau samuwa mukayi haka? Kodai kabi layin da ake raba zakka ne…. dan bata rai yayi sannan yace shikenan mama nibazan iya samo abu dakaina ba harsai anbani zakka wannan ai saikisa amin dariya idan aka jiki….
Kara washe baki tayi tana cewa nan ma kuma hakane wallahi kafini gaskiya, nikaina nasan na haifi yaro me zafin nema wanda nasan wataran zaiyi arzikin dazai ciremin takaici… yace inshaa Allah mama, kedai kiyita addu’a kawai.
Indai addu’a ne karka damu dama ina maka kuma zan kara kaimi sosai yanzu, kodon makiya ma da yan sa’ido.
Yau dai ba fati ba hatta kanwar bilki takasa bacci tsabar zumudin waya…. Fati tagama seta komai na wayan, har sha dayan dare suka kai fati nadanna waya bilki na kallo, fahad ne ya kirata ta dauka suka gaisa sai kuma kowa yayi shuru…. Ba karamin nutsuwa take nunawa fahad ba…
Gyaran murya yayi sannan yace ranki ya dade nawa zabiya in samu zazzakan muryar ki a daren yau kafun inyi bacci…
Dariya tayi wadda har sautin shi ya fito sannan tace ai bazaka iya biyan  kudin murya na ba, saidai kawai in ma alfarma ….
Hakan ma godiya nakeyi gimbiya…
Nifa kaga, kadaina min abu kamar wacce tafito a fada…
To aini a wajena kinfi wanda yafito a fada….
Haka dai sukayita tadinsu me kama dana soyayya, daga karshe yace mata yanason su hadu gobe, amma dan Allah tayi kokari karta karya mishi alkawari.
Bayan Ahmad ya gama seta wayanshi, credit din dubu biyar yasa, saboda wannan karon shi yakeson yakira sayyada su jima suna waya….
Komai na wayan burgeshi yakeyi, murmushi yakeyi shi kadai, yace ashe dai waya me tsada laushi da santsin screen dinta ma daban yake….
WhatsApp yashiga don ya nemo sayyada yamata magana itama yau taganshi a WhatsApp…..
Amma abun haushin shine, yana hawa wasu tsofin yanmatan shi har sun ganshi online sun fara turo mishi message, tsaki yayi yace gaskiya yanzu ajina yawuce naku don haka dukan ku tosheku zanyi wallahi, waiku suna yaran masu kudi amma bakuda aiki saidai jiran ni in kiraku ko kuma in tura muky credit, inaaa bazaiyu ba nadaina irin wannan soyayyan…..
Bayan yagama toshesu fitama yayi a WhatsApp din yayi dialing number sayyada… suna kallon film tareda Abida, tana ganin wayanshi tashi tayi ta zauna tana murmushi…. Har zata dauka Abida ta tare gaban wayan… kallon ta tayi tace what… matsowa Abida tayi tace mata dan Allah yau kam ki gayyato mana shi gida muganshi…
Hararan ta sayyada tayi, a hankali Abida tace mata please sister….
Saura kadan ya yanke tadauka, hira suka dan taba sannan daga karshe tace mishi, sweetheart idan bazaka damu ba inason kazo gidan mu, kaga baka taba zuwa ba, kuma sisters dina ma nason ganin ka…
Take yaji kanshi yashi wani rudu, hello tace saboda taji yayi shuru ta dauka ma wayan yanke ne… dan seta kanshi yayi sannan yace anything for my princess… murmushin jindadi tayi sannan tace mishi zan turama address din ta WhatsApp, alright yace…
Har zai kashe tace wait, baka gayamin yaushe zakazo ba?
Ki zaba duk ranan kikeso….
Umh, gobe
Gobe? Ya maimaita a dan zabure
Yes morrow, kasan nayi missing din ka sosai nima inason ganin ka…. Sosa kan shi yakeyi yana tunanin yadda za’ayi ya shirya komai har yaje gidan su sayyada ba a samu matsala ba…. Cikin tausassar murya yace mata toh shikenan Allah yakaimu….
 

 



*Oumm Ameen*💞

A ZATO NADonde viven las historias. Descúbrelo ahora