💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahimWannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 17
" are you crazy some "?ya furta a zafafe yana hura hancinsa har zata girgiza masa kanta alamun "a'a ! sai kuma tayi sauri ta gyada masa kanta alamun "Eh! dan ko giya ta sha bata isa tace masa "no ! ba bare tana cikin hankalinta "what's wrong with mr ata I did not do anything wrong ? tayi maganr acikin ranta tana mai sake kama kanta dan karta yi wani kuskuren da zai dakatar daita na wasu satittuka koma ya dakatar daita aiki gabadaya ."
" ahankali ya mike tsaye ya kamo lip's dinsa na kasa yana cizawa ahankali ahankali !! magana yake son yi amman ko ya bud'e bakinsa maganar bazata fito ba , daga can bakin kofa akayi knowking tare da cewa "may I coming sir ?". shiru yayi yaki cewa komai sannan yaki kallon kofar , some dake tsaye cikin tsananin tsoro da fargaba ta kalli glass din kofar taga prosper ne tsaye hannunsa rike da file mai cover green wani yawu ta hadiye sannan ta saci kallon inda mr ata yake tsaye taga baya kallonta ta sake juyawa tayi wa prosper alama da hannunta ya koma da sauri ya juya ya bar bakin kofar ."Mr ata yasa hannu ya d'auki wani file mai white cover dake ajiye akan makeken table dinsa yana dubawa , lokaci me tsawo ya d'auka yana dubawa yana shawagi acikin makeken office din nasa zuciyarsa na tafarfasa yayinda wata irin zufa ke tsatsafo wa some akan goshinta kamar an watsa mata ruwa .duk lokacin da taga mai gidan nata cikin damuwa itama sai ta tsinci kanta ciki dan kusan duk abinda yaje ya dawo akanta zai
qare tunda itace sectary dinsa duk abinda zai shiga ya fita ta sani ."Ya sake kamo gefen lip's dinsa. na qasa yana cizawa hannunsa dake rike da file ta zubawa ido tana tausayawa duk matar datai ganganci aurensa , tana goge zufan goshinta dake ta tsatsafo mata duk da karfin sanyin ac dake ratsa office din ."Cikin kulawa da girmamawa tace "sir !" ko zan iya kiran metting a yanzu ?"
"ahankali ya lumshe lumtsatsun idanuwanshi da suka d'an canza kala alamun tarin 'bacin rai yake ji acikin ransa "sir !ta sake kiransa a karo na biyu ahankali ya motsa lip's dinsa "go !" ya fad'a atakaice batare daya kalleta ba da sauri ta juya ta fice daga cikin office din tana sauke naunayen ajiyar zuciya ."Cikin kankanin lokaci ta dawo ta tsaya a gefe cike da kamewa da girmamawa tace "sir komai ya Kamala kai kawai ake jira." a natse ya goya hannuwansa duka abayansa ya soma daga kafafunsa dake cikin hadadden black canvers tana biye dashi abaya hannunta rike da wata takarda mai bango ja , tafiya kad'an sukai sai ga hisham da yaya Ibrahim tare da wasu manyan maikata guda biyar suka marasa baya suna takawa ahankali har zuwa qasan kamfanin madadin yabi hanyar da zai kai shi comference room sai suka ga ya karya yabi wata doguwar hanya , nan take some tayi gaba da sauri domin ta fahimci inda yake son zuwa kafin ya shiga conference room yayinda sauran suke take masa baya, bai tsaya akoina ba sai abakin wani makeken kofar glas wanda ya kasance anan ake ajiye duk wasu ayyukansu masu mahimanci ya zura duka hannuwansa acikin aljihun wondonsa yana kallon wajen yana bukatar a bude masa ya shiga tare da qarin bayani ."

YOU ARE READING
MAR'ADAMS
Romancelabari ne Mai dauke da soyayya , ilimantarwa, fadakarwa, nishantarwa jajicewar rayuwa .