...17...

417 17 0
                                    

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[17]

"Kufitar dani a wajennan nagaya muku,akan me banci sisin kowa ba kuce zanyi kwannan cell"
Jijjiga ƙarfen ɗakin uwaisu yake yana ihu maganganu,tunda rana yake wannan abin har dare yayi,ɗazu kamma abinnasa yafi yawa dayaga lallai a nan wajen zai kwana.
Ƴaƴan sa basu tabayin abinda zai kawoshi nan wajen ba duk iya shegensu,sai gashi wata can daba jininsa ba tasaka shi shiga wannan ɗakin.
Wari da zarni duk sun isheshi,tun yana toshe hanci har ya daina yafara zage zage. Abincin da aka turo masa a kwano tunda rana ko kallonsa bayyi ba,dan rainin hankali yana cikin wannan abinma zasu kawo masa abinci. Cigaba yayi da maganganunsa,ganin har yanzu babu wanda ya kulashi a cikinsu,sai kace ma basu san yanayi ba.
"Nace muku ku buɗeni na tafi gida,meyasa zaku rufeni anan wajen banyi laifin komai ba,wacce tayi hakan ai yakamata ku kamo bani ba"
"Dama da bamu ganta bane ai muka kamaka,ƴar ka tayi ayyuka laifi a gari ta gudu,a ƙa'idar kame kuma dama idan ba'aga ƴa ba ana iya kama uba ko uwa,in ba'aga miji ba ana iya kama mata. Dan haka bazamu sakeka ba sai ka an biya beli kokuma mun kama ƴar ka tukunna,domin laifukan da tayi da yawa.ta karya jari,ta ƙone ɗaki,ta nakasa yaro,sannan kuma ta kaji da dama"
"Wai inji uban waye yace muku ƴata ce ne? In banda munafurci kowa a garinnan yasan kan yawan ƴaƴana,yasan babu wannan abar a cikinsu,haka kawai ga can ubanta a jeji baza'a kamashi ba saini,da girma na da komai,dan rashin adalci"
"Kaga dan Allah kayi mana shuru,wanne girma gareka,duk garinnan babu wanda baisan irin abinda kake aikatawa ba,naga a irin waɗannan laifinnaka ka tura ƴarka auren goje saboda ka hallaka rayuwar ta. Duk da haka baka saduda ba kake ƙoƙarin cutar ɗan fulani ka aure ƴar sa. Dayake Allah ba azzalumin bawa bane sai ya nuna maka ƙarshenka,indai baka daina abinda kake ba ai bakaga komai bama. Kuma kayi shuru ka cika mana kunne,su wanda suka jigaka a cacar su zo su karbeka mana"
Shuru uwaisu yayi tareda samun waje ya zauna,duk abinda Ƴan sandan suka fadamasa babu ƙarya ko ɗaya a ciki. Taya zaiga laifinsu gaskiya suke faɗa,ƙanana dasu suna cimasa mutunci. Inda yakama girmansa kaman sauran sa'anninsa na anguwa duk haka bazata kasance ba.
Tunowa yayi lokacin da aka kai wani dattijo a unguwarsu gidan kurkuku da ɗansa yayi sata,a ranar muganen anguwa aka haɗu harda ɗansa Musbahu aka fito dashi. Amma shi dayake babu wanda yake daraja shi dashi da babu duk ɗaya,ko mutum ɗaya bai gani ba yazo wajensa. Duk mai yajawo masa banda budurwar zuciyarsa.?
Cikin sanyin jiki ya koma ya zauna a ƙasan cell ɗin,abincin da aka kawo masa ya buɗe,jallof ce cakwaɗaɗɗiyah,baka bambamceta da farar shinkafah inba kaga abin taruhu a jikiba.
Haka yasaka hannunsa ya yasa yakai bakinsa,saida ya runtse ido kafin ya hadɗiye,saboda yanda take faɗa da maƙogaransa kan bazata shiga ciki ba.

[Sumaimah a mahangar gani]

Da safe ina zaune naji muryar hamisu ƙanin Shareefah,tashi nayi na fito daga ɗakin na karbi kwanon hannunsa.
Godiya nace yayiwa ummansu da Shareefah kafin koma daki na rufe ƙofah.
Ƙosai ne a ciki mai zafi sannan aka soyah,da murnata na zauna na cinye tass nasha ruwa.
Gado na koma na sake kwanciyah ban fita ba kaman koyaushe,dan dama haka na kimtsa zanyi ɗin.
Can wajen kaman shaɗayan rana naji ana ƙira sunana,muryar namiji ce amman ba goje bane.
Saurin tashi nayi zaune na mutstsike idanuwana na fito.
Da tunga muka haɗa ido yana can ɗan gefe da baranda a tsaye.
Muna haɗa ido murmushi yayimin kana ya kauda idonsa.
"Ina kwana matar ogah"
Uhm wai matar ogah manya,na faɗa a raina,a fili kuwa ɗan murmushi nima nayi tareda cewa.
"Lafiyah kalau Tunga ya zirga zirga"
Amsa wa yayi a taƙaice kafin yafaramin bayanin abinda ya kawoshi.
"Uhm gashi wannan ki riƙe a wajenki,nasan ba lallai yabaki wani abun ba dazai tafi"
Mamaki yabani ganin ya miƙomin dubu biyu.
"wannan kuɗin fa na menene"
"Ko zaki siya wani abun idan buƙatar hakan ta taso,yace bayan ya tafi na kula da duk al'amuransa,baice da harda iyalansa ba amma kuma ninaga kema yakamata a baki wani abin a kuɗin da muka samo,koba komai bazaki rasa abin siya ba"
"Kulada al'amura,tafiyah yayi ne?"
Na tambaya cikeda mamaki.
Shima saida ya zaro ido jin irin tambayar danayi masa,yo ba dole yayi mamaki ba,yaji mata batasan mijinta yayi tafiyah ba.
"Ohh bakisan cewar yayi tafiyah,wani aikine ya taso wanda ya samu bada daɗewa ba,shine suka nemeshi jiyah akan zai fara aikin,yacemin dai na kula masa da komai sati guda zayyi ya dawo. Laah kuma hakane ba lallai ki sani ba,dan yace na faɗamiki kada komai da kike na aikinki ya sauyah,kiyi shi tamkar yana nan"
Ɗaga kai nayi a zahiri,yayinda ta baɗini kuma zuciyata tayi baƙiƙƙirin,wato zayyi tafiyah amma bai faɗamin ba,saima aikowa dayayi akan nacigaba dayimasa gyare gyare,tunda yake baisan cina ko shana ba saidai nayi masa aiki koh? Idan dan yana ganin ya sameni ne ta sanadin caca ai Ko dabbarsa ma ta sanadin wasan kalankuwa ya samota,amma yana kulada ita sosai,sai nice wato zai maida goruba koh?.
Ɗagawa Tunga kai kawai nayi,dan bansan mai zance masa bama. Allah ya dawo dashi lafiyah,shine abinda nasamu cewa bayan Tunga ya tafi. In kulada shi yaso ya bani haƙuri,ganin banason hakanne yasa ya tafi.
Ina nan tsaye a wajen naga gaji ta fito daga ƙofarta,wajenda kayan wanke wankenta suke,ƙuda yabisu yabisu har sun bushe saboda daɗewa a wajen.
Tsayawa tayi a gaban kayan tana kallonsu, kursiyyahce ta kawo kwanon dataci awara zata ajiye a wajen.
"Ke kursiyyah kije ki ƙiramin kawule ya debomin ruwa kuyi wanke wanke"
"Wai nikam gaji wlh bazanyi ba,haka kawai naga tun safe aka ce Atika tayi tace bazatayi ba,saini za'a saka"
Ƙofar tashige tana wani wantsala kamar tarwaɗa. Nidai ina nan tsaye ina kallonsu.
Da rana ma hamisu ne yasake kawomin abinci,amma sannan kam nace masa kada ya sake kawowa.
Dan kafin ya kawomin kursiyyah ta kawomin shinkafa da wake mai da yaji,wai gashi inji gaji nacigaba da aikina na safe.
Murmushi nayi ganin kwana ɗaya kawai harta daddara ta dawo hanyah. Ban musa ba na karba,danni ma daman hakan nakeso,banason kawomin abincin da ake daga gidan su Shareefan.
Ɗaukar daya nayi daga cikin abincin naci,ɗayan kuma na ajiye na yamma.
Washagari da safe ɗumame kaɗan ta gaji tabani,duk yadda naso abin ya tafi yanda zamuyi zaman lafiyah nasan hakan bazai faru ba sam,dan haka tunda nice mai son mu daidaita dole ni zanyi haƙuri da itah,kaman yanda naga inna tana yi da itan,gobe inna zata yi sati guda da tafiyh,sauranta sati ɗaya ta dawo kenan.
Kuɗin da Tunga ya kawomin na ɗako dubu ɗaya a ciki.Soda ta kawomin nayi wanke wanken,sabulun danakeyi dashi ma dama yaƙare wanda inna tasiyamin,nayiwa goje wanki dashi.
Hijabina na saka wanda nake sallah na fito waje ko zanga wani a cikin yaran unguwa ya sayomin sabulu da omo.
Na ɗan daɗe a tsaye kafin na samu wani almajiri da robarsa a hannu yana wurgawa sama.
"Dan mallam dan Allah zo na aikeka mana"
Na fada ina ƙirnsa da hannuna,tahowa yayi da hanzarinsa,kayan jikinsa na kalla,duk sun yayyage sunyi daƙan daƙan dasu,yana dosoni sai zarnine yake tashi. Wai rayuwa kenan,wato idan kaga rayuwar wani dole ka godewa Allah.
"Iyah ta gani"
"Yawwa dan Allah omo zaka siyomin da sabulu a wancan shagon"
"Tah"
Karba yayi ina kallonsa ya nufi shagon,kasancewar ba nisa ina hangoshi har yaje ya dawo.
Hamsin na dauka a kuɗin na bashi,ya karba yana godiyah ya tafi,nikuma na shigo gida.
Ƙofar gaji na shiga siyan awara,tunda nasamo sanji.
Sallama nayi ta amsa ciki ciki,bata huce ba kenan.
"Gaji a bani awara ta ɗari"
Nafaɗa ina miƙamata gudan ɗari biyar ɗin da aka bani a canji,tsayawa tayi tana kallon kuɗin naɗan lokaci kafin ta karba.
"Tohh amarya an fara samun kuɗine a wajen miji?"
"Amarya bazata samu kuɗi ba dole sai in miji ne yabata?"
"To ba cass bare ass,kana kuma babu jiyarar ƴan uwa,ai dole mu tambaya"
"Akwai wasu marasa cass da ass ɗinma a gidan dasuke siyan kayan masu cass da ass ai"
Hmm tace kawai kafin ta ƙirgamin awarar,dan tagano da Atika nake ƴar ta,shigar kaya a gidannan wanene ya kaita,kuma ba sana'ar fari bare ta baƙi,kuɗin jikinta sunfi na jarin awarar ma.
Canjina ta miƙomin na ɗari huɗu da kuma awarar tawa.
Karba nayi bansake cewa komai ba na bar ƙofar,zama nayi na cinye tass nasha ruwa kafin na fito yin wanke wanken.
Ga ɗiban ruwa ma yana jirana na randa ta data goje,da kuma saniyar can,dan dai kar a ɗaure dabba a hanata abincine tausayi ma bazai barka ba,da wlh bazan sake bata komai ba sai ranar dazai dawo,hmmm ga gyaran ɗakinsa ma,shima bazanyi ba sai ana gobe zai dawo inyaso.
Wani satinne ina? Kafin sannan ma idan nayi sa'a inna tadawo lokacin.

          __**__

"Toh sabon salo lallai yarinyar nan in banyi da gaske ba tsoronta zan faraji a gidannan..a ina tasamu kuɗi haka hadda sanja ɗari biyar,naga siyayya tayi na sabulu da omo ma a leda"
Buɗar bakin kursiyyah wacce take zaune a gefe sai cewa tayi.
"Ai inna Tunga ne wannan abokin yahya goje ya kawo mata kuɗin,dan ina banɗaki naji yana cewa wai,gashi ta rike kafin gojen yadawo. Tafiya yayi kuma zayyi sati bai dawo ba"
"Ke ƴar nan,kenan baya garin? Haba biri yayi kama da mutum,shiyasa ban ganshi ya shigo gidan ba har zuwa yanzu,wato kuɗi aka kawo mata ta dunga kashewa kafin ya dawo koh. Kuma ta rasa mai zatayi sai siyan omo da sabulu?"
"Wanke wanke zatayi mana dashi"
"Naga na aika ki kaimata sodar wanke wanken,wanne iyayine sai tayi da omo,kaman wata ƴar gayu,kowa ma ai da sodar yakeyi"
"Ohh gaji baki sani ba,ranar naji tana faɗawa inna wai intayi da soda hannunta tsatstsagewa yakeyi"
Barin ƙirga awarar gaji tayi tana kallon kursiyyah,wacce tagama shirin fita tallen safen.
"Oho dama hakane,ya akayi bansan zancen ba kuwa,ni inacan ina tunanin banza,ga hanya mai sauƙi wajen kamata da hannuna,sai nayi mata abinda da ƙafarta zatazo har wajena ta tsugunna,badai ni take mayarwa magana ba"
Gaji ta ƙarisa maganar tana murmushin mugunta.

Oohp anan zan tsaya fah sorry baikai sauran ba da shafi huɗu,wlh na gaji ne shiyasa🙏🏼 muhaɗu gobe kawai.



Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

SANADIN CACAWhere stories live. Discover now