MAR'ADAM'S EPISODE 7

166 3 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Book one
Free page

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page7

........" Cikin mugun firgici da tashin hankali aunty khadeja da aunty shahida suka yi shiru gabad'aya suna kallonta cike da sansar fargaba da tashin hankali "me zasu fad'awa mami  data d'auki soyayyar duniya ta d'aurawa aurensu ? " ita kam Maryam kasa kallon cikin kwayar Idanunsu tayi ta takure jikinta guri daya tayi kasa da kanta idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye gbdy ta kasa kwakwaran motsi a zaunen da take , wani iri take ji a gabadaya ilahirin jikinta ,sai lokacin taji wani irin kunyarsu tayi mata diran makiya .

ji tayi kamar ta tashi ta bar gurin sai Kuma taga hakan ba daidai bane ,basu cancanci haka daga gareta ba ,zasu d'auka raini ne dan haka ta cigaba da zama zuciyarta na tsalle da bugawa wasu hawaye masu zafi suka samu nasarar zubowa akan kuncinta tasa hannu ta goge wasu na sake zubawa ."
Sanyayyaye numfashi aunty shahida ta sauke tana gyara zamanta tare da janyo maryam zuwa jikinta tasa tafin hannunta tana share mata hawaye "kukan ya isa haka tunda baki son shi shikenan zamu san yadda zamu fahimtar da mani  amman da zakiyi hakuri kiso AD  hakika maryam da kin san kin dace miji na gani na fad'a ba dan AD ya kasance dan'uwana ba ,duk mace zata yi alfahari ya kasance miji agareta kuma uban ya'yanta ki tsaya kiyi tunani maryam karki yanke hukunci cikin tsoro da tashin hankali ".

Cikin tsananin kuka da tashin hankali maryam tace "a'a aunty shahida babu wani tunani da zanyi akan ya Adam dan yafi qarfina ta kowani bangare ban Isa na tsaya Inda yake ba bare na kasance mata agaresa ta Ina zan soma rayuwar aure dashi aunty shahida ? "Ta Ina zan fuskanci mutumin da bai qaunar ya bud'e idanunshi ya gani ? "duk duniya idan akwai macen da ya Adam ya tsana to nice "Ina zan kai tsoron da nake masa har nayi rayuwar aure dashi ? uwa uba baya Sona ta yaya kuke tunanin nima zan soshi har naso zaman aure dashi ?" wallahi aunty shahida ni tsoro ma yake bani ban ma san ta ya zan fara rayuwar aure dashi ba , da zarar nagansa bana samun natsuwar zuciya har sai na nisanta kaina dashi to ta yaya kuke tunanin zan iya zaman aure dashi Koda Ina son shi bare bana masa soyayya irin ta aure sai ta yan'uwantaka ?"

" ni yanzu tashin hankalina mami  wallahi bazan so taji wa......."kuka yaci karfinta ta kasa qarasa maganarta "dan wannan karki damu Ina da tabbacin da zarar kunyi aure shikenan maryam ,bazai nuna miki komai ba sannan zaki daina jin tsoronsa inshallahu zakiyi farinciki a gidansa. "maryam ta zumburo baki "Allah aunty shahida bazan iya ba shine miskilanci shine girman kai , uwa Uba zuciya idan na auri ya Adam bazai barni na rabi Inda yake ba kullum zan tabbata cikin gallazawarsa wa zai ceceni a hannunsa ? ta Kalli aunty khadeja hawaye na gangarowa akan quncinta "yan'uwana ku taimakeni karku bari a had'a auren nan , ban rainaku ba sannan ban ki shawararku ba amman abar wannan maganar yanzu baku ji yadda nake jin zuciyata ba ,ji nake kamar zata fashe tsabar tashin hankalin jin maganarku , Kalli yadda jikina ke rawa aunty khadeja Allah bazan iya ba ta k'arasa maganar tana sake rushewa da wani sabon kuka."

Aunty khadeja wacce tayi shiru tana sauraronsu tace " duk na fahimceki Maryam amman yana da kyau mutun yayi dogon nazari akan duk abinda ya kunno kai cikin rayuwarsa zamu baki lokaci kiyi tunani sannan kiyi istahara ..?maganganu masu sanyi da kwantar da hankali aunty khadeja tayi amfani dasu gurin son janyo hankalin maryam duk da a rikice take amman tana fahimtar komai dake fita daga bakinta ,naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana mai kallon aunty khadeja sannan taja gindi zuwa Inda take ta riko hannunta d'aya cikin nata ta damke gam jikinta na sake d'aukar kyarma muryarta a raunane tace "aunty khadeja bazan iya aurensa ba bari ma na fada muku gaskiya akwai wadan da suke sona sosai ku bari ya nemo matarsa a waje zai fi zame mana alkairi ......"

MAR'ADAMSWhere stories live. Discover now