PAGE 2

20 7 2
                                    

🍁🍁🍁NAWWAL🍁🍁🍁

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU 💞💞💞

ELEGANT VERIFIED WRITER'S 📚

PAGE 2

__________________________Basu suka isa ba sai gabda la'asar,Suhailat na ajiye Nawwal aka kira sallah a masallacin dake da dan tazara da gidan su, knocking Nawwal tayi a bakin gate din su,bayan kaman minti biyu mai gadi yazo ya bude mata,gaishe shi tayi fuskan ta da alamun fara'a,da kulawa mai gadi ya amsa mata yana tanbayan ta ya makaranta,"da Alhmd Nawwal ta amsa ta nufi cikin gida",bude kofar parlor tayi ta shiga bakin ta dauke da sallama, shiru kake ji a parlor babu kowa,direct up stairs Nawwal ta nufa,bata zarce ko ina ba sai dakin Mummy,sallama tayi a bakin kofar, Mummy da fitowan ta kenan daga bayi ta amsa mata tare da bata izinin shiga,"tura kofan Nawwal tayi tana ya mutsa fuska,gaida Mummy tayi ta naimi gefen gado ta zauna tare da jingina bayan ta"murmushi Mummy tayi tace kin gaji kohhh!Habibty,"daga kai Nawwal tayi tana shagwabe fuska",dan dariya Mummy tayi tace Allah ya shirye ki da san jiki wlh,Ni dai tashi kije kiyi wanka,zakiji karfin jikin ki,kuma kinga an kira sallah,maza kije kiyi sai kizo kici abinci kinji,yau favourite dinki na dafa"tashi Nawwal tayi da sauri kamar wata karamar yarinya tana tsalle tace yeeeeehhhhhhh!Mummy na shiyasa nake sanki kaman kinsan ko shi nake marmarin ci yanzu",dariya Mummy tayi tace i nasan abinda Habibty na tafiso,kinga ko dole na miki,ke dai je ki shirya lokacin sallah na tafiya,"da toh Mummy Nawwal ta amsa ta nufi dakin ta da sauri"dariya Mummy tayi tace Allah ya shirye ki Nawwal,zanga ranar da zakiyi hankali,ta karasa maganar ta da murmushi a fuskar ta tana girgiza kai.



Horn ta danna da karfi,da sauri mai gadi ya tashi ya bude mata gate,cilla anchin motan tayi ta naimi wuri tayi parking,jakar ta ta dauka sannan wayoyin ta da handout dinta ta fito daga motar ta kulle,har tayi taku uku kafin ta mika hannun ta ta baya ta danna makullin motar inda motar ta shiga key,danna kararrawar kofan parlor tayi,bayan kaman minti biyu mai aikin su ta karasa da sauri har tana tuntube,dan tasan ba mai wannan aikin face Suhailat,dan kaf gidan ita ke irin wannan salon,aiko tana buɗe kofan Suhailat ta rufe ta da masifa,har da zagi,uffan mai aikin bata furta ba,dan idan ta kuskura tayi magana toh ta siya ruwan dafa kanta.

Upstairs Suhailat ta nufa ta shige dakin ta,tana shiga ta ajiye kayan hannun ta a bed side drawer sannan ta yaye gyalen kanta ta linke,drawer ta nufa ta dau sabon towel,kayan jikin ta ta cire sannan ta daura towel,kayan data cire ta kwashe ta zuba su cikin basket din kayan datti,bayi ta shiga ta haɗa ruwan sanyi da ruwan zafi,bayan kaman minti goma ta gama wanka ta dauro alwala sannan ta fito daga bayin,direct dressing mirror ta nufa taja kujera ta zauna, lotion dinta ta dauko ta fara shafawa bayan ta kammala ta dau tulare tabi jikin ta da shi,tashi tayi ta nufi jikin drawer ta,gefen inda take ajiye kananan kaya ta bude ta dau bom-short da wani harmless singlet dukkan su fari kal-kal,kulle bangaren tayi ta bude inda take ajiye dogayan riguna ready maid,wani jan dogon riga ta dauka ta ajiye kan gado saman bom-short din data ajiye,gefen inners ta nufa ta dau jan bra da pent Shima kalan ja,kulle drawer tayi sannan ta shirya cikin kayan,bayan ta gama shiri ta bude bangaren hijabi ta dau wani jan hijabi dogo har kasa,kulle drawer tayi ta dau darduman dake bed side ta shinfida,saka hijabin tayi sannan ta tada sallah,bayan minti biyar ta idar,bayan ta gama Addu'a ta mike ta linke hijabin tare da darduman ta ajiye su kan bed side,dankwalin rigar ta daura ta dau babban wayan ta ta fice daga dakin ta nufi na Mum,bayan tayi knocking aka bata izinin shiga,tura kofan tayi ta shiga,iske Mun tayi akan darduma tana lazimi,gaida ita tayi,daga mata kai kawai Mun tayi ta cigaba da abinda take, Suhailat na ganin haka ta daura kafa daya kan daya ta kunna data ta bude tik tok........................................

Kuyi hakuri da wannan bani da lokaci  ne Amman insha Allahau zan riga squeezing nayi posting.

Ina qaunar ku maso yana tare da muku fatan Alkairi.

By Gimbiya Ayshu 💞💞💞.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 26, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

🍁🍁🍁NAWWAL🍁🍁🍁Where stories live. Discover now