...21...

429 16 1
                                    

*SANADIN CACA*

Mallakar SADI-SAKHNA

PROFICIENT WRITER ASSOCIATION

*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[21]


Saida A.M Aliyu yaje kusada sashen Mammah kafin ya yiwa masu take masa baya alamar su tsaya,dan tasha faɗamasa batasan yana shiga mata da wasu masu tsaron lafiyarsa wajenta.
Tafiyah yake shi kaɗai har ya shiga falonnata na farko,gabaɗaya wajen idan mutum yashiga sai ya ɗauka cewar a cikin faɗar gargajiya yake,amma ta faɗa a gani. Kasancewarta daman ita ƴar sarautar Zaria ce.
Hadimai ne suke ta kai kawo wajen ganin wajen ya kasance tsaff kuma mai ƙamshi da daɗin gani.
Tun a wajen ya cire takalmanta yana taka carfet ɗin daya shimfiɗe wajen har zuwa bakin turakarta.
Mai aikinta ce ta hannun damansa tayi masa iso kafin ya shiga. Dama da itah sukazo gidan tunda akayi aurenta,kusan itace ma tayi rainon A.M Aliyu.
"Ranka ya daɗe tace zaka iyah shiga"
Ɗaga kai yayi daga nan yasaka kai zuwa cikin ɗakin,a zaune take da farin mayafi a jikinta ta lullube ko ina da shi,da kaɗan kake gano jar doguwar rigar da take jikinnata. Akan sallayah take hannunta ɗauke da carbi,da alama lazumi takeyi..
Tsugunnawa yayi a gabanta tareda kama hannunta ya riƙe,yana masifar son mahaifiyar tasa,sannan baya tunanin akwai ranar dazai daina alfahari da ita,kasancewarta mai dattako dakuma tausayin na ƙasa da itah,shi bai san meyasa matarsa takasa godewa Allah da irin wannan suruka data samu ba.
Murmushi tasakar masa mai taushi tareda dafa kansa,duk da kana ganinta kasan dattijuwa ce,amma kuma a yanayin kallonta bazaka ce ta haifi A.M Aliyu ba.
"Mai samu wannan gwarzon jarumin haka?"
"Mammah wannan case ɗin na BC ya dameni,tsawon shekara bakwai tun Ahmad nada rai shima yayi iya ƙoƙarinsa,amma har yanzu abu ya gagara,mun kasa gano sirrinsu da kuma inda suke"
Murmushi tasake sake masa wanda yakesa yaji duk damuwar sa ta kau.
"Karka damu Abban Saleem komai na duniya a sannu ake binsa,sannan da sannu lagonsu zai karye kuyi nasara akan su,naga a labarai wai sun kai hari Local govt ɗin gwagwalada koh?"
"Hmmm haka fah,Gen Saeed ne akan aikin,amma da alama shima abun yafara gagararsa,gashi gwamnati na shirin ɗauke case ɗin daga wajenmu ta maidashi ƙarƙashin Civil security,wanda kuma nasan bazasu iya da aikin ba,yanada hatsari sosai"
Cikeda damuwa ya ƙarisa magana,duk da shi jarumine kuma wanda baya juya ƙasa da wuri,amma ga mahaifiyar tasa shi mai raunine dayake buƙatar tallafinta.
Tausarsa ta dungayi da kuma bashi baki har hakan yayi tasiri a ransa.

        ___***___

[Sumaimah a mahangar gani]

Yau kimanin kwana uku kenan da kaini asibiti da goje yayi,abubuwa da dama sun faru,ciki harda samun sauƙi danayi na hannuna,bana komai a gidan saidai nayi wanka na kwanta. Abinci kuwa kullum sau uku goje yake kawomin a rana,kuma dukka mai daɗi da rai da lafiyah,shikansa na kula shigarsa ta sanja ba kaman ta da ba,yayi kaya da yawa kala kala,mashinɗin daya kaini asibiti dashi ma ashe nasa ne,koda yake siyasa ta zo ai dole su samu kuɗi.
Hannayena sun warke sai sa'ba da sukeyi,kasancewar maganin mai tsada ne da kuma kyau.
A bangaren su gaji kuwa ko kallon rashin arziƙi basa yimin,saboda mungun gargaɗin da goje yayi musu,kullum da safe zan jisu suna faɗa akan wanke wanke,ko leƙasu banayi balle nasan mai sukeyi.
Yanzu ma a zaune nake ina kallon jikina,naƙara ɗan haske da kuma ƙiba,a iya kwana biyu kawai. Ashe dai hutu yanada daɗi,inaga tunda nayi wayo ban taba yin hutu kaman wannan ba.
Ledar dana gama cin indomie na ɗauke da kuma kofin na fita da su.
Da gaji muka haɗa ido tana ɗiban itace a wani fili dayake gefen ɗakunan inna mairo.
Harara ta maka min amma batace ƙala ba,nima daga kallo ɗaya bansake kallonta ba na saka ledar a shara na wanke kofina.
Koba komai dai na huta da muguntarta koda na kwana uku ne,dan har yanzu ban daina tunanin wataƙila goje zai daina bani abinci idan na warke.
Tsintsiya na ɗauka na share ɗakin da kuma barandar,har zan tafi wata zuciyar tace da na gyarawa goje sashensa ai tunda na samu sauƙi.
Cikin kasada kuwa na nufi ƙofar tasa,tayi datti kam ba laifi,haka yake rayuwa a ciki,koda yake kanna zo ma ai haka yake,kuma dan ya kulada ni kwana biyu bashi yake saka cewa wai ya shiryu bane daga yanda yake wata zuciyar ta fadamin.
Randarsa kam a cike take da ruwa,kasancewar yanzu hamisu ne ƙanin kursiyyah mai wanann aikin.
Makullin daya bani kwanaki na saka na buɗe ɗakin,hannu na saka ina kaɗe hancina,banda hamamin maza babu abinda ɗakin yake.
Uhmm hali zanen dutse.
Na faɗa a raina,wangale windown ɗakin nayi dana ƙofar,kayansa daya zuzzubar a ƙasa na ɗebe na saka su a gefe.
Saidai na fara da gyara fasalin ɗakin kafin na share shi,kayan daya 'bata kuma na fito dasu daga ɗakin,shin zanyi iya wanki kuwa dana fito dasu.
Tunani nake hannuna a kunkumi ina kallonsu,duk da hannuna ya warke amma bai gama komawa daidai ba,idan nace zan murza kayan wanki toh sai koma baya.
"Dama waye yace kiyi aiki da kika tsaya kina tunani,ko shima salon gulamane kai kice bansan cinki ba ban san shanki ba,ballantana halin da kike ciki"
Zabura nayi na ɗan koma gefe,saboda na bashi damar shigs ɗaƙinnasa,danna tare bakin ƙofar,dama yana bayana tun ɗazu kenan?.
"Kayi haƙuri,kawai naga zan iyah shara ne shiyasa"
"Eh to kuma shi wanki da bazaki iyah ba sainace saikinyi koh?"
"Ahah ..uhmm...."
"Ɗauresu ki sakasu gefe zan bayar a wanke,sannan kizo ki zauna akwai maganar da zamuyi"
Dumm naji kaina yayi,magana da goje? Uhm
Ɗaure kayan nayi kaman yanda nace,kana naje gabansa na zauna,idon yana kallon tsakar ɗaki,shikuma yana zaune a bakin katifa.
"Tunda yanzu kin warke saiki faɗamin dame dame kikeso na kayan abinci,kinsan dai bazan jure kullum in zan zubawa cikina abinci saina haɗo dake ba koh?"
Ɗaga kai nayi alamar ehh,aikuwa naji wata tsawa kamar a sama.
"Nida kai nayi miki magana dabazaki buɗe bakinki ba,kodan nayi jinyarki saina zama abin wasanki kai?"
"Ahah kayi haƙuri,ehh na warke zan dunga girkin za'a iyah siyowa,itace ne saikuma kayan abinci,inda abubuwan aiki daban su tukunya"
Kaman mai aljanu jin abinda nace kuma sai ya maida muryarsa yanda take.
"Tom shikenan,zan aiko Tunga ya kawo in anjima,ba lallai yau na dawo ba,sannan inna tace na faɗamiki Yau zata dawo,munyi waya da ita da wayar ƙaninta"
Duk da a razane nake bansan lokacin da murmushi ya kubcemin ba.
"Dan Allah toh shikenan barinje na gyara mata ƙofar sosai"
Tashi nayi zan fitah da sauri,har na manta baice na tafi ba.
Saida naje bakin ƙofa naji maganar sa.
"Na sallameki ne?"
"Au ehh um toh"
Nafara shirin dawowa ina inda inda.
"Jeki kawai"
Yafaɗa yanayin wata ƙaramar tsuka.
Uhm kai kasani dai nafada ina yin sashennamu da saurina.

Bawani gyara ƙofar take buƙata ba,amma haka nasake gyarawa dai,saboda murnar dawowar innan.
Bayan na gama wanka nayi nasaka kayana na zaman gida.. Ina kwance har bacci ya ɗaukeni.
Can kaman a mafarki nake jiyo sallamar mutum a baƙin ƙofar ɗakin.
Ɗan kwalina na ja na yafa na fito,himm naci karo da kaya a bakin ƙofar ɗakin.
Buhun shinkafah ƴar gwamnati,galon ɗin manja dana mangyaɗa,katton ɗin taliya ta leda,buhun gari na semo,macronni indomie harda su doyah da dankali.Sabon Risho a kwalinsa da kuma jarkar kananzir babba a ciki damm. Sabulai na wanke dana wanki masu kyau,harda macline.
Zare ido nayi ina dafe ƙirji,wannan kayan fah,wanene yayi batan kai ya shigo dasu haka?anyah bana gidan chairman bane ba kuwa.
Ina nan tsaye nayi suman tsaye tunda yashigo giɗan hannunsa riƙeda jakakkuna guda biyu,wani yaro ma yana biyeda shi da wata leda a hannunsa.
Dariyah Tunga ya tuntsire da itah ganin na ƙamekam kaman wata soja.
"Matar ogah wannan kallon fah,ogah yacemin dama kunyi maganar dashi ina,kan cewar za'a kawo. Ga wannan jakakkunan ɗaya naki ne ɗaya kuma na inna,wanann kuma wai ki soya shi ku dunga miyah dashi"
Jakakkunan na bi da kallo,sannan kuma da ledar da yaron ya miƙamin.
Har sannan ko ƙala ban ce ba,wasu kuɗaɗe yasake ƙirgowa ya miƙomin,hannu yana rawa na karba inaso naji su kuma na menene.
"Wannan kuma yace ki riƙe ki sayi abinda kikaga babu,in sun ƙare kiyi masa magana,ga yaronan zai dunga shigowa yana miki aika,inya kama sai ku dunga bashi abinci. Idan babu wani abin ni zan tafi"
"Ba.....bbbu komai ammmm....mmma kuwa ba mafarki nake ba?"
"Wanne mafarki ba mafarki,namune yake shirin hawa mulki,da kuma sabon ainkin ogah da yayi shima suka biyashi da tsoka,muma yanzu mun daina satar kajin mutane,gwangwajewa muke da daɗi,muma muka ci bareke matar ogah,ai ki sake jansa a jiki ki lashi arziƙi tunda Allah yakawoki a daidai sanda yayi kuɗi,dama ku kuke ganinsa kaman mungu,amma oga goje ai akwai kyauta,saidai in bata biyo ta kanka ba baya tunawa da shafinka. Inkika bi a sannu zaki gane kansa,kuma zakiji daɗin zama dashi,sannan akwai abu ɗaya danake son kiyi a rayuwarsa,in lokacin yazo da kanki zaki tambaya kuma nayi alƙwarin zan sanar dake.....zo mu tafi Yusuf"
Yafaɗawa yaron suka fitah waje bayan sun barni a duhu tsulum da bayyanar tasu.
Ledar da take hannuna na buɗe,kaji ne Yankakku an gyarasu tass. Samun waje nayi na ajiyesu tareda ƙirga kuɗin dayake hannuna,dubu ashirinne ciff.
Komawa ɗaki nayi na ajiye kuɗin da jakakkunan danaji kaman kayane a ciki.
Sauran kayan ma duk ɗakin na kaisu na ajiye,da nayi niyyar kaisu ɗaya ɗakin inna ne wanda babu komai a ciki,saikuma na tuna akwai masu halin bera a gidan sosai,karsu yi ɗan halin irin wanda sukamin a kuɗina.
Babu abinda zan taba sai inna ta dawo,ko wanne lokaci nasna zata iya dawowa a yau ɗin.
Dan har yanzu ban yarda Tunga da gaske yake gojene ya aikoshi ba tabbb wayaga duniya sabuwa.
    
          __**__
   
"Wlh gaji da gaskene nake miki,wannan yaron yayah gojenne ya dunga shigowa da kayan abinci yana jibgawa a ƙofar inna mairo wajen Sumaimah,hadda wasu jakkuna da bansan menene a ciki ba"
"Ke ƴar nan banason ƙaryar banza fah"
"Hmmm kinace wai ƙarya nake,ki zo ki leƙa ki gani mana,gatacan tana shiga dasu ma ɗakin innan"
Jirif gaji ta tashi daga kason abincin da take ta leƙo ƙofar innan,daidai lokacin da Sumaimah take jan buhun shinkafar zuwa cikin ɗakin innan.
Zaro ido tayi tana kallon sauran kayan da suke wajen,katton ɗin taliyah dana macaroni,kaman taje ta ɗebe haka takeji.
"Kambuuu wanne ƙusane yabasu waɗannan kayan abincin haka"
"Ohh baki sani ba,wanda goje yakeyiwa aiki shine ya tsaya takarar ɗan majalisa,kuma ana tunanin shine zaici,har mashin ya siya fah saboda dal kina gani yake hawa. Sannan kwana biyunnan kullum sai an kawowa Sumaimah nama da shayi mai kauri,kina gani ma sanda take zubawa a shara"
"Cabɗi wannan shine ka tura mutum rana an janyeshi cikin fadama,shegiyar yarinya haka zatayi ta famtamawa yanzu muna kallo....inaa aradu hakan bazai faru ba,bari Atika ta dawo daga talle musan nayi.hakama malam,ai dolene muma yabamu tunda ina matar ubansa,bazayyiyu a dangwali na banzar nan babu mu ba kam.."

Toh fah

   

Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank

Ko katin mtn ta nan
09035784150

VTU ta nan
2347068390570

Shaida kuma ta nan
09035784150

Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
----------------------------------------------------

Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please

SANADIN CACAWhere stories live. Discover now