TEN

425 25 7
                                    

Yau yakama wata daya da sati biyu da aurensu amma idan kaga bakinsu ya hadu to gaisheshi tayi ya amsa mata.

Har yanzu bata fasa shiga part dinsa ta gyara masa shi ta sanya tiraren wuta ba. Saidai abinci takan dafa a part dinta ta kai nasa part din ta jera.

Idan ya tashi chi tsabar isa ba zaiyi serving kansa ba saiya kira ta intercom taje tayi serving dinsa.

Haka zaici abinda ta dafa ya koshi kuma idan zai kwanta yasha tea dinda take ajewa a bedside dinshi amma kalmar nagode ko yayi dadi bata taba fitowa a bakinsa ba.

Hasalima idan ka kalla actions dinsa zaka dauka cewa dole yake cin abincinda ta dafa. Koda da rana daya bata taba tsallake hada mishi breakfast and dinner ba.

Yauma kamar yadda ta saba ta fito da basket rike kusan six ta nufi part dinsa. Idanta suka kai gurin inda ake parking motocin gidan.

Mota takai ashirin kala daban daban. A dayan gefen ta hango bakar batman dinda aka sanya kan lefenta kusa da ita kuma farar Benz dinta ce wacce abba ya siya mata.

Bude part din tayi da key ta shiga ciki ta maida kofar ta rufe. Dinning ta nufa ta jera bright green kulolin masu bakin handle.

Black porcelain jug din ta ajiye da cups dinsa guda biyu sannan ta fidda plate guda biyu da serving spoon guda daya ta ajiye.

Shiga kitchen tayi ta cika bowl din dinner set dinda tazo dashi ta cika da ruwa tadan ragesu sannan ta ajiye kan dinning din.

Me wannan kitchen din yayi miki da baza kiyi anfani dashi ba?

A firgice ta juyo wayarta dake hannunta ta fadi. Innalillahi wainna illaihir rajiun tafada yayinda ta juyo.

Kallanta yayi sannan ya kalla wayarta dake a kasa. She took a deep breath sannan tace harka dawo?

Dauke kansa yayi yakoma palorn to da kar in dawo?

Allah ya huci zuciyarka yi hakuri ba hakan nake nufi ba. Sannu da dawowa. Tabe baki yayi yace sannu.

Wayarta ta dauka ta kunna taga taki ta kawo. Subhanallah karki min haka dan Allah tace tana sake kokarin kunnata.

Ba tambayar ki nayi ba?

Daga kanta tayi ta kallesa. Chan ta tina tambayar dayayi mata dazun. Aa ta amsa tambayar.

Gyada kai yayi batareda yace mata komai ba. Jin ana kiran sallah yasata sulalewa tayi part dinta.

A natse tayi sallar ta gama tafara azkar dinta. Tana azkar din ta kunna tv tafara Kallan zee world.

Har akayi isha tana zaune a gurin. Mikewa kawai tayi tai sallar sannan ta cigaba da zama a gun.

Yanzu tasa a ranta koda wanne lokaci intercom din dake a main palor zaiyi kara. Sabida daya dawo daga isha yake danna mata kira.

Saidai har nine tayi shiru takeji. To ko yan mulkin sun tafiyarsu shi zaiyi serving din kansa?

Saida gabanta ya fadi Jin karar intercom din as she was lost in thoughts. Mikewa tayi ta nufi palor tayi picking.

Jin kawai tayi an katse wayar. Ajiyar zuciya ta sauke kamin ta koma bedroom ta cire hijab din sallar dake jikinta ta sake fesa Arabian tirarenta.

Neman dankwalinta tayi ta rasa so kawai taja luxury veil dinta ta yafa. Fita tayi bayan ta sanyawa kafafuwanta flat Christian Dior shoes.

Fatima has made it a routine for them dayake sau biyu kachal kawai suke haduwa. Duk ganinta da zaiyi to tsab clean tamkar wacce ta fito daga wanka yake ganinta.

Dazun ma akasi aka samu dan niyyar ta tana ajiye abincin ta koma ta sake wata shigar saidai kash ya ganta.

Dukda haka zaka dauka a lokacin tayi wanka ta sake saka kayan. Sallama tayi hadeda bude kofar ta shiga ciki.

Ganinshi a palor tayi zaune da laptop a gabansa sai typing yakeyi. Gaidashi tayi sannan ta nemi guri ta zauna.

Saida ya jima sosai kamin ya kashe laptop din ya mike yayi dinning. Binshi tayi tai serving abincin sannan ta zuba mishi coconut drink dinda ta hada.

Tuwo tayi da miyar egusi Kallan abincin ya tsaya yi kamin ya wanke hannu yayi bismillah yafara ci.

Yana gama cin abincin ya koma palor ya cigabada aiki. As usual packing din komai da komai tayi ta wanke sannan sauran abincin tasa a freezer dinshi.

Dagangan yau taki ta dafa mishi tea kaman yadda ta sabar mishi. Wucewa tazo zatayi yace mata ga sako a kan kujera nakine.

Dauka tayi tace mishi ta gode batareda ta duba ba ta wuce. Tana shiga dakinta ta bude ledar sakin baki tayi tana kallan meke ciki.

Chan ta fidda kwalin taga waya sabuwa dal sealed a cikin kwalin. Farar Samsung galaxy S22 ultra ce exactly irin tata data fadi dazu.

Murmushi tayi baki har kunne. Kallan wayar take tamkar jaririya ce a gabanta. Sanya wayar tayi tafara charging ita kuma ta fidda kayan baccinta ta sanya.

Tana gama sanya kayan intercom din palorn yafara kara. Shareshi tayi sanin waye da kuma dalilin kiransa.

Kwanciya tayi saidai tana kwantawa landline din bedroom din tafara kara. Kallanta tayi sanin idan tace bataji ta palor ba it's believable amma wannan kam it's impossible.

Dagawa tayi tace hello!

Ciwon mantuwa ya sameki ne a yau?

Na'am?

Tea da kuma tirare kawai yace ya ajiye wayar. Kallan landline din tayi tana murmushi tamkar mahaukaciya.

Hijab ta dauko daga cikin drawer dinta ta fesa mishi Chanel No 5 sannan ta sanya shi. Tana matukar son kamshin a duniya.

Hijab din is somewhat see through Amma bata kulaba saida ta shiga part din nasa. Kitchen din ta shiga ta dora ruwan zafin sannan ta sanya tea leaves in a pot.

Wasu abubuwan herbs da itace ta sake zubawa a ciki sannan to rufe pot din. Daya daga cikin flasks dinsa ta dauka ta ajiye.

Tace tea din tayi sannan ta zuba shi a cikin flask kamin ta kulle ta goge. Dakinsa ta nufa tayi tsaye a palorn saida ya amsata sannan ta shiga.

Ajiyewa tayi a kan bedside drawer yadda ta saba sannan tayi spraying wani abu kamar bakar humra amma kuma kamshin bana humra bane.

Take dakin yafara wani sassanyar kamshi ya bade dakin. Maidashi tayi inda ta dauko sannan ta kallesa.

Sakon dazu nagode kwarai Allah ya saka da alkhairi ya kara budi ya kuma biya maka dukkanin buqa tunka.

Jin tayi sounding genuinely happy yasashi dago kansa daga abinda yake ya kalleta. Fuskarta kawai zata nunama farin cikin datake ciki.

Ameen yafada kamin ya juya ya cigaba da sha'anin sa. Sake cewa nagode tayi sannan ta fita.

Ranar kwanan farin ciki tayi. Anjima ajima ta juya ta kalla wayar wannan karon hadda screen guard yasa mata a wayar.

Amma farin cikinta ragagge ya koma.

FATIMAWhere stories live. Discover now