PAGE 1

26 8 2
                                    

🍁🍁🍁NAWWAL🍁🍁🍁

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU💞💞💞

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

BISMILLAHIN RAHMANIN RAHIM

PAGE 1

__________________________Wata matashiyar budurwa na hango mai kimanin shekara goma sha tara,sanye take da dogon riga na abaya kalan baki,tayi rolling kanta da dankwalin rigar,kafan ta sanye da wani bakin kanvas,kai da gani kasan takalmin ya ci kudi,hannun ta rike da makullin mota da waya kiran iPhone 13 tana daddannawa,bayan kaman second biyu ta kara wayan a kunne,ringing biyu kawai wayan yayi aka dauka daga dayan bangaren,"Sallama wata matashiyar budurwa mai kimanin shekara goma sha tara tayi",amsa sallaman dayar matashiyar budurwar mai suna Suhailat tayi tana yauki sannan tace"ki fito mu tafi",da toh dayar matashiyar budurwar mai suna Nawwal ta amsa,"kashe wayan Suhailat tayi bayan ta gama magana",fita tayi daga parlor ta nufi parking space,wani bakin EOD ta bude ta shiga,bayan ta gama warming  motan ta ja shi ta nufi gate,horn tayi mai gadi dake cikin dakin shi ya fito da sauri ya bude mata gate ta fice daga gidan,bayan kaman minti biyu tayi horn a kofan gidan su Nawwal,fitowa Nawwal tayi jikin ta sanye da dogon hijabi kalan ja,hijabin ya amshe ta sossai,dama gata farar mace,bude wurin mai zaman banza tayi ta shiga ta gaida Suhailat,"amsawa  Suhailat tayi a dakile ta dauke kai",murmushi kawai Nawwal tayi ta juya tana kallan hanyya,ko tari bai kara hada su ba har suka isa makaranta,Suhailat na gama parking ta kalli Nawwal da har ta bude kofa zata fita tace"kar ki bar ni ina jira idan an tashi,inko hakan ta faru tafiya zanyi na barki",murmushin ta mai kyau Nawwal tayi tace insha Allahu sis Suhailat,"dalla mata harara Suhailat tayi sannan ta dauke kai,kulle kofan Nawwal tayi ta nufi hanyyan department din su tana murmushi,domin inda sabo ta saba da halin Suhaila,ta rasa inda ta samo wannan halin,girgiza kai kawai tayi ta shige Dpt din su.

Sai da Suhailat ta shafe minti goma kafin ta fitar da kafan ta daya daga cikin motar,bayan minti biyu ta fitar da na biyun,gyara zama tayi ta daura kafa daya kan daya,tana lasa waya,daga kai tayi taga wani mota ya doso parking space,"zaro ido Suhailat tayi sakamakon gane mai motan da tayi,da sauri ta dau jakar ta ta kulle motan ta nufi department din su da sauri tana tafiya tana waigen shi,tana shiga hall shima ya shiga ya kulle kofan,ajiyar zuciya Suhailat ta sauke ta naimi kujera ta zauna.


Da misalin karfe Uku da rabi Suhailat ta fito daga hall fuskar ta a murtuke,hannun ta rike da goran ceway water,tana tafiya a hankali kaman bazata taka kasa ba,tsaye ta tadda Nawwal a jikin mota ta nade hannun ta a kirjin ta tana ta kalle-kalle,dannan car key Suhailat tayi tayi unlocking motan,bude driver seat tayi ta shiga,Nawwal ma ta bude bangaren mai zaman banza ta shiga ta zauna bayan ta gaishe da Suhailat,bayan kaman minti uku Suhailat tayi reverse suka bar haraban makarantar.......................................

By Gimbiya Ayshu💞💞💞.

🍁🍁🍁NAWWAL🍁🍁🍁Where stories live. Discover now