chapter 3

25 2 0
                                    

*_A ZATO NA_*🧏🏻‍♀️
 
 
 
 
 
 
✍🏼✍🏼✍🏼 By *Zainab yerima* AKA *_ZEETY_*
 
 
 
_MARUBUCIYAR_
●ANEESATY
●HASKEN RAYUWA TA
●BAZAN BUTULCE BAH
●ACIKIN RAYUWA
●MURADIN RAI  
 
 
 
 
 
wattpad @Zeety-AZ
 
 
 
 
_Wannan littafin sadaukarwa ne ga *Fatima kole* maman Iman the owner of SKOLE collection_
 
 
 
 
 
*for advert contact 08080691306*
 
 
 
 
*3*




Tura baki tayi tana cewa inna kullum saina miki bayani amma kin kasa ganewa …

Mtsww inna tace tareda tafiya tabar fati tanata surutan ta.

wayan tane yafara ringing da sauri ta duba wata yarinyan dasuka taba haduwa a wajen biki itace take kiran ta, dan tsaki tayi saboda ita fati a duk shirmen ta batada tara kawaye yanzu danasani bata namber tayi, amma take wani abu ya fado mata ko ba komai meena zata mata amfani saboda yanzu gaskiya tanason tana samun kaya masu tsada saboda itama tana fantamawa.

dauka tayi daga dayan bangaren taji anacewa da fati gayu nake magana?

Wani far da idon ta tayi taji dadi sosai wato har yaran masu kudi ma sunsan ta iya gaye…

Ya akayi ne hajiya meena?

Wallahi biki muke dashi shine nace bari in gayyace ki sannan idan kina free zan kawo miki anko har gida….

Dasauri fati tace no karki damu basai kin kawo ba, kiban address din ki anjima kadan zanzo inkarba, au namanta ban tambayeki nawa ne kudin ba…

Murmushi meena tayi tace chill babe haba ke ai kawata ce kyauta zanbaki…. Wanni farin ciki ne ya lullube fati don ko bakomai tasan masu tsada ne.

Suna kashe wayan meena ta tafa hannu da daya kawarta da take gefe takejin duk abunda sukeyi, meena tace gaskiya wannan fatin dole tabi tafiyan mu kodon qualities din da mukeso atattare da ita, kinga nafarko tanada kyau don fati wanke hannu ka taba ne, tanada kyau na gaske me daukan hankali, fara ce me matsakaicin tsayi, gata da manyan idanu dimple dinta kuwa ko magana takeyi suna lotsawa….

Zamu shigo da ita gari kodon muma musamu babban rabo me tsoka…

**Tunda sayyada ta koma gida kai tsaye dakinta ta wuce tana shiga tafada kan gado ta lumshe ido sanyi AC na ratsa ta, tabbas badon Ahmad ba babu abunda zai fitar da ita waje a wannan ranan, wayanta ta zaro ta shiga gallery hoton Ahmad ta lalubo ta zubawa ido, babu abunda takeyi sai aikin murmushi…. A fili tace gaskiya wannan gayen ya hadu ya gama tafiya da imani na, ita kanta tana mamakin yadda tafada soyayyan Ahmad rana tsaka… tuno ranan dasuka fara magana a IG tayi…

***Wani rana yanata hidimar duba yanmatan dasuke tashe a social media a wayan abokin shi Ammar, kawai yaci karo da ita… profile dinta yafara dubawa yaga tanada over 1million followers sannan komeye tayi posting over 500k suke liking… duk da haka kuma bata cika posting hoton ta don kwata kwata pictures dinta a wajen basufi 4 ba… amma kana ganin ta kasan ta kure wajen haduwa da class tanada kyau na gaske kuma cikin hotunan datasa nata duka babu wanda tayi makeup…

Fara dudduba abubuwan ta yayi ko zai gane yar wayece amma baiga komai da zai nuna ita din wayece ba sunan ta yagani “ sayyada Salim” sai dan rubutun kasan datasa
Allah first❤️
family over everything💞
unique and simple👑
.
Har gumi yake hadawa saboda yamatsu yagane wani abu akanta kafun ya mata magana…

Ammar ne yace mishi yadai malam kagama cin lokacin ka fa zanyi amfani da wayana…

Dan Allah minti daya Abokina yanzu zan baka… a gaggauce ya tura mata sallama…

Saboda yadda take samun DM shiyasa data gani ko bin takan shi batayi ba….

Saida yamata magana sau biyar nan ma profile dinshi tafara zuwa….

Inkaga Ahmad a social media zakace dan hamshakin me kudi ne, sannan kuma celebrity yanada followers sunkai 500k kuma baya hoto sai ajikin gida mekyau ko wajen shakatawa mekyau kuma yana iya aron kaya takanas don yayi hoton daurawa a social media.
 

Meena sun tura mata address, tasamu gidan su ba tareda wani shan wahala ba…. Tundaga waje take santin kyau da girman gidan amma data shiga matsewa tayi don karsuga kauyancin ta…

Da fara’a sosai meena ta karbeta suka wuce da ita dakinsu…. Bayan ankawo mata abubuwan motsa baki meena taciro mata ankon kala hudu lace guda biyu da atamfa da material dukansu babu nakasa da 20k, zama tayi a gefenta tace ga ankon ki naso inbaiwa tela na ya dinka miki saidai kuma bansan measurement dinki ba, amma yanzu zamu fita tare sai mukai mishi…

dan murmushin yake fati tayi tace no karki damu hakan ma nagode…

murmushi meena tayi tace a ah kedai zamuje ya iya dinki sosai nasan zakiji dadin dinkin shi sannan ni zan biya miki kudin dinkin…

Thank God fati tace aranta don dama abunda dayasa taki batada kudin dinki ne irinsu telolin su tsada ne dasu, ita kuwa yanzu saitaje ta roki yayan ta kudin dinki, kaman daga sama taji meena tana cewa bani wayanki insa miki number danake WhatsApp dashi, dan daburcewa tayi sannan seta kanta tace babban wayana yabaci yanagun gyara…

Haba babbar yarinya dake kina kai gyaran waya, gaskiya bazaiyu ba muje asama miki sabo kawai zaro ido fati tayi aranta tace lallai wayannan sunason hadani fada da Inna …... 



*Oumm Ameen*💞

A ZATO NAWhere stories live. Discover now