Unrequited love. When a patient person reaches his limits what happens? He explodes. The true color of this wicked world and cruel life shows. When too much anger is held within, when feelings are bottled up, when lies are told to cover up more lies...
Zaki iya tafiya ki bada makullin motar da zaki fita da ita Bala zai duba idan dakwai abinda take bukata amma karkiyi magrib a wani wajen. Ki tabbata six ta miki a gida.
Kallansa safiya dake kwance kan three sitter din palorn tayi. A ranta tace mea wannan bawan Allah yake nufi damune?
Godiva Fatima ta mishi sannan ta mike hadeda yi mishi saida safe ta fice. A hanyar fita taci karo da farida.
Sannu ko ta daya. Farida ta fada tana murmushi.
Mayar mata Fatima tayi tace sannu ta biyu.
Wucewa ko waccensu tayi while Fatima na tinani a ranta to ita wannan matar hala yau albishir din aljannah akayi mata?
Fatima na fita safiya ta mike zaune baby banfa gane inda wannan abun ya dosa ba?
Batareda ya kalleta ba yace Ina jinki.
Me yasa ka tambaya wanchan matar taka idan ranar girkin tane?
Zare ido tayi baby gobe ranar girkina ne kuma ka yadda in fita inje dinner din ya musa. Kuma naji kace karta kai six.
Raising eyebrow yayi your point is?
Akan me ita zaka saka mata doka? Ina ruwanka idan takai gobe bata dawo ba. Ba ruwanka da inda zani Amma ita saika wani tambaya. Wato ita matar so.
Shareta yayi tayi kidanta tayi rawarta ita kadai.
Bazaka amsani ba?
Kallanta yayi sannu mommy kawai yace ya mike yayi cikin bedroom.
Ah lallai Abdallah da sake wallahi da sake nayi wasa sai yanzu naga nayi wasa ba kadan ba. Wato sannu uwarsa itada dole saiya amsata.
Kwaf tayi ta zauna ta cigaba da Kallan tv. While safiya na maseefar an bar Fatima bayan tambayoyi da sharudda, Fatima na chan tana kun kunin sai ita ake sakarwa doka.