Tea mai kauri suka hada mata tasha sannan ta koma kwana. Washegari kuwa koda ta tashi umma da habiba kawai ta gani a dakin.
================
Wayar dake kan center table din palorn tafara ringing. Mika hannu akayi aka daga. Matar akalla zatayi shekara sittin fara tas da ita tayi picking call din.
Hello Sa'adatu? Ina wuni? Lafiya kalau.
Shiru tayi chan tace eh. Innalillahi to shine baki fada ba? Wlh ba komai Sa'adatu. Tana a wacce assibiti ne? To shikenan sai munzo ki gaisheta.
============•••••••••••••••••
Ana karasa la'asar baba ya shigo dakin yace sannu Fatima ya jikin?
Murmushi tayi tace naji sauki baba. Kallan Rukayya dake cin abinci baba yayi yace to Ke Rukayya ya yarki taci abincin ne?
Aa baba cewa tayi batajin yunwa. Wannan ma daka gani ita aka debowa taki taci shine nakeci a madadin ta.
Gaba yasata yasa Rukayya ta debo abinci yasata chin shi. Tana cin abincin akayi knocking hadeda sallama.
Saida suka amsa sannan aka shigo. Murmushi Rukayya tayi ta rungume matar tace mommy Ina wuni?
Sakeni babu wani rungumeni da zakiyi. Saketa tayi tace haba mommy yanzu so kike a ganmu a rana?
Eh a ganmu din mommy ta fada tana zaunawa kan couch dinda ke kallan gadon marar lafiya.
Daga kan gadon Fatima tace mommy Ina wuni?
Kallanta mommy tayi taga kanta a kasa yake tace sannu uwar noke noke hadda bakida lafiyar ba zaki bari aga fuskar taki ba?
Alhaji Yusuf ina wuni?
Juyawa abba yayi yace dama jira nayi ku gama dramar ku keda yarki mu gaisa ya gida? Ya yaran? Fatan duk kuna nan lafiya?
Lafiya kalau wlh.
To Masha Allah yace yana daukar jug ya zuba ruwa ya mikawa Fatima yace sha. Sha tayi kamin ya ajiye kofin yace koke fa?
Karna kara jin ance kici abinci kince bakya jin yunwa so kike ulcer ta kama min ke?
Mikewa yayi yace aa latifa da Aisha tare ake daku?
Murmushi kyakyawan yan matan sukayi.
Rukayya tace baba tun shigowar su suke faman gaisheka Amma bakaji ba kana chan kana fama da anti taci abinci.
Toh nakoyi babban laifi ban gaisa da ya'yana ba. Kuyi hakuri yafada yanasa hannu aljihu. Kudi ya fitar yan naira dubu dubu sabbi dal ya mikawa wacce nake sa ran itace latifa yace gashi ki siya chewing gum.
Girgiza kai tayi tace aa baba munyi girma da amsar kudin iyayen mu. Abba ai da wannan girman namu idan bamu baku ba aiko bazamu amshe naku ba.
Murmushi yayi amshi nan kinji idan na kara tsufa kya mayar min. Amsa tayi sanin halin abba tace to abba Ina godiya.
Hannu ya sake sawa a aljihu ya ciro wasu yace mamana ga naki kema. Amsa aisha tayi tace na gode abba.
Sallama sukayi da mommy sannan ya wuce. Yana fita mommy ta kalla Fatima tace har yanzu wannan halin naki yana nan ba?
Murmushi Fatima tayi tace aa mommy ba haka bane. Mommy kiyi mata fada wai ita a dole sai first class.
Wallahi mommy lokacin datake project saiki tsaya kanta ki shekara hamsin kina magana bama jinki zatayi ba Rukayya tafada cikeda haushi.
Murmushi mommy tayi tace hakane fatin baba? Rufe fuska tayi tace mommy fita batun rukayya kinsan sanyi yafara shigowa.
Dariya suka saki gaba dayansu a dakin banda rukayya datace anti nice mahaukaciya? Shigowar umma da habiba tasa firar katsewa.
Aisha dake kusada kofa ta karbi ledar fruits dake hannun umma tace umma Ina wuni?
Lafiya kalau Aisha sannu kinji. Amsa gaisuwar sauran tayi sannan tace hajiya Khadija harkun iso? Ko kimin waya?
To ai ganin nayi ga yaran suna tayamu fira basai an kiraki ba tunda zakizo din ai. To ai shikenan.
Kin ganmu nan yau kwana biyu Amma har na kagara su barmu mu koma gida. Wlh zaman assibiti ba dadi.
Hakane Amma ai kila suna da dalilin kin sallamar ku.
Wane dalili? Sunce stress ne yayi mata yawa wunin jiya duk bacci tayi har safe ai ko wanne irin stress ne ya kamata ace ya tafi.
Murmushi mommy tayi tace still dai kiyi hakuri ai zasu sallame ku idan lokaci yayi.
Sai gab da magrib su mommy suka bar assibitin kamin suje saida ta ajiyewa fatima dubu ashirin gefen gadon ta.
Da sallama suka shiga gidan tana shiga tayi kicibus da kyakyawar halittar data rikita Fatima harta kaita assibiti.
Kai Zaki(not pronounced as zaki like lion but as zaki a little softer in the end) Amma ka cika bawa mutane tsoro wallahi me haka?
Mommy Ina kika tafi?
Bansani ba ajiyeni kayi daza kazo kana min iko? Idan har iko kake so ka nuna kasake aure ka ajiye mata sannan kayi mata wannan ikon.
Kallanta yayi Allah ya huci zuciyarki mommy kiyi hakuri. Gefe yabi yayi tafiyarshi masallaci dan har an fara kira.
Tsaki mommy tayi taje upstairs ta shige dakinta. Harga Allah abun Zaki yana ci mata tuwo a kwarya amma tasan me zatayi.
Abubakar kuwa sallah sukayi mutanen da sukaga labari a tv sai mamaki sukeyi. Shi kuwa ko kulasu baiyi ba ya mike yayi gida bayan yayi isha.
Fuskar nan tasa a hade ya shiga cikin gidan dan sanin yayi saiya tarar da mommy a palor kuma idan taga alamar akwai far'a a fuskar shi saita dauko magana.
Sallama yayi ta amsa mishi tamkar ba itace a dazun tayi mishi fada ba. Zaunawa yayi yace nazo banga abba ba.
Ka jira ai ganinsa zakayi tafada cikin halin ko in kula. Daga haka ya kama bakinsa yayi shiru sanin cewa yan masifar suna kusa.
Shigowa abba yayi da sallama a bakinsa. Suka amsa shi. Neman guri yayi ya zauna sannan suka gaisa.
Kallan Abubakar yayi yace na tsaida ka ko? Girgiza kai yayi yace aa abba.
Yauwa, to Ina maganar da mukayi sati ukku da suka wuce? Harka kawo min sunan yarinya nace zanyi bincike?
Eh abba.
To Masha Allah nayi bincike kuma ban gamsu da abinda nagani ba ko akwai wata wacce kuke magana da ita?
Babu yafada kansa tsaye.
Murmushi abba yayi ma ma'ana kana nufin cewa sai ita ko?
Ba haka make nufi ba abba. Ko wannan din dan kun matsane shiyasa.
Abba yafi minti biyu yana Kallan Abubakar batareda yace kala ba. Sanin yayi idan har yace Abubakar bazai aura wannan yarinyar ba to ya bashi dalilin dayake nema.
Murmushi yayi a ransa yace nina haifeka bakai ka haifeni ba in kasan wata to baka san wata ba. Jeki zan kara tinani idan na yanke shawara zan nemeka.
Saida safe yayi musu yayi tafiyarsa gidansa. Yana fita mommy ta kalla abba kasan abinda yake nema kenan?
Nasani amma bazan bashi abinda yake nema ba nasan yadda zanyi in ciyo kan wannan matsalar.
Ya jikin ita Fatima da kukaje?
Ta samu sauki dan har ita hajiya Sa'adatu tana complain kan cewa anki a sallamesu.

YOU ARE READING
FATIMA
RomanceUnrequited love. When a patient person reaches his limits what happens? He explodes. The true color of this wicked world and cruel life shows. When too much anger is held within, when feelings are bottled up, when lies are told to cover up more lies...