...22...

499 16 1
                                    


*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[22]



[Sumaimah a mahangar gani]

Tun ɗazu nake zuba idon ganin inna,motsi kaɗan saina leƙa ƙofar gida,safa da marwa nake yanzu ma a kan baranda ina tunanin anya kuwa zata dawo ɗin,ganin yamma tana shirin yi amma shuru bata dawo ba.
Kasancewar ban buɗe stove ɗin na fara amfani dashi ba,kawai murhu na haɗa na gyara naman,saikuma na tafasa taliya..
Har na juya zan koma ɗaki sainaga inna Mairo tashigo gidan,magana suke da almajirin daya shigo mata da kaya,wani farinciki na tsinci kaina dashi,ban lokacin dana tafi da gudu na rungumeta ba.
Dariyah tayi tana cewa.
"Allah sarki,duk da na tafi na barki amma kike murnar dawowa ta,nayi zaton ai zakiyi fushi ganin na ƙara sati guda"
"Uhm naji haushi kam har kuka nayi,amma ya wuce tunda kin dawo,zo muje ki zauna ki huta,daga gani kin gaji"
Jan hannunta nayi muka shiga cikin ɗakinnata,saidai tundaga bakin ƙofah danaga ta tsaya nasan abinda yabani mamaki ɗazu tagani,wato kayan da goje ya kawo.
"Sumaimah wannan abin kumafah,waye ya kawo wannan kayan haka?"
"Uhm goje ne ya saka Tunga ya kawo ɗazu,wai yakamata mufara abincinmu"
"Eh to yanzu ba zancen abincinba,a ina yasamu kuɗin daya siyo waɗannan kayan,a sanina dashi bashida ko sisi,ko wajen mai shayi ma bashi ake rubuta masa,taya yasamu wani kuɗin siyan waɗannan kayan"
Cikeda zullumi take maganar,kanaji kasan bata yadda da kayan ba.
"Nima na faɗi haka sai Tunga yace wai ɗan siyasar su ne yaci,suma haka suka samu kuɗin dayawa,inaga kuma shugaba"
"Oh na manta ma da abin zabe,in hakane shikenan Allah ya kyauta,amma zan sake tambayarsa,kai wannan ƙasa tamu wai dan zakaci zabe sai kayita rabawa matasa kuɗin al'umma?. Allah ya shirya shuwagabanninmu kawai"
"Ameen ya Allah"
Gyalen dayake wuyanta ta ajiye tareda zama a bakin ƙaramin gadonta.
"Yana sameku Sumaimah ya mutanen gidan,da zan shiga ƙofar gaji nace mata na dawo,sai kuma naji wai ta tafi anguwa. Wannan kayan ki gyarasu mana shima abin girkin ki buɗe ki jerashi,ina kin iyah amfani dashi?"
"Ehh na iya,ina dafawa yaya Musbahu indomie a nasa na ƙofarsa"
"Yawwa toh ki shirya komai,ai dama da kinyi tun ɗazun basai kin jirani ba"
To nace tareda ɗakkowa kuɗin daya bani ɗazu na miƙa mata.
"Inna gashi wannan ai a ajiye inda abinda za'a siya na amfani"
"Ahah ki riƙe a wajenki tunda kece mai siyan abubuwan,ni bazan riƙe kuɗi ba a hannuna,kiyi yanda ya dace kawai,in neman shawara ce saiki tambayeni,amma batun na karba bai taso ba. Sannan a kayan ki ɗebi wasu ki kaiwa su gaji,duk da an san zaman da akeyi amma tayi ƙoƙari sosai nayin abinci"
Maida kuɗin nayi inda na ajiye,abincin na zuba mata taci sannan muka hau hira,wadda duk na abinda ya faru ne da batanan,wani tayi dariya wani kuma ta jijjiga kai. Abinda take cewa kawai nayi haƙurine watarana zai wuce,a lokacin baya bana yarda da zancen ta,amma yanzu nafara yarda da zai wuce watarana sai labari.
Kafin dare na shirya komai yanda zanyi amfani dashi,Sannan su gaji ma na cire musu wanda zan kaimusu.
Jakakkunan da Tunga yabani kuwa kayane a ciki na sakawa,kowanne kala uku da hijabi da takalmi flat mai kyau,idan nace banyi murna na wlh ƙarya nake,ko a mafarki bantaba tunanin samun kayan a lokacin ba.
Tunda magriba nake jiran naji gaji ta dawo,amma sai bayan isha tukunna naji muryarta tana magana da hamisu akan wai bai ɗebi ruwan da ta sakashi ba.
Sallama nayi na shiga,hannun ɗauke da kayan dana kai musu,shuru tayi da faɗan tana kallona,duk da bani take kallo ba sai abin hannuna..
Washe baki tayi tana min magana,abinda tunda nake bata taba yimin ba sai yau.
"Ahh Sumaimah kece da darennan,naji Addah Mairo ta dawo ko,yanzu nake shirin zuwa nayi mata sannu da dawowa ai"
Wai meee?? Ba mafarki nake ba kuwa,gajice take waɗannan kalaman masu daɗi.
Dawowa nayi daga mafarkin dana tafi nace.
"Ehh ta dawo run ɗazu da bakyanan,ga wannan kayan abinci ne,sannan inna tace mu faɗamiki ta gode sosai,zamu dunga girkinmu yanzu"
"Ahhh me yayi zafi daza'a raba girki haka rana tsaka,mai zai hana ma ni zan dungayi kaman koyaushe,kice mata ta kawo kayan girkin za'a dungayi ba matsala"
Anya kuwa gaji tanada kunya? Nayiwa kaina wannan tambayar,juyowa nayi ina mata kallon mamaki.
"Ahah karki damu gaji babu komai zan dungayi,yanzu ai gurege yazo ga harawa,koda zata kare walau nan kusa kokuma ya daɗe,amma dai yanzu kam zaici ya more. Kuma karki damu inna bazata ƙwace gonar marigayi ba a hannun babansu Atika,sannan kuma injin markaɗenta ma bazata karba a wajensa,dama ina dasu ake ciyar da gidan,yanzu babu mu a ciki kuci iyah ku kaɗai"
Ban tsaya jin abinda zatace ba na fita daga ƙofar bayan na ajiyemata kayan,a zaton ta duk abinda take ba'a sani ba,nunawa take kaman ita take ciyarda gidan,bayan gonar da ake noma hatsin ba nasu bane,injin markaɗen da baban su Atika yasaka yara suna aiki dashi yana karbar kuɗin duk na inna ne.
Kayan aikina da nazo dasu na fito dasu,tunda nazo gidan yau wata na guda sai yau zanyi wani abu na ƴan cin kaina.
Kula tuwo da miya na ɗakko na abincin goje,saikuma kwanukan da zanyi amfani dasu na aikace aikace.
Da daddare ban sake abinci ba,kasancewar wanda nayi ma na rana bamu cinye ba,kuma goje yace ba lallai yadawo ba.
Dan haka hirarmu muka sha har bacci ya ɗaukemu,cikin farinciki da annashuwa.

SANADIN CACAWhere stories live. Discover now